Sashe 12
Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da bisimillah ta shiga gidan dan Allah yasan ta tsani ganin su fareeda dan basa ga maciji ko kadan,
parlon ta wuce ta dinga sallama taji shuru ta wuce ciki ta murďa kofar dakin umma haďe da sallama, tana sa kai ciki sukayi karo sosai da Affan wayarshi ta faďi kasa,
baya taja da sauri rike da kanta tace washhh Allah kaina,
kai baka san mutum zai shigo bane,
ya tsuguna ya ďauki wayarshi yace saboda idon mudubi gareni da ke hasko min abinda ke waje ko,
ta turo baki tabi ta gefenshi zata wuce ya tare kofar yana kallon cikin idonta yace baki iya bada hakuri ba ko, ta sakar mishi harara tace kai zan tambaya wannan tunda ni ka bige ma kai kuma har yanzu zafi yakemin,
yayi murmushi yace lallai yarinya zaki kwana anan dan bazaki taba wucewa ba sai kin bani hakuri, tayi dan guntun tsaki ta juya ya maza ya janyo hannunta ya matseta sosai numfashinsu na gaurayuwa,
runtse idonta tayi tace ka sakeni in tafi, bin ko'ina na fuskarta yakeyi da kallo yace ina zaki,
a tsiwace tace ina ruwanka dalla ni ka sakeni ko inyi maka ihu,
yayi dariya yace bakinki a bude yake ay go ahead, ya ďauka wasa takeyi yaji ta saki ihu da karfi,
da sauri ya saketa ya koma baya a zuciyar shi yace wannan wace irin yarinyace,
da gudu zeenatu ta fito tana waige tace Afeeya me ya sameki, ta ruga bayanta tace wancan ne ya bige min kaina kuma wai sai na bashi hakuri,
zeenatu ta kalleshi tace zanci maka Affan ba gurin jabeer kace zaka ba,
yace wallhy umma karya takeyi sai yanzu ma na gane afeeyah ce, ya harareta yace jarababbiya kawai, yasa kai ya fita yana mamakin irin girman da afeeya tayi,
gurin aikin jabeer ya wuce dan ya kosa ya ganshi rabon da su ga juna tun da ya tafi egypt dan ummanshi ta hanashi dawowa hutu saboda lafiyarshi dan ita kanta a ďarare take a gidan saboda yadda oyiza ke hurda da wasu mutane a cikin gidan da kuma yawan mafarke mafarken da takeyi akan oyizar da ďanta, ga alhj basheer ma sai yadda tayi dashi,
Sunyi matukar farin cikin ganin junansu dan jabeer ma gurin aikin ya bari suka fita yawo sunata hirar yaushe gamo,
sai gurin karfe 5 na yamma suka dawo gida,
gidansu afeeya jabeer ya sauka dan tun safe bai ganta ba kuma yasan tana can ta damu......
Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah
A daren ranar da Affan ya dawo suna zaune a parlon dukkansu har su salma da suka ri'ka a gida ba aure,
zeenatu dai na ďakinta dan ko tazo ta zauna cikinsu to fa takaici zai sa ta tashi ta koma daki saboda alhj basheer ko kallonta bayayi,
hira sukeyi shi da Affan saboda farin cikin ganinshi, duk irin hararar da oyiza take mishi baisa ya daina hira da ďanshi da yakejin kamar shine ma ranshi gaba daya, mikewa yayi yace ina zuwa affan je ka ce ma ummanka tazo,
Affan ya tashi yaje ya kira zeenatu, dakyar ta yarda tazo dan bata san dalilin kiran ba, wasu takardu ya fito dasu masu yawa yana mikama affan daya baya,
yana gama mika mishi yace kasan takardun menene wannan,
Affan ya girgiza kanshi, alhj basheer yayi dariya ya kalli zeenatu da oyiza yace ku zama shaida na malakkawa Affan company na na lagos dana nan kano,
sai kuma estate dina na Abuja da gidana dake nan Nasarawa, wannan kyautar da nayi wa Affan ba wai dan yafi sauran ya'ya na bane, a'a sai dai dan shine namiji kuma nasan ko bayan raina zuri'ata bazata taba shiga cikin kunci ba in dai Allah ya tayashi riko da duba dukiyar, ya kalli salma da farida yace ku mata ne, kuma aure zakuyi, dan haka duk wata kyauta da zan muku bazata yi wani tasiri a gurinku ba saboda karkashin wani zaku tafi,
wata rana Affan shi zai zama uba a gareku,,
wayyo zan so ku hango min oyiza a wannan lokcin,
kiriss ya rage zuciyar ta buga saboda alhj basheer ya kyautar da duk wata muhimmiyar kadararshi ga affan, shuru kawai tayi jikinta na fitar da zufa, a zuciyarta tace hmmm maiyi baya faďa wannan karan ka kaini bango alhj,
mikewa tayi tace ma su salma ku tashi mu tafi, suka mike suka wuce fuuu cikin bacin rai,
zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tace dan Allah ka rufa mana asiri, wallhy Allah kadai yasan abinda kyautar nan zata haifar,
yace ta haifar da komai zeenatu, Affan ďana ne ko bayan raina shi ne magaji na, dan haka ki bishi da adduoin neman tsari kawai,
tace to Allah ya tsaremu da tsarewarshi, ameen yace sannan suka cigaba da hira yace ma affan ya tashi yaje ya adana takardun, Affan ya mike yana jujjya takardun ya wuce ďaki ya bar iyayenshi na hirar da suka daďe basuyi ba...
Tun safe jabeer ya fita da Afeeyah da Ameerah yawo, duk guraren shakatawa da wasannin dake cikin garin kano saida suka je, a shop rite suka tsaya yayi musu siyayya suka fito a gajiye zasu shiga mota,
wata kyakyawar farar yarinya suka hango ta tunkaro su tana dariya,, rufe mota jabeer yayi yana dariya ya karasa kusa da ita yace "Nadiya Lameeďo" idonki kenan, tayi dariya tace kai zan ma wannan tambayar Jabeer, ya kake?, yace am cool walhy, ya skull ko aiki, tace duka, bani cntct dinka zamuyi magana a waya dan naga sauri kakeyi,, ya ciro card dinshi ya bata itama ta bashi nata sukayi sallama ta wuce,
mota ya shiga ya kalli Amirah dake gaba ya waiga ya kalli Afeeyah da ta cika tayi famm yace juyin mulki akayi kenan,
ke Amirah koma gurinki itama ta dawo gurinta,
Amirah ta buďe kofar zata fita Afeeya tace saidai fa mu zauna tare a baya, amirah tace kaji ko yaya, wallhy tun ďazu nake ce mata ta dawo nan taki,
kallonta yayi ta mudubi yayi dariya yace amirah shigo muje,
suna isa kofar gida ta buďe motar ta shige ba tare da tabi takan kayan da ya siyo musu ba,
Amirah ta kwashi nata kayan ta shige gida itama, jabeer ya gyara parking ya kwaso kayan ya fito dasu ya shiga gidansu,
kwance ya sameta can karshen gadon hajja tayi ruf da ciki hajja na mata magana tayi banza da ita,
jabeer ya zauna bakin gadon ya gaida hajja ta amsa tace yau kuma me kayi ma mutuniyar taka,
jabeer yayi dariya yace wallhy babu abinda nayi mata rigima ce kawai, Afeeya ta ďago idonta a kankance tace har kana wallhy,
ya kalleta yace to me akayi,
tace nima bansani ba, ta mayar da kanta kan katifar ita kanta bata san me zata ce ya mata ba ita dai tasan taji masifaffan zafin ganinshi da tayi da wata,
juyin duniya yayi ta faďa mishi abinda yayi mata amma sam taki ďago kai ma bare ta bashi amsa,
hajja taja tsaki tace tashi ka tafi ka rabu da ja'ira da kanta zata nemeka, in ba iskanci ba babu abin da aka ma mutum ya hau fushi, to in kin ga dama ki fashe,,
jabeer zaiyi magana ya ji wayarshi na ringing, ya mike da sauri yace hajja dan Allah ki rarrasheta kafin na dawo tun dazu Affan ke jira na, hajja tayi tsaki tace ni ban iya wacce ka iya ba, ya fita yana dariya. ..
Sai bayan isha suka rabu Affan ya wuce gida,
ya na sa kafarshi cikin gidansu yaji muguwar faduwar gaba,
wucewa ciki yayi a hankali jikinshi a mace ya shiga dakin mahaifiyarshi,
zama yayi ya dafe kanshi yana jiranta dan a tunaninshi tana bayi ne,,
wani irin ihu yaji mai firgitarwa ya mike da sauri yana kasa kunne yaji daga inda ihun ya fito,
kafa kunnenshi yayi a jikin toilet yaji ba alamar mutum a ciki, umma... umma.. ya kira sunanta sau biyu yaji shuru ya tura bayin,
juyawa yayi da sauri da yaga bata yana kwala kiranta,
muryoyin mutane ya dinga ji a can saman gidansu gurin shan iska,
a hankali ya karasa gurin yana leke a tsorace saboda muryoyin da yaji harda ta maza a ciki,
wani razanannan ihu ya saki haďe da faduwa kasa sumamme sakamakon abinda idanuwanshi suka gani.....
Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah