← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 48

Sashe 7

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe garin daurin auren ne ya dauki matarshi da kawayenta biyu suka kamo hanyar kano, tunaninshi ďaya shine yadda zai fara tinkarar zeenatu da maganar ya auri oyiza saboda sam duk wainar da ake toyawa bata sani ba, ita dai taga ana ta aikin gyaran part din gefenta sama da kasa amma sam bata kawo aure yayi a ranta ba, sai gurin bakwai suka shigo garin kano, kallon garin oyiza da esther keyi har suka kawo kofar dankareran gidan alhj basheer dake zoo road,
a kofar gidan alhj bara'u ya hango su tsaye shi da malam atiku suna hira, ganin motarshi yasa suka mike suka karaso gurinshi da saurinsu, ya leko ta cikin glass cikin fara'a suka gaisa, yace ga amarya fa ku gaisa,
alhj bara'u yayi dariya yace wace amaryar kuma, alhj basheer yace amaryata da aka ďaura min aure da ita jiya,
malam atiku yace shine ko labari ranka ya daďe to Allah ya sanya alkhairi sannu amarya,
oyiza ta gyara gyalenta tace yauwa, alhj bara'u ma yayi mishi addu'a suka ja suka tsaya shi kuma ya danna kai cikin gida kirjinshi na duka sosai, parking yayi suka fito duka su ukun suna mika gasu ďirka2, sannu alhj basheer yace musu sannan ya fara tafiya suna binshi a baya,
yana buďe kofar main parlon yayi arba da zeenatu cikin kyakykyawar shigar material dinkin stone work fatar nan tata sai kyalli takeyi ga wani kamshi da sanyin dadi ko'ina a cikin parlon, da sauri ta karaso tana mishi sannu da zuwa,, gabanta ya faďi sosai da ta hango su oyiza amma sai ta kara fadada fara'arta tana musu sannu da zuwa, karasawa sukayi cikin parlon suna yabawa da kyau da tsarin parlon ga kuma kula da yake samu ta musamman,
zeenatu ta nuna musu guri suka zauna ta wuce kitchen cike da tambayoyi a zuciyarta, kayan shaye2 ta kawo musu da snacks tanata yake,
ta kalli alhj basheer da ya dafe kanshi tace yallabai gajiyar ne, tashi muje ciki kayi wanka,
oyiza cikin kishi ta watso ma zeenatu harara,
alhj basheer yace zauna zeena akwai maganar da nakeso muyi dake,
ta nemi guri kusa dashi ta zauna,
a hankali ya fara magana yace sai kuma kika ganni da baki,
tayi murmushi tace eh,,
yace dafatan zaki fahimceni zeenah, kinsan komai nufi ne na Allah kuma matar mutum duk inda take sai ya aureta,
ya nuna oyiza yace wannan matata ce jiya aka ďaura min aure da ita bawai dan inci mutuncinki ko kuma dan bana sonki ba, "a'a" wannan auren ki ďaukeshi kaddararre ne daga Allah kuma babu mamaki safiyya na tafe da alkhairai masu yawa cikin gidan nan,
zeenatu da tayi mutuwar zaune tayi maza ta saita kanta ta kirkiri murmushi tace kaii barka Allah ya sanya alkhairi nayi maka murnar samun karuwa,
ay aure cigaba ne yallabai Allah ubangiji ya bayyana alkhairan dake cikin wannan auren kuma alkhairan ya wanzu a tsakaninmu,
yace ameen yar albarka zeenatu nagode sosai da kika fahimceni,
tace ba komai yallabai bana jayayya da abin da Allah ya kaddara Allah ya bamu zaman lafiya,
yace ameen, nan yayi introducn zeenah a gurin oyiza da irin muhimmacin da take dashi a gurinshi,
oyiza ranta ya baci da irin praisn zeenah da yakeyi a gabanta da kawayenta,
bayan ya gama maganganun da zaiyi yace ma oyiza su tashi ya nuna mata part dinta, suka mike kamar samudawa suka rataya jakunkunansu suka wuce,
zeenah da kiris ya rage ta fashi da kuka ta danne kishinta ta shiga kitchen ta hado musu abinci ta kai musu dakinsu ta fito tayi nata dakin ta rufeshi da key ta faďa gado tanata rusa kuka,

Can dakin oyiza kuwa bin ko'ina sukeyi ita da kawayenta suna tsalle suna murna ganin irin dukiyar da alhj basheer ya zuba a ciki, zama sukayi a kan gado esther tace oyee baby sai kinyi da gaske da wannan matar dan da ganinta ta iya munafurci, evelyn tace green snake kenan, gata very pretty, gaskiya akan matar nan na kara yarda black is beauty kuma suna kama da bash,
oyiza tayi tsaki tace trust mee mana ai matar nan sai mai aikina ta fita daraja bari dai in haihu, kunsan bata haihuwa kuma na riga na gano abinda alhj yafi so a rayuwarshi kenan haihuwa,
ta shafa cikinta tace baby boy zan haifa maka alhj a lokacin ne zan nuna karfin ikona a gidanka,,
duk suka kwashe da dariya evelyn tace shegiya a ina kika san baby boy zaki haifa, oyiza tace bansani ba amma dat's wat I want kuma zan samu kinsan ni duk abinda nake so sai na samu, suka kara kwashewa da dariya suka cigaba da hira har dare ya raba sannan sukayi bacci oyiza batai maganar sallar magrib da isha ba,
wa ma yasani ko tayi na safe da rana ohooo......

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:33] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Tun daga ranar suwaiba ta samu gurin zuwa su zauna suyita hira suna shewa suna kulle kullensu dan ta kuntatawa zeenatu, anan suwaiba ke yini In ba ranar girkinta bane,
ko kallon zeenatu ta daina yi, saboda ita a ganinta tayi kawa wacce zata ci arziki da ita kamar yadda ma'u ke ci da zeenatu,
(bata san bomb ta samu a madadin kawa ba)..

Watansu uku da aure oyiza bata fara nuna komai na halin tsafinta ba,
sai dai abinda ke bawa alhj basheer mamaki game da ita shine rashin sallarta, ko ya matsa mata tayi sallah to fa zata san yadda tayi ta zille dan baza tayi ba,
gurin zeenatu kuwa mugun kyankyamin cin abincin oyiza takeyi saboda sam bata yarda da musuluncinta ba, ko sun haďu a dinning ana cin abinci sai tace ita yanxu abinci mai nauyi bata mata cikinta yakeyi,,

a cikin wannan lokacin ne oyiza ta fara laulayi mai zafin gaske,
komai bata iya ci, haka ta tsani kamshin gidan gaba ďaya, tunda alhj basheer yasan ciki ne makale jikin oyiza shikenan duk wani kula da soyayya ta duniya ya ďauka ya daura mata,
babu dama zeenatu tayi abu in oyiza tace bata son kamshin shi to fa shikenan zai hauta da faďa sosai kamar tababbe,
suwaiba ce ke shigowa ta kula da ita suyita yada habaici dan zeenatu taji haushi, duk da zeenatu na jin haushin abin amma sai ta danne ta dinga tambayar oyiza ko akwai abin da takeso, ko kallonta oyiza batayi bare ta bata amsa,
abubuwa suka hadu sukayi ma zeenatu yawa, gashi sam mijinta ya juya akalarshi gurin kula da oyiza a cewarshi,
gurin Ma'u da amaryar da Alhj bara'u yayi kadai zeenatu ke samun sauki,

Kayan baby babu wanda alhj basheer bai siyo ba a nan nigeria da waje, kuma duk kayan maza ya siya dan a scaninng an tabbatar mishi namiji ne, itama chummy ta tabbatar mata namiji zata haifa, gaba daya oyiza ta gama wasa wukarta dan ta gama hada plan din yadda zata mallake gidan da duk wasu kadarori na alhj basheer,

Cikin oyiza ya kusa wata tara alhj basheer ya ďauketa suka tafi india acewarshi zasu fi samun kula ita da babynshi,
tafiyarsu ita tasa zeenatu tasamu sauki take bacci da adduointa cikin kwanciyar hankali, da rana su ma'u da Abida amaryar Alhj bara'u su shigo su ďebe mata kewa da bata shawarwari duk da Abida itama ba isashshen lafiya gareta ba saboda cikin dake makale jikinta na wata hudu,

A daren ranar talata ta idar da sallar tana shirin kwanciya taji ringing din waya, daukar wayar tayi taga alhj basheer ta dauka cikin mamaki dan rabonshi da ya kirata har ta manta,
sallama ta mishi ya amsa murya babu walwala tace ya mai jiki, yace da sauki ta sauka lafiya,
zeenatu ta washe baki tace Allah ya raya ya kuma bata lafiya, me muka samu,
kukan da oyiza ke yi ya hana shi bata amsa, kuka takeyi sosai tana fadin ya za'ayi ace ya' mace ta haifa,
tsawa ya daka mata yace to ubanwa kike tunanin ya canza miki, ko wannan din ke kika bawa kanki,
ki rufe min baki kar ranki ya baci,
zeenatu ta kashe wayar da sauri ta hau gado ta dukunkune (nidai bansan me ke ranta ba a wannan lokacin, farin ciki ne ko kuma tausayin oyiza,, masu kishiya su bamu amsa plss..)..

Satinsu biyu a india suka dawo gida cikin koshin lafiya,,
tun acan ya raďa mata sunan mahaifiyar oyiza wato Salamatu (ummu Salma) tunda suka dawo makota ke shigowa yi mata barka, suwaiba sai tausarta takeyi akan gara ita tana haihuwa ba juya bace,
wannan kalaman na suwaiba suna matukar sosa ran zeenatu su ke sata kuka a kullum dare da rana tana rokon Allah akan ya bata farin cikin rayuwa itama,
dan haihuwa farin cikin rayuwa ne, in ka haihu ka wuce bakin cikin duniya da lahira,
ya Allah ka azurta wadanda basu haihu ba da ya'ya masu albarka cikin gaggawarka bata shaidan ba,
wadanda suke dashi kuma Allah ka shiryar mana kuma ka tayamu raino ameen thumma ameen.....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣2⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Shekarar ummu salma uku, in ka ganta sak uwarta gata katuwa kamar renon agric, tana matukar samun kulawa gurin mahaifinta dan ba kananan kudi yake kashe mata ba,
a wadannan shekarun banda karfin imani da salatin annabi da tuni zuciyar zeenatu ta buga saboda ko kallo kwakwkwara tayi ma ummu salma to fah zata fashe da kuka ta dinga nunata, shi kuwa alhaji basheer babu bincike babu komai zai hauta masifa wani lokaci harda gorin haihuwa,
zeenatu sam ta kasa gane kan mijinta saboda kullum alamuranshi kara tabarbarewa sukeyi sam babu sauki a tare dashi game da ita dan ko hanyar dakinta baya bi, ta ma manta rabon da su kebe tare a matsayin mata da miji,

Oyiza kuwa yanzu burinta ta samu ciki amma kafin ta samu sai ta shirya tsaff saboda wannan karan bazata taba yin sakacin haihuwar ya mace ba, sai kace ita zata bawa kanta haihuwar,,
( kaii Rashin ilimin addini shine babbar cuta a rayuwar dan adam)
Chapter 7 · 0% Book details