← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 48

Sashe 44

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kwance take kan kirjinshi ta cukwikwiyeshi tana kuka mai ban tausayi tana faďin
"meyasa ka tafi ka barni na tsawon lokaci, meyasa baka daukeni mun tafi tare ba ka barni cikin wannan wahalalliyar duniyar mai cike da azzalumai marasa tsoron Allah,
ta tsunguna a kasa kukanta ya tsananta tace dan Allah yaya jabeer karka sake tafiya ka barni,
ba karamin wahala nake sha ba saboda rashinka,
I grew up in your arms plss led me die in it, plsssss,
ďagota yayi suna kallon cikin idon juna taga wani haske mai matukar kyau a cikin kwayar idonshi,
a hankali taji yana faďin tafiyata bazata taba zama wahala agareki ba,
naso kasancewa tare dake amma Allahn da ya hallicemu bai halicceki dan ni ba shiyasa ya ďaukeni domin ki kusanta da wanda yake makusanci na hakika a gareki,
dama ni ba mazauni bane zuwa nayi in nuna kamannina in koma ga ubangijin talikai,
tabbas nasan lokacin da nake da rai baki da wata matsalar rayuwa, yanzu kuwa nasan ko baki gama sanin meye rayuwa ba kinsan kadan daga ciki,
mu'imuni ako da yaushe Allah na jarabtarshi ta kowane bangare, duk wanda ya kansance cikin farin ciki a kullum to tabbas ya binciki kanshi domin duniya kurkukun mu'imuni ce sannan aljannar kafiri,
kafiri marar tsoron Allah, ko wanda ke sabawa Allah shi kaďai ne ke samun farin ciki marar yankewa a duniya,
akwai lokacin da zamu shiga farin ciki amma cikin lokaci kalilan sai bakin ciki ya maye gurbin wannan farin cikin,
to ki sani duk musulmin dake yawan shiga cikin jarabawar Allah lallai ba karamar soyayya bace tsakanin wannan bawan da Allahn shi, domin shiga kunci ga musulmi kankarar zunubi ne,
wasu kuma zaki ga basu da wata damuwa komin zunuban da sukeyi ba shi zai hana Allah ya barsu cikin farin ciki ba, sannan kome suka nema suna samunshi kamar su suka tsara rayuwarsu, to wadannan Allah ya barsu da kansu ne har sai sun tuba,
kullum mu'imunin kwarai yana cikin jarabawar ubangiji masu tsananin rabo su ke cinye jarabawar dari bisa ďari,
ya share mata hawayen idonta yace zanso Afeeyata ta zama daga cikin masu cinye jarabawar ubangiji a koda yaushe,
zanso ki daina yawan zubar min da hawaye domin hawayen basu kara komai sai wahalarwa ga kyakyawan idanuwanki,
zanso ki manta batun soyayyata a matsayin wanda zai aureki ki sanya soyayyar yaya a zuciyarki domin samun tsaftattaciyar addu'a daga gareki,
ki kular min da Affan kamar yadda zaki kula dani domin ni da shi bamu da wata maraba kuma nasan zai kula dake kuma ya kaunace fiye da yadda ni nayi, ki yawaita istigfari domin istigfari yana kusanta bawa da ubangijinshi kuma mai yawan yinshi zai kasance kullum cikin nutsuwa da walwala,

cikin sheshshekar kuka Afeeyah ta buďe baki zatayi magana jabeer ya sa hannu ya rufe bakin yace karki ce min komai ga Affan can yana jiranki zaku tafi gida, nagode sosai da ziyara,
cikin kuka ta cire hannunshi a bakinta tace dan Allah yaya jabeer ka tsaya kaji abinda zan faďa maka,
girgiza kanshi yayi yana mata murmushi hasken hakoranshi suka rufe idonta ta durkushe a gurin tana kallonshi cikin hasken tana kuka sosai tana kiran sunanshi,
wata sassanyar iska ta shiga kaďawa a gurin har hasken jabeer ya bace ma ganinta,
runtse idonta tayi tana kuka sosai tana faďin dan Allah karka tafi ka barni,

Hannu taji cikin nata ana murzawa a hankali sannan taji saukar ruwa a kan hannun,
a hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai ta saukesu kan Affan dake zaune kusa da ita kanshi a kan hannunta yana zubar da hawaye,
lumshe idonta tayi hawaye na zuba ta gefensu ta fara tuno mafarkin da tayi akan jabeer,
meyasa ya tafi bai tsaya yaji abinda zance mishi ba, meyasa be bari nasan abinda zan faďa mishi ba,
shikenan bazan kara ganinshi ba har in koma ga Allah,
to ni yaushe zan mutu, wayyo Ya Allah ka dauk---- Affan yayi saurin toshe mata baki da hannunshi yasa hannu yana share mata hawayen dake gangarowa daga cikin idonta,
buďe idonta tayi ta kalleshi tasa hannu ta ďan ture hannunshi cikin muryar kuka tace kukan me kakeyi,
da mamakinta sai taji ya kwanto jikinta yace kukan abin da kikeyi,
a hankali tace ai bakasan kukan da nakeyi ba,
ya ďago jajayen idanuwanshi yace nasan har duniya ta naďe bazaki taba yin kukan komai ba in ba na rashin jabeer ba,
cikin mamaki ta kureshi da ido hawaye ya kara zirarowa a cikinsu cikin rawar murya tace kasa--- ya fashe da kuka yace nasani Afeeyah, nasani,
nasan jabeer ya tafi ya barni,
nasan bazan sake ganin fuskarshi mai dauke da murmushi a kullum ba,,
nasan bazamu sake haďuwa mu rungume juna mu faďa ma juna damuwarmu ba,
bansan me yasa mutuwa ta zabi jabeer ta barni, bansani ba Afeeyah,
ya karasa fadi yana kuka kamar karamin yaro,,
kuka suka dinga yi babu mai rarrashin wani a cikinsu,
saida sukayi mai isarsu sannan Affan ya ďago ya kalleta murya a dashe yace nagode, nagode da abin da kikayi min,
kau da kanta tayi tace ka gode ma Allah da kaka liman,
ya juyo da fuskarta yana kallon rinannun idanuwanta yace kullum cikin gode musu nake,
godiyarki ta daban ce Afeeyah, babu wanda zai dauki kasadar da kika ďauka a duniyar mu ta yanzu,
kinyi mana abin da ko dan uwa na jini bazai iya yi mana shi ba, bamu da wata kalmar da zamuyi amfani da ita gurin gode miki, Afeeyah tace karka gode min na cika kudirin jabeer ne, wannan shine burinshi na karshe, saboda wannan kudirin aka kashe min shi,,,
Affan yace nasan komai Afeeyah kuma in shaa Allahu wacce ta kasheshi ba anan duniya ba ma har a lahirah bazata taba samun kwanciyar hankali ba,
Afeeyah tace tun a duniya nakeson Allah ya wulakanta min ita, wallhi da nasan ita ce silar mutuwarshi na rantse da bazan kyaleta ba da nayi mata abun da zata gwammaci mutuwa da rayuwa,

Affan ya share mata hawaye yace ki kwantar da hankalinki nasan yanzu duk inda take a cikin bala'i take,
Afeeyah ta girgiza kanta tace da hannuna nakeson in kasheta kuma yau dinnan,
Affan yace hmm nima naso hakan tun ranar da na dawo cikin hayyacina,
nan ya bata labarin komai harda dawowar umma da bacewar oyizah,,,,,
cikin mamaki Afeeyah tace zatayi abinda yafi haka muguwa azzaluma, Allah ya isa tsakanina da ita,
in shaa Allahu sai tayi mutuwar kask---Affan ya katseta da sauri yace wannan adduar bata kamace ki ba, Allah yasan yadda zai tafiyar da irinsu ki zuba ido ki jira lokaci,
Afeeyah tayi shuru tana kallonshi kamar ba shi bane tababben bawan da baya taba maganar da zaka iya fahimta a da,
Allah mai iko......

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Chapter 44 · 0% Book details