← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 48

Sashe 17

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk irin tururuwar da mutanen unguwa keyi a kofar gidan zuwa gaida affan basu samu shiga ba dan ko kofar masu gadi basu buďe musu,
hakan yasa mutane suka hakura da zuwa gaisheshi saidai in sun hadu da alhj basheer suyi mishi jaje a waje, maganar zeenatu kuwa banda yan'uwanta da su Abida babu wanda ke tunawa da ita addu'a kuwa kullum yinta sukeyi akan Allah ya bayyana ko gawarta ne..
Oyizah kuwa likkafa taci gaba don ba kananan kudi takeci da ciwon affan a guri alhj ba ,
duk bayan sati daya da kudin da yake bata da sunan ana ma Affan saukar alqur'ani da rubutu, amma bai taba maida hankali gurin ganin affan yasha rubutun a gabanshi ba saboda ya yarda da oyizah 100%,
haka in malam Atiku ya bashi rubutu a bawa affan ko jabeer ya amso mishi sai dai daddy ya bata yace ta bashi yana fita zata zubar dasu tayi ta musu tofin Allah tsine...
Abinda yafi ďaga mata hankali yanzu shine ta rasa inda Affan ya ajiye takardun kadarorin da alhj ya bashi,
kullum zata zaunar dashi a siyasance tace ya dauko mata takardun da alhj ya bashi, cikin rashin fahimtar abinda take nufi zai tashi yaje ya tattaro duk takardun dakinshi ya kawo mata,
babu irin duban da batayi ma dakinshi da na zeenatu ba amma sam bata gansu ba,, gashi tana tsoron tambayar alhj basheer dan kar ya harbo jirginta, haka ta saduda da tunanin in alhj ya mutu dukiyar duk nata ne da ya'yanta dan ko Affan ma mallakinta ne....

Wannan shine mafarin ciwon Affan da yanzu yake cikin shekara ta uku cikinshi, a wannan shekarun ko sau ďaya affan bai taba fita da kafafuwanshi ba sai dai a kaishi checkup a mota tare da oyizah amma fita shi kadai sam bata yarda dashi ba dan ba karamin kafi tayi mishi ba,
Salma da farida kuwa maidashi sukayi kamar toy haka zasu tasashi a gaba suyita dariya in yana shirmenshi...

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣6⃣ By Aysha Ya'u Kurah

☆ cigaban labari ☆

Gida jabeer ya tafi bayan sun gama hira da hajja da Afee akan lalurar Affan, yana shiga ya wuce parlon mahaifinshi, zaune ya samesu da ummi ya gaisar da babanshi ya amsa fuskarshi dauke da fara'a yace ya jikin abokin naka, jabeer yace alhmdullih baba, Abida ta kalleshi tace ina Afeeyar take shine ta tafi babu ko sallama, jabeer yace ai ummi taga kina bacci ne shine muka shiga gurin affan tare,
Alhj bara'u ya kalleshi sosai yace jabeer yaushe Afeeya zata fara jarabawa,
Jabeer yace next uppr week zasu fara, alhj Bara'u yace hasashena ya zama gaskiya kenan, mun zauna da malam atiku mun tattauna game da maganar aurenku ni in sona ne ma ayi kafin ta zana jarabawar, Abida tace haba alhj ay gaggawa ba namu bane ina laifin in sun gama da sati ďaya, alhj bara'u yace to koma yaushe ne Allah ya kaimu dan na kosa in aurar da jabeer, Abida tace kace dai ka kosa kaga yan jikokinka,
alhj bara'u ya kwashe da dariya yace ma jabeer ya tashi ya tafi, jabeer ya fita shima yana dariya..

Cikin ikon Allah aka tsayar da ranar Afeeyah da jabeer kamar yadda Abida tace,
murna a gurinsu ba'a cewa komai babu wanda zai iya gane wanda yafi murna a cikinsu,
shiri jabeer yakeyi sosai da planning din yadda zasuyi rayuwarsu da Sweet Afee dinshi da ya'yan da zasu haifa tare, duk shirin da yakeyi bai hanashi zuwa gurin Affan ba kullum suna tare da yamma kuma kullum sai Affan ya tambayeshi ina barbie dinshi,
jabeer shirme yake maida abin saboda yasan bayi da isashen hankali, da jabeer yaga abin na Affan bana karewa bane sai yake zuwa ya dauko Afee dakyar suzo gurin Affan, in Affan ya ganta to fa aranar murnarshi ta karu kenan saboda ya dinga mata shirme kenan yana kwaso kayayyaki yana bata wai ta tafi dasu gida,
a cikin yan kwanakin suka dan fara sabawa kadan2, dakyar jabeer ya fahimtar dashi cewa an kusa daura mishi aure da Afeeya, dariya kawai yayi yace to in kukayi aure zaka barmin ita anan gidan, jabeer yace sosai ma ai anan zata zauna, Affan yayi dariya ya kalli afeeyah yace wai haka, ta gyaďa mishi kai tace eh,
wani irin ihu yasa ya mike wai zaije ya fadama mummy,
da sauri Afeeyah ta riko hannunshi ya tsaya chakk yana jin wani irin abu a rikon da tayi mishi,
juyowa yayi kamar me hankali ya kalleta itama shi take kallo haka jabeer kallonsu kawai yakeyi,
jikinta ne ya bata jabeer na kallonta tayi saurin sakin hannun Affan tace karka faďa ma mummy zatace kar abaka ni ko yaya jabeer,
jabeer ya gyada kanshi yana kallon Affan, zama Affan yayi yana murza hannun da Afeeyah ta rike yace to babu abinda zatamin in ta sani,
Afeeya ta gyada mishi kai tace baza ma tasani ba,
jabeer yayi mamakin yadda affan yaji maganar afeeya, mutumin da magana in dai akan mummy ne to babu wanda ya isa ya tsayar dashi, kallonsu ya cigaba dayi yadda yake mata hira tana biye mishi suna kyakyata dariya sai yaji daďi a ranshi dan ko ba komai zai yi amfani da Afeeyah ta dinga dawo dashi hanya,
sam baiji kishin komai a ranshi ba dan yasan Affan baida hankali kuma ko yanada hankali ma bazaiyi kishi ba saboda yasan irin son da afeeyah take mishi..

Safiyyar monday jabeer ya shirya da wuri saboda zai kai Afeeyah makaranta ranar zasu fara jarabawa,
a kofar gidansu ya sameta tsaye tayi kyau sosai tana jiranshi, kusa da ita ya kai motar ta bude ta shiga suka gaisa,
yace da fatan kinyi karatu ko, tace sosai ma banyi bacci sosai ba,
yace kedai fadi gaskiya kodai kin boyo xpo, ta turo baki tace kaima kasan wuce nan duk da bana zuwa 1st kasan dai ban taba wuce 10th ba,
yayi dariya yace 3rd term ss2 dakyar na roka fa aka barki a 10th din shine zaki wani cika min baki a faďa da dambe ne dai ake baki A1,
ta harareshi tace eh naji ďin, yayi dariya ya tada motar suka wuce yana cigaba da tsokarta, kan titin "hausawa" ya hango motar gidansu Affan, bai bi takanta ba bare yasan su waye a ciki, ya wuce ya sauke Afeeyah a skool haďe da yi mata adduoin samun nasara..

Yana fitowa daga layin skull dinsu ya kuma hango motar, wannan karan Affan ya hango a gaba da baloon a hannunshi yana dariya mummy ta hakimce a baya,
bin motar yayi dan yanason yaga Affan kafin ya tafi aiki, asibitin da ake mishi check up suka tsaya, saida suka shiga ciki Jabeer yayi parking, saida ya gaisa da wani abokinshi da suka dade basu haďu ba sannan ya shiga,
sam oyizah bata ganeshi ba saboda hankalinta a tashe yake da result din check up din,
jabeer yaji doctor na cewa gaskiya an gode Allah dan zai iya dawowa normal cikin kwanakin nan saboda mun samu improvement sosai, ya mika mata magani yace wannan maganin shine maganinshi na karshe in shaa Allah in ya kare komai zai zama normal,
jabeer saboda murna zaiyi magana ya bugi wata nurse kayanta suka zube ya durkusa ya kwashe mata yana bata hakuri,
yana ďagowa yaga har sun fita sun shiga mota,
binsu yayi a baya har gida,
a waje yayi parking motarshi saida ya tsaya a waje ya kirah office ya dau excuse sannan ya shiga ciki da sauri,
babu kowa a parlon gidan hakan yasashi hawa sama saboda tsananin murna, tsayawa yayi jikin wata kofar da yakejin magana da karfi haďe da huci kamar zakanya,
lekawa ya fara yi ta gurin mukulli, ya hango Affan zaune kan wani jan kyalle,
da sauri ya dago kanshi jikinshi na rawa ya ďeka ta window, oyizah ya hango da wata halitta suna magana suna zagaye Affan,
suna gamawa yaga an bawa oyiza wani ruwa ance ta bawa affan muddin yasha to bashi ba samun sauki kuma haukarshi zata fi ta da,
oyizah tayi dariyar jindadi tayi sujjada ga wannan halittar nan da nan yaga ta bace,, jabeer sai mutsike idonshi yakeyi a tsorace kamar a mafarki,
muryar oyizah ce ta dawo dashi hayyacinshi waya takeyi da esther tana faďa mata duk yadda tayi ta mayar da Affan haka har abin da tayi ma zeenatu,
a kidime jabeer ya fara fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
jin tayi shuru ne yasa ya leka da sauri ya hangota ta mike zata bawa Affan wannan ruwan,
cikin zafin nama ya murda kofar ya kabe ruwan ya zube a kasa, oyizah ta kalleshi a firgice tace j-a-b-e-e-r, ya dago Affan ya rikeshi yana mata wani mugun kallo yace asirinki ya tonu, muguwa azzaluma, matsafiya mai shan jinin alumma,
naga duk abinda kikeyi yau in shaa Allahu karshenki yazo, yaja hannun Affan zasu fita oyiza tace jabeer ka dawo, ka rufa ma kanka asiri dan wallhy babu wanda ya isa yaga karshena,
ka dawo ka fadi nawa zan biyaka ka rufa min asiri,
jabeer bai saurareta ba ya fita dan a tsorace sosai yake,
suna zuwa gate Affan ya fisge hannunshi yasa ihu yana faďin mummy kizo ga su lion nan zasu kamani, ihu yakeyi yana ja baya ya ruga ciki da gudu,
jabeer ya kalli gate din cikin mamaki dan shi baiga komai ba,
har zai koma ciki sai kuma ya fasa ya fita a fusace,
Police station ya nufa yana zuwa kofar gurin ya fara tunanin to ina evidence yake,
Affan shi kadai ne evidence kuma bashi da hankalin da za"a saurareshi,
shuru ya zauna a motar yana tunanin mafita, can ya fara tunanin yadda zaiyi affan ya samu sauki, a zuciyarshi yace malamai zan tara suyi ta mishi addu'a ita kuma oyizah zan mata lamfa in nuna mata kamar bazan fadama kowa ba har sai nasan yadda nayi har Allah ya bawa Affan lafiya,...

Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Chapter 17 · 0% Book details