← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 48

Sashe 33

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan fitar hajja da kamar minti uku kaka liman ya kalleta yace ya mai gidan naki,
Afeeyah tace yana nan lafiya kaka,
kaka liman yace lafiyar ciki ko ta waje,
Afeeyah ta dago cikin rashin fahimta tace ban gane ba kaka, yace ina nufin wace irin lafy, lafiyar koshin lafiya ko kuma ta duka harda kwakwalwa,
Afeeyah tace lafyr koshi kaka, sannan lafiyar kwakwalwarshi ma ina tantama akanta,
wani lokacin in yayi abu kamar cikakken me lafy baya mintina kuma sai ya koma kamar da,
kaka liman yace to yaya kika fahimci mutanen gidan, ina nufin a tunaninki wane irin zama sukeyi da yaron nan, kina ganin suna kaunarshi tsakan--- sammm ta katse kaka liman, tace muguwar tsana sukayi mishi wallhy,
amma a gaban daddy sai su nuna basu da kamarshi, sannan kaka bata barinshi yayi sallah, duk wata ibada bata barinshi yayi, sannan kaka jiya da dadd--- yayi saurin katseta yace tambaya daya nayi miki, bari in yi miki cikakkun bayanai akan abubuwan da baki fahimta ba tukunna sai mu shiga wani,

mijinki ba lafiyar koshi kadai gareshi ba harda ta kwakwalwa,
tambayarki zanyi,? tsakaninki da Allah kinajin zaki iya yin duk abinda ya dace domin ki kubutar da mijinki daga wannan halin da yake ciki,?
Afeeyah ta gyada kanta tace zanyi kaka,,, yace yauwa yar albarka,

Ki sani mijinki ya samu saukin tabuwar da kwakwarshi tayi sai dai kuma azababben sihirin da ake mishi shi ke kara dagula kwakwalwar ya rasa fahimtarshi ya dinga yin abu kamar yaro, wani magani ake bashi wanda idan yayi awa shida bai sha ba zai iya dawowa mai lafiya amma ba sosai ba saboda akwai wasu tsibace tsibbacen da aka birne a cikin gidan wanda gano su sai ansha matukar wahala,
duk ranar da aka hako wadannan asiran to wannan ruwan maganin ya daina tasiri a jikinshi domin duk wata tabuwar kwakwalwa zata barshi, karki ce sihirin wasa akayi mishi, wannan na gasken gaske ne wanda yake da matukar wahalar karyewa, kin fahimceni ko, Afeeyah ta gyaďa kanta tace ay kaka duk abinda aka ce min matar nan zatayi bazan musa ba saboda ni ganau ce ba jiyau ba,,,
shigowa dakin sukaji anyi babu sallama,
da sauri suka waigo dan ganin ko waye.......

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Oyizah suka gani tsaye idonta kyarr kan Afeeyah, gefenta kuma salma ce rike da basket din abinci,
gaban Afeeyah sai faduwa yakeyi a zuciyarta tana adduar Allah yasa bata ji tautanawarsu ba,
gyaran murya kaka liman yayi ya kalli oyizah yace an wuni lafiya,
da sauri ta kauda kanta tace lafiya lau ta karaso gaban gadon Afeeyah jikinta a mace tace ya jikin,
da sauki Afeeyah ta fadi ba tare da ta kalleta ba,
salma kuwa ajiye basket din tayi ta koma gefe tana cika tana batsewa,
mikewa kaka liman yayi ya kalli Afeeyah yace bari in koma,
Kiyita "hasbunallahu wa ni'imal wakil" saboda maganin musibun duniya, Allah ya kara sauki ya kuma inganta abin dake cikin ki,
Afeeyah tace ameen kaka nagode yaushe zaka dawo,
yace too zan dai gani amma ay bazan koma ban sake dawowa ganin jikin naki ba, tace to sai ka dawo kaka,
ya kalli oyizah da kanta ke kasa yace to hajiya sai anjima ko, tace to sai anjima,
har ya fita ya kuma lekowa yana kallon kwandon abincin yace
"ki danne kwadayinki, in har ya taso miki to ki tambayi goro a baki domin kwantar dashi kin gane ko"
Afeeyah ta kalli kwandon nan take ta gane manufarshi tace to kaka nagode,

Oyizah da ta tabbatar kaka ya tafi sai ta dago kanta ta zauna ta dafa Afeeyah tace sannu, amma jikin da sauki ko,
umm kawai Afeeyah tace,
oyizah tace kin ci abinci kuwa,
Afeeyah ta yatsina fuska tace bana iya cin abinci amai yake sani, oyizah tayi murmushin mugunta tace shiyasa na dafo miki abincin da nasan masu ciki naso,
salma ďan zubo mata,
Afeeyah tayi saurin cewa a'a ta barshi doctor yace a daina bani abinci saboda aman na wahalar dani, oyizah tace doctors din nan sun cika iyayi manta dasu kici babu aman da zakiyi,
Afeeyah tace saidai ko zuwa anjima dan yanzu bacci nake ji, oyizah zata kara magana cikin bacin rai salma ta katseta tace haba mummy dole ne, ji yadda kike wani pettn dinta tunda tace baza taci ba ba sai ki kyaleta ba, cikinta,,,,
oyizah ta harari salma tace baki san me lalurar ciki sai an matsa mishi yake cin abinci ba,
ko so kikeyi in bari ta wahalar min da jika,
Afeeyah ta kwanta tace uhmm,
oyizah tace rabu da salma kinji bata san lalurar ciki ba shiyasa, salma tayi tsaki ta tashi ta fita daga dakin tana mamakin yadda mummy ke lallaba wannan yar iskar yarinyar,
babu yadda oyizah batayi ba akan Afeeyah taci abincin da ta kawo amma firr taki, har hajja ta shigo tasa baki Afeeyah tace ita sam yunwa ne bataji kuma tana ci zatayi amai,
oyizah ta boye bacin ranta tace to hajja anjima ki tabbatar taci saboda bai kamata mai karamin ciki ta dinga zama da yunwa ba,
hajja tace karki damu in shaa Allahu zata ci, oyizah ta dan kara zama shuru kafin ta tashi tayi musu sallama haďe da jaddada ma hajja akan ta kula da Afeeyah ta dinga cin abinci akai2,

cikin mamaki hajja ta kalli Afeeyah tace kin ga matar nan yadda ta canza kamar ba ita ba, gaskiya naji dadin yadda ta nuna kulawarta gareki ga dukkan alamu ta saduda ta fara sonki,
Afeeyah ta juyar da kanta gefe a zuciyarta tace kwarai kuwa tana matukar son kasheni hajja ai dole ta kula dani kafin hakanta ya cimma ruwa,
buďe kulolin abincin hajja tayi tana fadin masha Allah irin wadannan namomi haka,
Afeeyah tayi saurin mikewa tace hajja dan Allah a ina zan samu agwaluma ko cashew anan gurin,
hajja tace aiko akwai wani mai agwaluma da na gani anan waje bari in duba Allah yasa bai tafi ba,
Afeeyah tace ameen dan Allah hajja ya baki mai tsami sosai, hajja tace to ta fita da sauri,
tana fita Afeeyah ta mike ta kwashi kulolin abincin tayi waje dasu ta zuba a bola tayi saurin komawa daki, ko minti biyar hajja batayi ba ta dawo da agwaluma cikin leda ta mika mata,
kwanciya Afeeyah tayi ta dauki agwaluma daya ta fasa ta fara sha,
salatin hajja ne yasata juyowa da sauri tace lafiya hajja,
hajja tace kulolin ne naga babu komai, Afeeyah tace eh na cinye baki ga dama na mutum daya ta yi ba, hajja tace daga fita ta har kin cinye, Afeeyah tace eh mana to nawa abincin yake,
hajja tace shine dan bakar mugunta ko naman baki ragemin ba,
Afeeyah tayi dariya tace ke kuma nama ne aranki sai kace wata kurah,
hajja tace waya sani ko kurar ce gaskiya kin shiga hakkina,
Afeeyah tace karki damu hajja nah anjima nasan zamu samu wasu naman,
hajja tayi tsaki ta tashi ta fita wanko coolers din...

Bayan isha'i kaka liman ya dawo asibitin, sun dade suna hirah da hajja kafin ta basu guri shi da Afeeyah,

kaka liman ya kalli Afeeyah yace dazu muna magana bamu gama ba na tafi,
yanzu sai muyi sauri dan naji gobe za'a sallameku ko,
Afeeyah tace eh,
kaka liman yace nima goben zan koma,
da fatan duk abubuwan da na fada miki dazu kin fahimcesu ko,
Afeeyah ta gyada kanta,
yace yauwa to yanzu sai ki faďa min abinda kika gani,
nan Afeeyah ta faďa mishi duk abinda ta gani jiya da daddare,
kaka liman ya jinjina kanshi yace wannan shine abinda nakeso Allah ya nuna miki dan nasan da na faďa miki hakan tun farko to tsoro bazai barki ki shiga gidan ba ma bare har tausayin affan ya shigeki ki yarda da taimakon da zakiyi,
wannan abun da kika gani shi jabeer ya gani amma nashi ya banbanta da naki saboda shi yaji suna tsafin ne akan Affan da mahaifiyarshi,
shin tunda kika shiga gidan kinji ko sau ďaya alhj yayi maganar zeenatu,
Afeeyah ta gyada kanta, kaka liman yace to bashi ba ma har yan uwanta da makusantanta basa iya maganarta ko ke kin taba tuna ta tun bacewarta,
cikin mamaki Afeeyah tace a'a kaka,
Chapter 33 · 0% Book details