Sashe 20
Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
wani kauye suka je a cikin kasar Nigar mai suna "Tsatsunburum (s Burum)"
kauyen bashi da nisa da zangon daura, gaba da gidan sarki sukaje kaka liman yace ya tsaya anan,
jabeer ya kalli gurin,
a katange yake da wata katuwar bishiya a ciki, kaka liman ya fito ya shiga gurin jabeer na binshi a baya, ashe wata katuwar rijiyace a cikin gurin mai cike da tarihi,
kaka liman ya kwance ledar da ya zo da ita ya fito da wasu layu da magunguna ya fara haka rami ya binnesu sannan ya ďauko wata gora a cikin jakarshi da magunguna a ciki yasa hannu a cikakkiyar rijiyar ya debo ruwan cikinta sannan suka fito daga gurin,
jabeer dai kallon gurin yakeyi ga rubutu a jikinshi amma rubutun ya fara gogewa,
ya kalli kaka yace kaka amma wannan rijiyar tana kunshe da tarihi ko,
kaka liman yace kwarai kuwa,
abin al'ajabi ya taba faruwa a gurin nan,
ya nuna mishi wata bishi dake dan nesa kaďan da gurin yace kaga waccan bishiyar, jabeer yace eh kaka, yace to daidai saitinta da gurin kiwon shanu ne, shanaye da yawa ake kiwo a gurin, "akwai wata saniya guda ďaya kullum aka bata abinci sai taki ci haka ruwa, saidai a ganta kullum da yamma tazo nan gurin da muka shiga kafin a katange shi ta daďe a gurin har sai dare take komawa cikin yan uwanta, kullum haka takeyi sam bata cin abincin da ake basu, ana cikin haka rannan sai mai shanun ya dinga binta a baya dan ganin abinda takeyi a gurin, yana zuwa gurin yaga ta kafa kanta a wani ďan tsukukun rami tana shan ruwa, tana gamawa yaga ta kwanta karkashin bishiyar nan lokacin tana karama sosai a gurin take bacci har dare sannan ta koma cikin yan uwanta, in takaice maka dai wannan saniyar tunda ake kiwonta bata taba cin abinci ba wannan ruwan shine ya zamo ruwa da kuma abincinta sannan wannan bishiyar ta zamo gurin hutu a gareta har ta mutu a gurin, bayan ta mutu ne mutane suka haka wannan ramin ya zamo rijiyar da bata taba kafewa ba duk wahalar ruwan da akeyi a garin tofa wannan rijiyar na nan da ruwanta sannan wannan bishiyar tana nan bata taba fadi ba shekaru fin 100 dan nima labari aka bani,
jabeer yace ikon Allah shine aka katange ta, kaka liman yace kwarai kuwa kuma cikin ikon Allah ruwan cikinta yana zama waraka ga duk wanda ya yarda da Allah kamar yadda ta kusugu take,
jabeer yace Allah ya kara ma Annabi daraja, kaka yace ameen jabeer shiga muje dan zan ga Aminina "Maina dogon yaro" shima akwai abin da zai bani daga nan mu wuce cikin daura mu karasa,
jabeer yace to kaka, suka shiga mota suka wuce jabeer na kallon girman bishiyar yana tasbihi ga Allah...
Sai bayan magriba suka gama komai suka dawo gida a gajiye,
dakyar jabeer ya iya taba abincin da Goggo ta kawo mishi sauri2 dan yana son ya dauki hanyar gida komin dare,
babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwana yace samm bazai kwana ba dan gobe da wuri yake so fara aiwatar da aikin cikin gidansu Affan wanda shine mataki na karshe na aikin,,
sai da yayi isha' sannan kaka liman ya fito yayi mishi rakiya yana kara nuna mishi yadda zaiyi amfanin da maganin yana kuma mishi faďa akan yayi taka tsantsan da oyizah,
jabeer ya shiga mota yace in shaa Allahu kaka zanyi duk yadda kace, mun gode sosai, kaka liman yace to Allah ya tsare kayi tuki a hankali ďan boko, jabeer ya tada motar yace baka da matsala tsoho, yaja motar suna ďaga ma juna hannu, saida yaga kulewar motarshi sannan ya juya gida,
haka kawai ya tsinci gabanshi da tsananin faďuwa,
a waje ya zauna yana bin sawun motar jabeer da kallo yana mishi adduar Allah ya kiyaye hanya...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah
★ 9:54pm ★
Tun bayan magriba hadari mai tsananin duhu ya taso yana kokarin haduwa a gabas,
iska ce mai dadi taketa kaďawa a wannan lokacin har zuwa karfe 9:32pm, lokacin ne hadarin yamma ya kusa haďuwa da na gabas, iska mai karfin gaske haďe da guguwa da walkiya su keta tashi ta ko'ina kamar zasu tashi gidaje da motocin biladama,
yaf yaf ruwan feshi ke busawa a cikin iskar,
A wannan lokacin gudu jabeer yakeyi cikin motarshi yana Allah Allah ya isa kano kafin goma ko kuma goma daidai,
wuce motoci yakeyi yana tafiyarshi cikin kwanciyar hankali yana wiping yayyafin dake sauka a kan glass din motarshi, karfe 9:50 ya rage saura k.m baifi 15 ba ya shigo garin kano, murna ya dinga yi dan yasan in shaa Allahu kafin 10:30 zaiga Afeenshi,
har ya dauko wayarshi zai kirata sai ya fasa so yakeyi kawai ta ganshi kafin lokacin da ya daukar mata..
Wani haske ya gani ya gifta gabanshi hade da girgiza mai karfi wacce tayi sanadiyyar fitar tayar motarshi ta gaba,
runtse idonshi yayi sosai yana kalmar shahada saboda yadda yaji shi a sama motar na juyawa sosai, wasu masu trailer sukayi parking gefen hanya suna salati cikin tsoro saboda yadda motar ke wulwulawa a sama,
saida tayi minti uku a haka sannan ta daki wani katon dutse ta tarwatse a kasa dai2 lokacin ruwa mai karfi ya tsuge haďe tsawa, mutanen gurin kowa ya kunna full light dinshi suka karasa kusa da motar jiki na rawa saboda basu taba ganin accident irin wannan ba,
ba karamin dagargajewa motar tayi ba, nan da nan suka fara kokarin ciro mutumin da suka gani a gaban motar, da kyar suka iya ciro jabeer saboda wani karfe da ya shige cikin hancinshi ya bullo ta kanshi,
kuka mutanen gurin sukeyi suna salati saboda sun tabbatar da wanda suka ciro a cikin motar nan bashi da sauran rai,
da sauri suka soma bincika aljihunshi dan motar babu abin dauka a cikinta, driving licences suka gani sai kudin da ya baci da jini ko ta ina,
farar shaddar jikinshi ma babu wanda zaice fara ce dan duk ta koma ja, basu samu adress dinshi jikin d.l din ba sai dai sunanshi,
daukarshi sukayi cikin mota suka shigo cikin garin kano suka zarce police station dashi,, (innalillahi wa inna ilahir rajiun)
A kuma dai2 wannan lokacin Affan na zaune kusa da daddynshi suna dan taba hira duk da rabin hirar tasu shirme ce,
a hankali ya karkatar da kanshi yana kallon daddy idonshi ya ciko da kwalla yace daddy yau ma kaga har dare yayi abokina baizo ba, ya kalli inda ya tara wasu fararen duwatsu guda 8 na kirga yace daddy kagani yau kwana 8 kenan,
alhj basheer ya shafa kanshi yace kayi hakuri Affan kasan yanata shirye shiryen biki dole ka rage ganinshi,
Affan ya marairaice fuska yace to daddy ni yaushe zaka min aure, alhj basheer yayi dariya yace duk ranar da ka shirya Affan,
Affan yayi dariya shima yace daddy ay na shirya, daddy yace to wacece matar,
Affan ya rufe idonshi yana girgiza kai fuskar Afeeyah nata mishi yawo a cikin kwayar idonshi da kwakwalwarshi,
yayi saurin bude ido yace Barbie din jabeer, daddy ya kara sautin dariyarshi yace wacece kuma barbie, Affan yace AFEEYAH, daddy yayi dariya yace Afeeyar da jabeer zai aura,
Affan ya gyada kanshi yana dariya yace eh daddy ay yace zai bani ita ta dawo nan gidan da zama,
daddy yayi dariya yace to naji tashi kaje ka kwanta kaga ruwa na neman tsugewa,
Affan ya mike yana murna yana fadin daddy zai aura min barbie..
dariya alhj basheer yayi ya mike ya wuce dakinshi dan oyizah tayi tafiya tun da safe..
Affan na shiga ďaki ya haye kan gado yanata wakar abu ďaya, tsawar da akayi mai karfi tayi daidai da faďuwar gabanshi, mikewa yayi daga kan gadon ya leka window yana kallon ruwan da ya tsuge kamar da bakin kwarya,
Affan cikin tsoro ya rike kirjinshi dake tsananin bugu ya fita da gudu yayi dakin daddy,
da kyar daddy ya lallabashi suka kwanta tare amma fa bacci ya kaurace a idonshi dan daga ya runtse idonshi to fuskar jabeer zai gani yana kuka mai tsanani..