← Book details Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 71

Sashe 48

Shahaab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar yabata yace"mama wannan sune Wanda suka hada wannan vedion da aka turo muku keda munirat, Amma Kuma narasa Ina nasan fuskokinsu, kamar de qawayen munirat ne"

Mama ta kar6i wayar, tana ganinsu tace"sune mana, qawayen tane, ai wani lokacin idan sunzo Ina ganinsu, tosu menene amfanin hada wannan shirmen? Menene ribarsu nayin hakan?shiyasa banaso munirat ta dinga mu'amula da qawayen banza irin wannan, yanzu banda raini yaza'ai suyiwa mijin qawar su haka?"

Cikin damuwa yace"shine abinda nagani Nima"

Tace"kaje ka sameta kuyi maganar, Amma su din karka yi musu komai, kabar su Suda mahaliccinsu, idan sunyi hakan ne da wata manufar ai gashinan Allah yatoni asirinsu, kodan mutuncin dasuke yi Suda matarka, karabu dasu, Amma kasa a qwace wayoyin su a duba sosai idan akwai irin vedion agogeshi, wannan 6ata suna ne, ita Kuma saika fada mata tasan irin mu'amular dazata dinga yi dasu"

Cikin gamsuwa da bayanin Nata yace"to mama"

Daga Nan yatashi yanufi part dinsu, yana tunanin tayaya zai iya yiwa munirat din maganar aurensa da Aisha?

Yana shiga falon nasu yaga TV a kunne ta nayi, Kai tsaye dakinta yanufa, yanaso ya nuna mata kuskuren ta akan laifin data masa na saida filayen mama, sannan Kuma ya hanata mu'amula da wannan qawayen Nata, saboda karsu dinga Zua suna hure mata kunne har taqi yarda suyi Zaman lafiya itada Aisha, gefe guda Kuma ga wata irin masifaffiyar sha'awa da yakeji, yadade-yadade, abun yamasa yawa, yana buqatar mace,da tunanin maganar auren nasa yashiga Dakin Nata, saide abun mamakin yana tura qofar yaji ta abude, tana zaune akan gado tabawa qofar Dakin baya,dinkin dake jikintane yamasa kyau, shiyasa ya tsaya daga bayanta yajingina da jikin qofar Dakin yana qare mata kallo, wannan ne Karon farko da yaji tsoron yiwa matarsa magana saboda auren dayake shirin yi, munirat kuwa waya take, kwata kwata ba taji shigowar saba, tariga tasan cewa baya gidan shida mahaifiyar tasa, shiyasa Hankalinta kwance taci gaba da fadin"suna dawowa zan sanar daku, zan San yanda zanyi in sakawa securities din maganin bacci alemo susha, Kuna ganin wayata kuzo ku kashe ta"(🙆🏻‍♀️)

Cikin tsananin tsoro, mamaki, dakuma firgici, Shahaab yazaro Idonsa waje(😳)
waza'a kashe?
Gabansa ne yafara faduwa, magana zaiyi mata, Amma saitaci gaba da cewa"karku damu, nafada muku babu matsalar komai, zan turo muku photon gidan, da inda zaku shiga har cikin dakinta, nafada muku Kuna zuwa kawai ku kashe ta, na tsaneta!, na tsaneta!!, na tsaneta!!!, tashiga cikin rayuwa ta tayi min Kane-Kane, ta hanani Zaman lafiya da mijina, harni zata bude baki tana fadawa zai qara aure, lalle-lalle ku tabbatar kun aiwatar da abinda nasaku,tsohuwa ce bazata muku wahalar kisa ba, Kuna kashe ta kushigo Nan Nima ku yanke ni, yanda baza'a gane dasa hannu na aciki ba, itama yarinyar dazai aura zan dawo kanta, karku kira wayata zan dinga kiranku idan buqatar hakan tataso"

Ruf idon Shahaab suka rufe, kwata kwata saiya daina ganin komai, baisan lokacin da qafafun sa suka fara rawa ba, saiji yayi yafadi qasa jagwab, salati yake acikin zuciyar sa, banda hannunsa guda daya da yakeji yana masa rawa, dayan Kuma ba yayi, saikace Wanda cutar 6arin jiki takeso ta kamashi, cikin ikon Allah yana motsa hannunsa yana salati har yaji hannun nasa yadena rawa, Idonsa yabude ras!.

Tun lokacin daya fadi tajuyo ta kalleshi, idan qirjinta yayi dubu, to yau gaba dayansu saida suka fadi, yanda gabanta yake luguden faduwa harji tayi kamar wani abu yafada cikinta, lokaci daya jikinta yad'auki karkarwa.

Shikuwa Shahaab wani irin kallo yake mata na tsoro, kisa!? Kisan mutum Kuma mutum dinma ba kowa ba Sai mahaifiyar sa?

Lokaci daya Idonsa yayi jajir!
Cikin sauri yatashi yawuce dakinsa, yana zuwa ya zauna akan gado tare riqe Kansa dayake masa barazanar rabewa gida biyu, wani irin kuka ne yazo masa Wanda Rabon Dayayi wannan kukan harya manta, kuka yake sosai harda shashsheka, acikin wannan halin tashigo Dakin nasa ta sameshi, tana zuwa ta zuba gwiwarta aqasa tareda sakin wani irin kukan, tsawon lokaci suka dauka Ahaka, shi yana kuka itama tanayi, saida taga bashida niyyar ce mata komai sannan tasa hannu ta riqe qafafun sa tace"my Dear, Dan Allah kayi hakuri, wallahi nadena, natuba kayafemin, bada nufi nayi hakan ba, kayi hakuri bazan sake ba"

Taqarasa maganar tana dora kanta akan tafin qafafun sa, cikin sauri ya d'ago Kansa tareda goge Hawayen Idonsa, muryarsa adake, kamar bashine yayi kukaba yace"MUNIRAT, kitashi kitafi gidanku daga yau Bana buqatar ki acikin rayuwa ta"

Cikin sauri ta d'ago ta kalleshi, hannunta tahade waje daya tace"mahmud nikake Kora daga gidanka yau?idan nayi niyyar aikata kuskure ashe bazaka Jani a jikinka ka nunamin illar hakan ba?Saboda kasamu wadda tafini?"

Runtse Idonsa yayi, cikin tsawa yace"munirat na tsaneki, nadauki yarda nabaki, na amince dake, nasoki fiyeda kowa abaya, banajin maganar mahaifiyata saboda soyaiyar danake miki, mama na itace komai nawa, itace mahaifina itace mahaifiyata, ban rageki dakomai ba amma kin dauki filayenta kinje kin siyar,banyi miki magana ba, kinsan ko saboda me? Saboda Ina sonki, qawayenki sun hada min vedio na banza da 6atanci nida yarinyar datake ganin darajar mahaifiyata kamar Tata mahaifiyar, sun turo miki, kin dauki gaba Dani, kin hanani haqqi na, now saboda maganar aure Harkina cewa kin tsani mama,aje akashe ta, akashe min mahaifiya ta munirat? Sakamakon dazaki nunamin kenan? Wannan shine tukwicin soyaiyar Dana nuna miki abaya? Yanda kikace kin tsaneta Nima na tsaneki munirat, kiyi hakuri bazan iya cigaba da zama da wadda bata qaunar mahaifiya taba, kifice daga gidannan, kifice daga unguwar Nan,kifice daga cikin rayuwa ta"

Gabanta ne yasake faduwa, dama yasan da maganar takardun data sace? Wata irin tsananin kunya ce tasake rufeta, taji kamar qasa ta tsage ta shige ciki, lokaci daya jikinta yayi Sanyi kalau, bata taba nadamar abinda take aikata masaba Sai yanzu, ta Kuma yi Imani tabbas Mahmud yana sonta, domin kuwa Mai sonta ne kawai zai'iya yin haquri da maganar filayen Nan batare Dayayi mata hukunci ba, ta kalleshi Tace"Mahmud...."

Kafin taci gaba da magana ya dakatar da'ita ta hanyar daga mata hannu(🤚🏻) yace"munirat, namiki saki daya, kitashi kitafi gidanku"

Cikin tsananin firgici tasake cewa "Mahmud...."

Idonsa ya runtse, ko kadan baison sake ganin fuskarta, cikin 6acin rai yasake cewa"munirat, namiki saki na biyu kitashi kibar min gidana"

Zaro idonta tayi, mamakine yasa tasake cewa "mahmu...." kafin ta qarasa cewa Mahmud din, yasake cewa "munirat.....namiki...."

Cikin sauri tatashi tafice daga d'akin tana kuka mecin rai, ta tabbatar idan bata fitaba, yanda ransa yake a6ace, to idan Ana saki goma, yau zai iya yimata shi.

Ko Kallan dakinta bata Kuma yiba, ta warware Dan qaramin mayafin data daura akanta, ta nufi bakin get tana kuka me tsananin ciwo

(haba Shahaab.... 😭😭😭)

(wayyo Anty Munirat 🥹🥹🥹)

Allah ka rabamu da sharrin zuciya 🤲🏻

Shahaab littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda Allah, nide ban yafe ba

300 kacal
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034

Mrs Usman ce✍🏻

Page 25

Kasancewar ta matar megidan yasa kokusa basuyi kuskuren hanata fita daga gidan ba, hankalin megadi yaqi kwanciya, ya hanzarta zuwa cikin gidan, yasamu mama tana dudduba kayan da Hajja ta hado mata tataho dashi a leda, cikin rawar jiki Yace"Hajiya...ga Hajiya qarama can tafita tana kuka, da alamun ba lafiya ba, shine nace Bari nazo na sanar dake"

Cikin sauri mama tatashi tace"subhanallahi, Bari inje part din nasu"

Tashi tayi tafice ta nufi part dinsu, zata Iya cewa rabonta data zo part din Shahaab harta manta, saboda bata zuwa gudun kar taga abin 6acin rai, ita Kuma bazata iya yin shiru ba.

Saide tana zuwa tayi sallama taji shiru, Kai tsaye dakinsa ta nufa, yanayin data ganshi aciki ne yasa gabanta faduwa, wani irin numfashi Shahaab yake fitar wa kamar wanda yake gab da shirin mutuwa, salati tasaka tafara tatta6a jikinsa taga abu yaqi qarewa, cikin sauri tad'auki wayarsa ta sanarwa da doctor halin da ake ciki, sannan takira Ramadan shima tafada masa.

Zama tayi tajashi jikinta daqyar, ta dora Kansa akan cinyarta tafara Tofa masa addu'ah, cikin Yan mintuna qalilan doctor yazo, cikin sauri yafara dudduba shi, dayake yazo da kayan aikinsa Kai tsaye ruwa yafara daura masa, yayi masa allurar bacci, sannan yafara harhada wasu alluran, Adede lokacin Ramadan yashigo Dakin da gudu, kan Shahaab din yanufa gabansa banda faduwa babu abinda yake, ko kallon mama baiyi ba yadubi doctor yace"yaya ake ciki? Meyasame shi?dazu dazu fa mukai waya dashi"

Saida yagama hada alluran yayi masa, sannan ya kallesu yace"bawata matsala bace babba, damuwa ce ta masa yawa, saide Kuma kuyi haquri, hawan jini ya kamashi, Dan da ba'a kirani akan lokaci Bama yanayin dayake ciki, zai iya haifar masa da cutar paralyzed, Amma nayi masa allurai,idan yagama baccin zai tashi lafiya insha Allah, Sai abashi wannan magungunan yasha, please Hajiya akula da abunda zai sashi damuwa Dan Allah"

Cikin damuwa mama tace"likita idan akwai damuwa afita dashi qasar waje kawai"

Murmushi yayi yace"Hajiya mama idan abun yayi tsanani nida kaina zance akai shi, nafada miki babu komai, damuwa ce tamasa yawa"

Cikin sauri tace"to wacce irin damuwa ce zata dameshi shida yake shirin zama ango? Nafi tunanin dawowar mu gida ne yanzu, saboda matarsa tafita tana kuka"

Cikin ladabi yace"idan kinyi min izni zan iya tafiya?"

Cikin sauri ta d'aga masa Kai tace"babu damuwa, idan yafarka,zan kiraka"

Daga haka yajuya yafita, mama ta kalli Ramadan daya dafe goshinsa da hannunsa Kansa yana sunkuye, duk wannan batun da ake Kansa yana qasa, yayi Nisa cikin tunani menene yake damun abokin nasa har ya haifar masa da hawan jini?

Mama ta kalleshi Tace"Ramadan ko kunyi magana dashi ne yafada Maka wani abu?"

Ajiyar zuciya yasauke yace"mama munyi magana dashi de ansaka ranar aurensu, Bayan haka yacemin idan yadawo gida zai nemeni,Amma ni Hankali na yaqi kwanciya kode zamu dauke shi daga Nan ne? Gara a fitar dashi mama, banason abinda zai ta6a lafiyarsa, saboda ta ko'ina muna buqatar sa acikin rayuwar mu"

Mama tace"dawowarmu kenan, ni Ina zaune megadi yacemin inzo munirat tafuta tana kuka, Ina zuwa saina ganshi a wannan hali Sai numfashi yake ja baima San inda Kansa yake, Amma mu bari yafarka din mugani, idan da sauqi shikkenan, idan Kuma da damuwa kawai saimu tafi"

Ajiyar zuciya yasaki yace"toshikkenan"
Chapter 48 · 0% Book details