← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 48

Sashe 34

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kaka liman yace mugun asiri akayi mata,
karyewar asirin na farko shine jin da jabeer yayi mata har ya sanar da ni,
a aikin da nayi na gano laya ce aka turata cikin bakin DAMO aka binne ta anan cikin gidan da kuke,
Afeeyah ta zaro idonta tace a cikin gidan? yace kwarai kuwa,
sannan duk wasu asiran da tayi a cikin gidan ta binnesu da yawansu bansan takamaimai inda ta binne ba amma suna cikin gidan,
in har Allah ya taimakemu muka san inda suke har muka ciresu to saukin abun yazo dan mun riga mun gama wasu ni da jabeer karashen ne wannan kuma sune masu wahalar,
Afeeyah ta jinjina kanta tace to kaka ya za'ayi musan inda tayi binne binnen,
kaka liman yace shine yanzu abinda nake tunani,
hannu yasa a aljihu ya ciro wata bakar leda, bude ledar yayi ya fito da wasu layu guda biyu da wani ruwan turare sai garin magani,
layun ya fara mika mata yace rike wadannan layun, dafatan zaki jajirce akan duk abinda zaki gani,
Afeeyah tayi kulu kulu da ido tace kaka banyi yarinya da daukar wannan kasadar ba kuwa,
kaka liman yayi dariya yace Afeeyah kenan sai kiga abinda zakiyi ni bazan iya yinshi ba saboda wani lokacin kwakwalwar yaro tafi ta babba kaifin rike abu,
Afeeyah ta gyada kanta tace to Allah ya bani juriyar iyawa yace ameen abinda ya kamata ki fadi kenan,
wadannan layun a karkashin pillown ki zaki sasu,
in zaki kwanta kiyi alwala kiyi sallah kiyi addu'a sosai akan Allah ya bayyana miki guraren da akayi wadannan binne binne, sannan ki shafa wannan turaren a jikinki ki kwanta kina mai kyautata niyya, in shaa Allah cikin kwana bakwai Allah zai nuna gurin da suke,
duk wani abun tsoron da zaki gani na rokeki ki daure kar wannan tsoron ya sare gwiwarki,
ke kadaice garkuwar bayin Allahn nan, in har kika sare to ki sani babu wani wanda zai iya daurewa yayi wannan aikin,
Afeeyah ta gyaďa kanta tace in shaa Allahu kaka zan daure, nasan ina tare da Allah da kuma kai,
yace masha Allah, sannan wannan maganin ki dinga ba Affan yana sha, kafin kwana bakwan nan zai dinga yin wasu abubuwa wadanda zasu dinga dawo dashi cikin hayyacinshi ya dinga tunanin abubuwan mamakin da suka faru dashi a shuďaďdun lokuta, kin gane bayanin ko,
Afeeyah ta gyada kanta tace eh na gane, to amma kaka yaya zanyi in na gansu,
kaka liman ya mike yace wannan kuma shawararki ce,
in kiga zaki iya ciresu ki taimaki uba da kakar abin dake cikinki to in kuma zaki barsu su dawwama a haka nidai na gama nawa yanzu naki kadai ya rage sai mu barma Allah sauran,
Afeeyah tace to kaka nagode sosai, ya miko mata wayarshi yace samin numberki kiyi flashing in wani abu ya shige miki duhu kya nemeni,
Afeeyah ta amsa tasa mishi numbrta sukayi sallama ta bishi da kallo har ya bace ma ganinta
, ganinshi kadai yana kwantar da hankalinta, badan tsufan shi ba da babu abinda zai hana a kirashi da jabeer dinta....

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Karfe 9 na safe aka sallameta suka ďunguma zuwa gida a motar alhj basheer,
oyizah na zaune a parlonta tana gyara farce hankalinta sam ba'a kwance yake ba dan
tun jiya take jiran jin mummunan labari game da Afeeyah amma shuru gashi har gari waye,

Shigowar motar alhj basheer ne yasa ta mike ta kwashe kayan gyaran kumban dan taje ta tarboshi ko zataji wani labari a gurinshi,
tana buďe kofar parlon tayi tozali da mai taurin kashi wato Afeeyah,
kallon mamaki ta tsaya yi mata a zuciyarta tace to ko karya hajja take mata yarinyar nan bata ci abincin ba,
Afeeyah ta katse mata zancen zucin da takeyi tace ina kwana,
oyizah ta sauke ajiyar zuciya tace lafiya lau ta juya ciki bata ko bi takan hajja dake rike da kaya ba,

Side dinsu ta wuce tana kallon hanya ko zata ga Affan,
da bismillah ta murďa kofar dakin suka shiga ita da hajja,
bayi ta wuce ta cire kayan jikinta tayi wanka ta dauro alwalar walha, ta windon bayin ta hangoshi
zaune gurin fishpond idonshi kyar a cikin ruwan baya ko kiftawa, murmushi tayi ta fito daga bayin,

sai da tayi sallah ta shirya cikin bakar jallabiya sannan ta fita gurinshi,

A hankali ta karasa gurin tayi saurin rufe mishi ido da hannunta, shafa hannun yayi cikin firgici yasa ihu yana ďaga kafarshi dan kar ya faďa cikin ramin kifin,
da sauri ta toshe mishi baki tana dariya tace nice matsoraci, juyowa yayi ya kalleta nan take ya saki dariyar farin ciki ya rungumeta yace ina kika tafi ki barni,
ta dago fuskarshi tace ina daddy yace maka ya kaini,
ya shagwabe fuska yace mummy tace min bazan kara ganin ki ba, jiya suka dinga min ihu anty salma har da duka na,
Afeeyah tace am sorry gani na dawo daga yanzu babu wanda zai kara maka kallon banza ma bare har ya dukeka tashi muje kaci abinci,
ya mike da sauri yana dariya suka wuce daki...

Da sauri oyizah ta bar gurin dan kar Afeeyah ta ganta,
wani irin bakin ciki ne yake taso mata a cikin zuciyarta,
shin me zata ma wannan yarinyar ta daina ganinta kwata2 a rayuwarta,
a cikin yan kwanakin nan ganin yarinyar nan shine abinda yafi komai bakanta ranta, aiki biyu kenan tayi akanta kuma duk masu karfi amma basu kama ta ba,
tabbas wannan gara inyi mata me kankat, tabbas yau ne numfashinta na karshe a duniya dan barin Afeeyah a duniya barazana ce a gareta dan yarinyar na neman fin karfinta,
a tarihin rayuwar oyizah tun tana karama babu abinda ke tsaya mata a gaba bata kau dashi ba dan haka wannan karan Afeeyah bata isa ta rusa sa'arta ba,
da wadannan tunanin ta karasa ďaki ta zauna neman mafita, wani sashi na zuciyarta ya bata amsar cewar ta bada Afeeyah kawai su "chummy" suyi bandaro da jinin tsinaniyya, in ba hakan tayi ba to kuwa tana zaune kwado zai mata kafa,,
dariya tayi cikin gamsuwar shawarar da zuciyarta ta bata, nan ta mike ta fara shirye2 kafin dare yayi ta sadaukar da jinin ďiyar ma'u da malam Atiku,

To oyizah muje zuwa muga zaki iya da Afeeyah...

Cikin jindadi suka kammala cin abincinsu na dare wanda hajja ta aiko musu,
bayan sun gama ta jiko maganin da kaka ya bata ta bashi yasha dakyar yana sha yana furzarwa,
saida ta nuna mishi bacin ranta sannan ya sha da yawa,
yana gama sha ta gyare gurin ta dawo ta zauna suka fara yar hira,
murďa kofar suka ji anyi suka waiga suna kallonta,
da fara'a ta karaso gurinsu tace amarya da ango, sannunku da hutawa,
Afeeyah ta kau da kanta tace yauwa, oyizah ta zauna gefensu tace Afeeyah ya kamata ki ďan leka gida ki gaishesu dan gani nayi tunda kikazo gidan nan baki shiga ba, daga nan sai ki dan zaga da Affan yaga gari ko ya kikace,
Afeeyah tace hakane mummy amma ay naga affan baya fita ko,
oyizah tace shiyasa nake so ki ďan fara fitar dashi yayi refreshing,
Afeeyah tace to duk yadda kika ce, ta mike ta dauko hijab dinta tace tashi muje,
ya tashi yana kallon oyizah alamun yana so ya tambayeta yaje ko a'a,
gyaďa mishi kai tayi alamar yaje, dariya yayi ya bi bayan Afeeyah suka fita,
dariyar jin dadi oyizah tayi ta rakasu har gate sannan ta juyo da sauri tayi dakinta ta kwaso kayan tsafinta ta nufi side din su Afeeyah,

Tafiya takeyi da sauri saboda manta Turaren da tasa a ranta duk ranar da xata gida zata kaima mahifinta,
tun a parlor ta gane akwai mutum a bed room dinta,
labewa tayi ta leka a hankali,
ba karamin firgici ta shiga ba ganin oyizah tsaye a gefen gadonsu tana shimfiďa farin kyalle a kasan katifarsu,
da sauri ta fita daga dakin lokacin da taga ta dauko zanin gadon su ta mayar ta shimfidashi yadda yake,
a guje ta fita ta samu affan a inda ta barshi murya na rawa tace muje,
ya kalleta yace ina turaren, dakyar ta saita kanta tace muje dai gobe zan kai mishi..

Sai goma saura suka dawo gida,
babu wanda Afeeyah ta faďa ma abin da tagani dan ta riga ta gama kudira abinda zatayi tana komawa gida,
suna shiga ta zaunar da Affan a parlor ta kunna mishi tv tace kar ya tashi bari ta gyara cikin dakin,
tana shiga daki ta yaye zanin gadon da bismillah ta ciro farin kyallen ta naďe zanin gadon ta ajiyeshi gefe sannan ta fito ta kalli affan tace ina zuwa bari in mayar ma da mummy zaninta,
yace to ya cigaba da kallon cartoon dinshi,
tana fita tayi hanyar ďakin mummyn cikin sanďa dan tasan yanzu tana gurin daddy,
a hankali ta murďa kofar ďakin ta shiga da addua a bakinta,
da sauri ta yaye zanin gadon tasa farin kyallen kamar yadda taga oyizah tayi sannan ta maida zanin gadon ta shimfidashi yadda yake tasa kai ta fita daga ďakin da sauri.....

Mrs Tijjani shattima
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Tana komawa daki ta tarar da Affan na gyangyaďi a kan kujera,
da sauri ta shiga ďaki ta canza zanin gado ta tofe ko'ina da addu'a ta sa layun karkashin pillownta sannan ta shiga bayi ta ďauro alwala ta fito ta wuce parlor ta tarar har ya bingire a gurin yana bacci,
tashin shi tayi a hankali ta kaishi ďaki ta tofeshi da addu'a ta rufeshi da bargo sannan ta shimfiďa dadduma tayi raka'a biyu,
a gurin ta zaune har pss 2 tana addu'a tana tunanin abinda oyizah tasa mata a karkashin gurin kwanciyarta,
a zuciyarta tace koma meye ya kare miki can Allah ya kara tsaremu daga sharrinki,
mikewa tayi tana hamma ta hau gado ta kara shafa addu'a sannan ta kwanta tana kara rokon Allah ya nuna mata guraren da akayi binne binnen nan dan alfarmar annabi da hasken al qur'ani....
Chapter 34 · 0% Book details