← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 48

Sashe 37

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tafe take a cikin gidan tana bin inda bata taba bi ba tun zuwanta gidan a zuciyarta tana yabawa da kyau da tsarin gidan,,
Kamar giftawar walkiya ta hango wani katon DAMO yana bin wata mata tana gudu tana salati haďe da ihun neman ďauki,
da sauri ta bisu tana addu'a zuciyarta cike da tsoron wannan damon dan bata taba ganin suffa irin tashi ba,
ja da baya tayi saboda yadda ta hango wannan damon ya hankaďa matar cikin wani kewayayyen flower bed ya haye kanta,
tun tana jiyo ihun matar har ta daina jiyowa saboda matar ta nitse ciki sai tashin kura mai karfi kawai take gani,,,
a firgice ta juya jikinta na rawa ta hango wannan damon ya fito daga cikin flower bed din yayi gurin fishpond, yana zuwa gurin ya rikiďa ya koma kifi ya shiga ciki,,
a hankali ta tako ta leka cikin ramin ta hango kifayen sun cure kansu sun zama kifi ďaya,
a gigice ta koma baya tana sauke numfashi tana fadin "innalillahi wa inna ilaihir rajiu'n," dan ganin yadda kifayen nan suka cure ba karamin daga hankalinta yayi ba,
cikin sassarfa tayi hanyar daki,
anan ne ta haďu da wani tashin hankalin dan ganin wata guntuwar halitta tayi a kofar ďakin oyizah tayi wuf ta shige ta kofa ba tare da ta buďe ba,
nan jikinta ya fara rawa ta leka ta window ta hango wannan halittar ta haye gado ta nutse cikin katifar,
wata dariya taji an saki mai karfi haďe da guguwar da ta fito da wani mugun bakin hayaki daga karkashin gadon,
da sauri ta juya zata koma ďaki taji haushin karnuka a bayanta, tana waigawa taga bakaken karnika sun fi ďari sun doso inda take suna haushi kamar zasu tsaga gidan,
a razane ta fara gudu tana fadin "hasbunallahu wa ni'mal wakil,"
bin ta karnunkan suka fara yi da gudu suna kara yin haushi,
tana zuwa kofar dakinta taji an taďiyeta ta fadi kasa sosai,
ja baya ta farayi tana kara karanto adduoi da karfi tana kuka,
wani irin tsalle wani katon kare yayi zai hau kanta,
a razane ta runtse idonta ta saki ihu mai karfi haďe da tashi daga baccin da takeyi,
Affan ta gani a zaune yayi tagumi yana kallonta,
kauda kanta tayi ta janyo wani zani a gefenta tana share zufar da ta jikata tana fadin
"'A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min ghadhabihi wa 'iqaabihi, wa sharri 'ibaadihi, wa min hamazaatish-shayaateeni wa 'an yahdhuroon.""
Singlet ďinshi yasa a gefen kunnenta yana share mata zufar da take gangaro mata daga kanta,
juyowa tayi ta kalleshi tace har ka tashi, karfe hudu fa yanzu,
ya karkatar da kanshi gefe idonshi ya ciko da kwalla saboda mafarkin mahaifiyarshi yayi amma sam ya kasa tina mafarkin,
da sauri tasa hannu tana share mishi kwallar idonshi tace menene,?
A hankali ya kwanta lamo a jikinta yana kara zana fuskar zeenatu a cikin kwakwalwarshi,,
shafa kanshi ta fara yi tana karanto addu'a tana tofa mishi a kanshi har bacci ya ďaukeshi,
haka suka kasance a wannan daren Afeeyah bata koma bacci ba dan tana matukar tsoron ta runtse idonta ta kara yin wani mafarkin....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari sukuku ta gama aikinta,
sai da suka karya sannan ta kirah kaka liman tayi mishi bayanin abubuwan da ta gani a cikin mafarkinta,
cikin mamaki yace na faďa miki mugun tsafine dankare cikin gidan nan,
yanzu gurare uku zakiyi aikin kisa a ranki Allah na tare dake,
ki tabbatar yau kinsa an hake wannan flower duk abinda kika gani a ciki ki cire shi,
sannan ki tabbatar wadannan kifayen yau basu kwana a gidan nan ba,
kisan duk irin dabarar da zakiyi kisa a fitar dasu daga cikin gidan a wanke gurin ya zamana ba komai a ciki,
sannan guri na uku shine mai wuyar, yadda zakiyi ki shiga wannan dakin nata har ki iya bankade karkashin gadonta,
Afeeyah dai ta gama tsorata matuka idonta ya ciko da kwalla tace kaka duka suna da wahala, wallhy har yanzu jikina rawa yakeyi,
yace nasani jikata nasan suna da matukar wahala amma Allah zai mayar maki dasu masu sauki daga kin fara,
dan Allah karki ji tsoro zan tayaki addu'a ina daga nan, Allah zai taimakeki saboda niyyarki mai kyau ce, kisan duk yadda zakiyi ki bankade na karkashin gadon nan dan duk wasu alkadaranta anan suke, in mun gama da wannan zan fassara miki na karnunakan nan,
jiki a sanyaye Afeeyah tace to kaka nagode sai anjima, yace to sai anjima Allah yayi miki albarka tace ameen kaka...

Karfe 11am ta fito daga ďakinta ta fara bin hanyar da tabi cikin mafarkinta,
sannu a hankali take tafiya har saida kafarta ta sada ta da wannan kewayayyen flower bed ďin da farida ke raya shi da ruwa babu dare babu rana,,
karasawa tayi gurin flower ta leka ciki dan tasan duk dabarar da zatayi a hake mata gurin,
ta kai minti uku a gurin ta hango tanimu mai Guga rike da bokiti a hannunshi,
da karfi ta kwala mishi kirah ya taho da sauri ya tsuguna yace hajiya gani,
Afeeyah tace dan dan Allah a ina zaka samo fatanya inason a shiga cikin nan ne ayi min digging dinshi naga kamar ana gyara sauran kullum banda nan,
tanimu ya rike baki yace wallhy hajiya ko katakon gurin nan ba'a yarda mu taba bare ganye bare kuma har mukai ga hakeshi,
Afeeyah tace to saboda me, yace wallahu aalamu, nima ban sani ba,
Afeeyah tayi tsaki tace kira min mati naga shi ke kula da flowers din gidan,
da sauri ya mike yaje ya kira mati suka taho tare,
dakyar da yaudara tace ma mati yazo ya hake mata saboda alhj yace za'ayi shuka ne a gurin,
jin alhj ne yace yasa mati zuwa dauko fatanya ya bude gurin ya fara haka tun karfi,
gefe ta koma tana addu'a tana kallonshi, yana tsakiyar hakan ne ya jiyo taurin wani abu, da sauri ya dago shi da fatanyarshi ya fara girgijeshi kasar na kakkaba,
Afeeyah na hango kafar ta gane ta dabba ce, da sauri tace mati ajiye dan Allah ka samo min ruwa in dauraye hannu na,
dasauri ya ajiye yayi gurin pampo,
cikin azama ta karasa tayi bismillah ta dauko wannan damon tayi cikin dakinta dashi ta naďe shi cikin wani zani ta turashi karkashin gado,
tana komawa gurin ta tarar da farida na balbale mati da masifah,
Afeeyah ta karaso da sauri ta kalli fuskar mati gwanin tausayi tace ya akayi ne mati, mati yace hajiya saida na faďa miki ba'a taba gurin nan kika dage sai na hake shi, gashi yanzu hakan na min barazana da aikina,
Afeeyah ta kalli farida dake harararta sannan ta maida kallonta ga mati tace dama wannan ce ta dauke ka aiki,
ya girgiza kanshi yace a'a, Afeeyah tace to dan me zatayi sanadiyar aikinka,
naga dai wannan aikinka ne, ko alhj yasan baka gyara wannan flower,
mati yace a'a bai sani ba,
Afeeyah tace to maza ka cigaba da aikinka tunda dama dan albashi kakeyi,
farida tace ke kuma asuwa dan uwarki,
Afeeyah tace ni as uwarki dan ita uwar taki,
fareedah ta rike baki cikin mamaki tace mummy kike zagi,
Afeeyah tace uwata ce ita ko kuma kina tunanin uwa tafi uwa ne,
kai mati cigaba da aikinka in ka gama kayi watering din gurin ka rufe ni ina da abin yi,
farida ta hassala ta finciko Afeeyah da karfi tace wallhy yau sai naci ubanki a gidannan,
duka duka yaushe aka haifeki da zaki tsaya kina gaya ma mutane magana,
Afeeyah ta haďe rai sosai tace sakeni kar muyi creating sin a gurin nan,
farida tace baza'a sakeki ba,
Afeeyah ta buge hannunta da karfi tace dallah sakeni,
farida ta daga hannunta cikin fushi zata mareta Afeeyah tayi saurin rike hannunta tace karki fara wannan gangancin dan wallhy bazamu kare faďan nan yau ba,
ki bar ganinki katuwa wallhy babu abinda zaki dauka ajikina dan abun a zuciya yake, kuma sannan da kike cewa yaushe aka haifeni to bari kiji ko jiya aka diga maniyyi na na fito yau na fiki daraja a idon duniya saboda nayi aure kuma nasamu Apple of marriage, ke fa? har yanzu kina gida babu mashinshini bare har yayi yunkurin dauka, tayi wurgi da hannunta taja tsaki ta wuce ta barta tsaye idonta jajur....
Chapter 37 · 0% Book details