← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Juya kan motarshi yayi ya nufi gurin wani babban malami dake zaune a Tarauni,
saida ya jira malamin ya gama da almajirai sannan ya shiga suka fara zantawa,
Bayan malamin ya gama jin bayanin jabeer sai ya jinjina kai yace tabbas imani yayi karanci a wannan zamanin, na dade banji rashin imanin da har yakai wannan ba,
ya kalli jabeer yace in shaa Allahu zamu hadu mu fadawa Allah nan da kwana uku zuwa hudu komai zai dai2ta kai dai ka dauke kafarka daga gidan ka barta cikin tunanin baka fadama kowa dinba sannan kayi taka tsan tsan da ita, jabeer yace to malam nagode sosai ya ajiye musu kudin sadaka sannan ya mike ya fita,
Gurin malamai uku yaje a ranar duk yayi musu bayani suma sun dauki alkawarin yi mishi addua ba dare ba rana,,
ranar jabeer ya yini cikin bakin ciki babu yadda ummi da Afeeya da hajja basuyi ya faďa musu abinda ke damunshi ba amma yaki fadi,
Afeeya har kuka tayi mishi duk dan ya fadi amma bata samu nasarar ya fada din ba,

Oyiza kuwa rasa yadda zatayi tayi, ya akayi wannan mayen yaron ya shigo gidannan ya hayo har sama yaji sirrina, kallon affan tayi da ya fara bacci saboda tsoron abinda ya gani a gate,
wani dogon tsaki taja a zuciyarta tana tunanin yadda zatayi da jabeer, yanxu tasan yama gama tona mata asiri saboda haka in ta dau mataki akanshi jama'a zasu zargeta gara tabi komai a hankali..

Kwana biyar da faruwar wannan alamari oyiza taji shuru babu Wanda ya tinkareta,
sannan alhj basheer bai canza mata ba kamar yadda tayi tsammani,
hakan ya bata karfin gwiwar fara aiwatar da duk wani mugun nufinta saboda a tunaninta tsafinta ne ya toshe ma jabeer baki ya ki fadawa mutane,

Shi ko jabeer hankalinshi a tashe yake dan duk malaman da yasa su addu'a kowanne larura ta faďa mishi, daga wanda ya rasa ďanshi sai wanda yayi paralys sai kuma wanda ya rasa mata,

cikin tashin hankali ya dawo gida yayi tagumi yana tunanin mafita,
"Kaka liman" ne faďo mishi a rai nan da nan ya kira wayarshi,
kaka liman yasa wayar a kunnenshi ba tare da ya duba wanda ya kirashi ba yace "malam dan boko dan Bara'u jikan limamin Daura ya ta dabo,"
jabeer yayi dariya yace lafiya lau kakan dan boko ta dabo na gaida Daura, ya kuma tsufa da tsohuwa,
kaka liman yace tsohuwa tana can tana damun hura kasan bata son ayi mata kishiya,
jabeer yace kai ka isa kayi ma Goggo kishiya, kaka liman yace kaji ja'iri kaima fa naga auren nan zakayi nima ina ga cikin satin nan zan nemo wata a cikin nan nijar auro,
jabeer ya kwashe da dariya yace gara dai ka tafi can dan matan nigeria sun fi karfinka, kaka liman yace lallai baka san wanene Abdullahi ba,
a gobe in matarka nakeson aure tana ganina shikenan kai kuma taka ta kare, jabeer cikin dariya yace dan Allah karka kasheni da sauran raina, bari in fada maka dalilin kiran da nayi maka,
kaka liman yace inajinka,
jabeer ya kwashe komai ya faďa mishi har larurar malamn duk ya faďa mishi, kaka liman ya ajiye goron hannunshi yace wannan ta shahara matuka jabeer, ka kirani zuwa karfe takwas na dare zanyi binciken duk wani kullin da sukayi dan sai an fara takanshi kafin a tsunduma cikin addua,
a wannan karan bada malami zata gwabza ba da ni "liman dan Baba" zata gwabza jinina da duk na wani nawa ya fi karfin matsafa saidai idan abun yazo da karar kwana,
jabeer yace to zan kiraka kaka nagode sosai,
kaka liman yace ďan nema rike godiyarka in zaka taho ka siyomin shaddoji da kayan mata in haďa a lefe in auro sabuwar amarya, jabeer yayi saurin kashe wayar yana dariya...

Duk wasu abubuwan tsafi da kulle kulle babu wanda kaka liman bai gani ba, abinda ya kasa ganewa shine na zeenatu gata nan dai an nuna mishi ita a baccinshi bata motsi kuma an nuna mishi tana nan kusa dashi saidai baisan takaimai gurin ba,
ko da yayi ma jabeer bayani yace dole akwai hake haken da sai an haka sannan za'a warware abubuwa sai hayaki da wasu magungunan da zai haďa mishi, dan haka ya bashi kwana uku yazo ya sameshi sai suyi wanda zasuyi a daura sauran ya tafi dashi ya karasa a kano,
jabeer yaji daďi sosai ya dinga ma kaka godiya saboda yasan ko ba komai abokinshi zai samu lafiya kuma zaayi punishing oyiza 4 her deeds,

Tun daga ranar kaka liman yake aiki babu dare ba rana duk da ana yawan kawo mishi farmaki cikin dare haka suke gwabzawa har su hakura su tafi su barshi,
ranar kuwa da ya gama haďa magungunan saida gidanshi ya kusa rushewa saboda girgiza,
bai wani tsorata ba saboda shima hatsabibin bafulatani ne, a cewarshi shi a duniyar nan baiga abin tsoro ba banda Allah shi kadai yake tsoro a ko dayaushe amma mutum dan adam wanda Allah ya ara ma lokacin tsafi ko wani abu to ba abun tsoro bane dan idan Allah ya tashi tarwatsasuu a lokaci daya zaiyi ba tare da bata lokaci ba...

Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Sati ďaya ya rage bikinsu,
lokacin yayi daidai da kammala jarabawar su Afee,
Fitowarsu kenan daga exam hall ita da safnah kowannensu sai share zufa yakeyi, skul mosque suka wuce sukayi sallah suka zauna bin inuwar gurin saboda gajiya, hira sukeyi duk akan jarabawar da suka zana yau kuma ta karshe,
sai da suka fi minti talatin sannan suka mike da niyyar tafiya gida,
a dai2 gate din fita makaranta suka tsaya ganin anyi cincirundo kan wani yaro ďan ss2, Afeeyah tayi tsaki tace dadina da skool dinnan son gulma dan Allah ji yadda aka wani zagaye yaron can kowa so yakeyi yaji abinda ya sameshi, safnah tace may be abin da ya sameshi babba ne dan kuka yakeyi sosai gunin ban tausayi,
Afeeyah tace to Allah ya kyauta muje ko, safna tace ga "Zulaikha Sambo" can tahowa bari tazo muji me ya faru,
Afeeya tayi tsaki tace dan Allah safnah mu tafi wato kema kin fara son jin abinda bai shafeki ba ko,
kafin safnah tayi magana zulaikha ta karaso gurin su, safnah tace Zully me ke faruwa a can gurin, zully tayi fuskar tausayi tace wallhy mahaifiyar waccan yaron ce ta rasu yanzu aka zo aka faďa mishi, safnah tace ayyah Allah ya jikanta mutuwar mahaifiya ay babbar cuta ce tanada zafi sosai walhy,
Afeeya da jikinta yayi sanyi tace Allah ya rahamsheta mu kuma yasa mu cika da imani, suka amsa da ameen,
safnah tace ay mune abin tausayi Afee, gara ke tun kina karama kika rasa taki yanzu zaiyi wuya wata mutuwa ta girgiza ki,
zully tace kwarai kuwa,,
Afeeyah tayi murmushi tace har gobe ina tunawa da mamana duk da bawani daďewa mukayi tare da ita ba, wallhy kullum na kalli hotonta sai na zubar da hawaye,
mutumin dake debe min kewar tunaninta tun ina karama shine wanda bana fatar rasa shi har karshen rayuwata,
ta kalli safnah tace kikace babu mutuwar da zata girgiza ni, to wallhy kinji na rantse da Allah bana fatan mutuwa akan yaya Jabeer amma ni nasan duk ranar da aka ce min ya mutu to nima binshi zanyi in kuwa lokacina baiyi ba to walhy ko in haukace ko in zama marar amfani,
dariya suka saka sosai safnah tace ay ke baki da hankali,
da in mutum na mutuwa ana binshi kuma Allah baya sa dangana da duk wadanda suka rasa makusantansu suma sun dade da mutuwa,

Afeeyah tayi tsaki tace dan Allah ya isa haka maganar mutuwar Allah yasa mu cika da imani,
suka amsa da ameen sannan suka wuce zuciyar Afeeyah a dagule dan ta tsani zancen mutuwa...
Chapter 18 · 0% Book details