← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 48

Sashe 25

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar da za'ayi sadakar bakwan jabeer kuka sosai Affan ya tsare mahaifinshi dashi akan shi gobe in ba'a kawo mishi Afeeyah gidan nan ba bazai kara cin abinci ba, hankalin alhj basheer ya tashi matuka saboda yadda Affan ke kuka harda majina,
dakyar ya lallabashi yace gobe in shaa Allahu zan dawo maka da ita gidannan kaji, Affan ya share hawayenshi ya rungumeshi cikin jin dadi yace bari inje in faďa ma mummy sai tayi mata abinci mai dadi ko,
alhj basheer ya gyaďa kanshi,
Affan ya tashi ya fita yana ihun murna, binshi alhj basheer yayi da kallo a zuciyarshi yana tunanin yadda zai tinkari alhj bara'u da mahaifin Afeeyah da maganar auran mahaukacin danshi dan in ba aure ba babu abinda zai kawo Afeeyah gidanshi ta zauna,
dakinshi ya wuce yana jiyo ihun Affan a waje yana yi yana tsallen murna....

Da wuri aka idar addu'ar bakwai akayi sadaka sosai mutane suka watse,
alhj basheer zaune a parlon alhj bara'u suna yar hirah jefi2,
alhj Bara'u ya kalli alhj Basheer yace alhj tun a gurin addu'a na lura da yanayinka kamar wani abu na damunka, alhj basheer yayi ajiyar zuciya yace wallhy alamarin yaron nan ne ke matukar bani tsoro, alhj Bara'u cikin damuwa yace alhj Basheer kenan ay cuta kaffara ce,
ka dinga godewa Allah da lalurar da ya ďaura mishi dan shi kadai yasan sirrin dake cikinta, gara kai ma zaka kalleshi a haka kaji dadi,
yayi murmushi mai ciwo yace Allah ya kai rahama kabarin jabeer, alhj basheer yace "ameen" amma ni ba ciwon Affan bane ya dameni,
wani abu yake so inyi wanda a ganina son zuciya ne in har na yarda na biye mishi,
alhj bara'u yace menene shi alhj,
nan alhj basheer ya faďa mishi duk abinda Affan ke faďa mishi game da mafarkinshi, alhj bara'u yayi ajiyar zuciya zaiyi magana kaka liman ya shigo da sallama,
da sauri suka mike suna mishi sannu da zuwa dan ya koma Daura tun ranar uku, zama yayi a gajiye yana amsa musu, bayan sun gaisa Amirah ta kawo mishi abin kari ya zauna kamar ba gidan ďanshi ba dan baida wannan kauyancin akanshi yaci abincinshi son ranshi yana ci suna hirah,
alhj basheer ya kalli alhj bara'u yace bari in tafi anjima ma karasa maganar,
kaka liman yayi maza cikin wasa yace zauna tare za"a karasa maganar dani in dai ba ta gulma bace,
suka kwashe da dariya suka ce bata gulma bace kaka, yace to a cigaba mana, daga ganina sai ku bari,
alhj bara'u yace to Baba bari mu cigaba kaima sai ka bada shawararka,
yayi murmushi yace to inaji,
alhj bara'u ya fada mishi komai kamar yadda alhj basheer ya fada mishi,
kaka liman yayi murmurshin jin daďi a zuciyarshi yace ikon Allah kenan jiyan nan nake tunanin yadda zanyi a karasa burin jabeer sai gashi cikin sauki wacce yakeso ita zata karasa aikin da ya dauko na amininshi, tabbas akwai wani boyeyyen alamari a cikin wannan auren in har ya ďauru,
ya kalli alhj basheer yace to meye abin son zuciya anan, aure fa kace bawai wani abu ba, kuma ay Affan a wannan lokacin yana bukatar mata saboda haukarshi ba wata hauka bace kawai dai yana abubuwan kananan yara ne, yanzu in har Allah ya tabbatar da auren nan kai da kanka zaka sha mamaki saboda yanzu ne zai samu wacce zai zauna da ita dare da rana kuma nutsuwa sosai zata shigeshi har ta iya kaishi ga samun sauki in Allah ya so, dan komai sai ya so ko ba haka ba,? suka ce haka ne kaka, yace to ku barmin komai yanzu zanje in samu malam atikun in faďa mishi in so samune ma ayi auren yau tunda me zamu jira, nayi imanin hankalin jabeer zai kwanta a cikin kabarinshi in har wannan auren ya yiwu saboda masoyanshi ne kuma hakan zaisa ako da yaushe su dinga tunawa dashi, amma in mukayi sakacin barinsu suka auri bare to fa zasu manta dashi cikin adduoinsu ko ba jima ko ba daďe,
alhj basheer yace haka ne kaka, to ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairin dake cikin auren, Ameen sukace gaba dayansu sannan suka kama wata hirar...

Zaune take a gefen gado kanta na kallon sama hawaye na gangarowa daga gefen idonta,
cikin muryar damuwa Hajja dake zaune a gefenta tace yanzu dan Allah bazaki yi tawakkali ba Afeeyah, ace yau kwana bakwai babu ci babu sha sai aikin kuka, duk kin rame kin lalace, wannan kukan da kikeyi bashi zai dawo da jabeer ba, Allah ya fiki sonshi shiyasa ya ďaukeshi daga wannan rikitaciyyar duniyar, kamata yayi hakuri ki dangana lamarinki ga Allah ki dage wajen yi mishi addu'a wannan shine kadai zai nuna lallai son da kike mishi babu algus a ciki, kinsan yadda jabeer ya tsani yaga zubar hawayenki gashi saboda shi kin kwana bakwai kinayi ba bacci bare cin abinci, gaskiya in har kikace haka zaki cigaba dayi hankalinshi bazai taba kwanciya ba gara ki dawo da walwalarki kamar yadda kika saba duk da nasan da kamar wuya amma hakan zaki daure tunda kinsan ba'a taba mutuwa an dawo ba,,
Afeeyah tunda har manzon Allah S.A.W yabar duniya to ki tabbatar da babu mai shigowa cikinta ya zauna,
muma yau ko gobe zamu bi jabeer inda yaje,,,
Cikin kuka Afeeyah tace Allah yasa yau ďin ne, Hajja kin kasa ganewa ne, nayi duk iya kokarin da zanyi in hana kaina kuka na kasa,
dan Allah ki fada min yadda zanyi in daina kukan mutuwar yaya jabeer, tun ina karama bansan kaina ba fa nasanshi,
ya bani kulawar da babu wanda ya bani ita, ya soni ya kaunace ni, kuma yayi yaki da duk wani abun da zai sani damuwa,
ta kara fashewa da kuka murya na rawa tace ya Allah ka sassauta min wannan jarabawar tayi min zafi da yawa,,,,
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣7⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Zama tayi a gefenshi cikin muryar kuka ta gaisheshi,
sai da ya ďan jima sannan ya kalleta batare da ya amsa ba yace bazan hanaki hawayen nan ba dan bansan dalilin zubar su ba,
ki zubar da su san ranki in kin gama sai ki saurareni,,
Afeeyah ta haďiye kukan hade da goge hawayenta tace nagama kaka,
kaka liman ya kalleta yace kin tabbata,,
ta gyaďa mishi kai tana ajiyar zuciya, yace to Allah ya kara miki hakuri ya kuma kara miki dangana, tace Ameen,

kaka liman yace magana nakeso muyi dake, inaso ki saurareni kuma kiyi wa maganar kyakyawan duba a mizanin hankali, kina jina,?
tace eh inajinka,
yace madallah,
yau jumma'a dai2 kwana bakwai da mutuwar jabeer ko ba haka ba,
tace haka ne kaka,
yace gobe sati, satin da yaso zama ranar tarihi mafi girma a rayuwarku ke da jabeer,
sai kuma Allah mai kowa mai komai bai yarda ba saboda dama ya rubuto ke ba matarshi bace kuma shima Allah ya rubuto bazai taba yin aure a rayuwarshi ba zai koma gareshi,
Shin Allah baya sonku ne yayi muku haka,
ta girgiza kanta da sauri,
yace Allah shi kadai ya barwa kanshi sanin boyayyen alamarin dake tattare da rayuwarki shiyasa ya ďauke jabeer a lokacin da kike bukatarshi domin ki fuskanci wata rayuwar,
ki sani Afeeyah in har a rubuce a allon Allah gobe ne ranar da zakiyi aure to babu makawa sai an ďaurashi, Allah sarki jabeer, bayan iyayenshi da yanuwanshi baiso kowa ba kamar yadda yaso ku ke da Affan, shin a soyayyar da jabeer ya nuna miki zaki iya cika burinshi da ya fara bai karasa ba,
da sauri tace koda kuwa wahalarshi zaiyi sanadiyyar raina kaka,,
alhmdullh kaka yace a zuciyarshi sannan yace bana fatan yayi sanadiyyar ranki jikata, nasan zakiyi duk abinda nace,
jabeer ya dauko aiki mai matukar hatsari kuma Allah bai bashi ikon karasawa ba, yanzu ni da ke zamu karasa shi amma banason ya zama hatsari a gareki,
Afeeyah dole ki fitar da kanki a sahun yara domin ke ba yarinya bace, dole ki zama mai jajircewa a cikin wannan kasadar da zamu sa kanmu,
da siyasa nakeso muci yakin nan domin yakin yafi karfin yinmu amma baifi karfin Allah ba,
Allah yasa zaki daure zuciyarki in kikaji jahadin da zakiyi domin masoyinki,
Afeeyah tace koma menene zanyi kaka in shaa Allahu,, kaka liman yayi murmushi cikin jin dadi yace Afeeyah gobe in Allah ya kaimu zaki bar gidanku ki koma gidan Alhj basheer da zama a matsayin matar ďansa,
mikewa Afeeyah tayi da sauri tana girgiza kanta idonta ya fara kawo ruwa tace kaka" Affan??, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
kaka liman yace nutsu Afeeyah ki nutsu ki zauna muyi magana domin babu abinda zai hana wannan auren sai Allah, kafin ki shigo dakin nan nayi istahara akan lamarin nan na gano abubuwa da yawa saboda haka ki zauna mu cika ma marigayi burinshi,
Afeeyah ta zauna tana kuka tace kaka har abada bazan taba iya auren wani ba, bazan iya ba,
na daukarwa kaina alkawarin bazan yi aure ba har in koma ga mahaliccina, nasa a raina ni zan zama uwar gidan yaya jabeer a aljanna,
kaka liman yayi dariya yace kuruci dangin hauka, alkawarin ki kenan, kika san alkawarin Allah akanki, bakisan mijinki ba, yawan ya'yanki da kuma adadin rayuwar zakiyi kafin ki koma gareshi,
dan haka ki kauda wannan maganar ki fuskanci rayuwar gaba, jabeer ya riga ya tafi bazai dawo ba dan haka mu ida aikin alkhairin da ya fara domin samar ma ruhinshi salama,
nidai bazan faďa miki komai yanzu ba,
zanso ki zauna a gidan ki fara ganin komai dake faruwa da kanki hankalinki zai baki ki gane abinda nake nufi, zan dinga waiwayoki akai akai dan akwai yan tambayoyi da zan dinga miki domin mu dinga sanin matakin dauka ta kasa2, duk abinda kika gani karki nuna kin gani saboda tsaro kin gane ko,
Afeeyah da kuka yaci karfinta ta kasa magana sai kallonshi kawai takeyi yana mata jawabi kamar tace mishi ta yarda da maganar auren,
Chapter 25 · 0% Book details