← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 48

Sashe 19

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar haka Afeeyah ta wuni sukuku,
wasu irin muggan tunanin mutuwa takeyi, da taga abin bazai fishsheta ba sai ta ďauki qur'ani ta fara karantawa,
a haka jabeer ya tadda ita,
gaisheshi tayi haďe da ajiye alqur'anin a mazauninshi,
kusa dashi ta dawo ta zauna ta zuba mishi ruwan da hajja ta ajiye mishi ta mika mishi tana kallonshi, kallonta yayi shima da ya karbi ruwan yace yau naga duk kin wani natsu ne ko wani ne ya taba min ke,
ta gyada mishi kai,
ya ajiye ruwan hannunshi yace to menene, ko kina son wani abu ne,
ta kara girgiza kanta,
ya bata rai sosai yace akwai damuwa a fuskar nan kinada wanda zaki faďawa da ya wuce ni,
tace um um,
yace to fada min da sauri kinji, idonta ya ciko da kwalla muryarta na rawa tace ba komai,
hajja tace iskanci ne kawai fa da shagwabar banza yau ko abinci bata ci ba saboda abin ya motsa,
jabeer yace dan Allah hajja kiyi shuru karki kara bata min ranta, tashi muje waje ki faďa min kinji,
ta mike jiki a sanyaye suka fita,
a zaure suka tsaya ya kalleta yace ki mayar da kukan nan kar ki bari ya zubo, in naji abinda ke damunki ya cancanci kuka sai in tayaki muyi tare kinji,
ta gyada kai har lokacin kwallah na makale a cikin idonta, yace to inajinki waye ya taba min ke,
ta shagwabe fuska tace ni ba abinda ke damuna kawai dai ina tunanin mutuwa ne,
ta shige jikinshi sosai tace yaya jabeer ay bazaka mutu ka barni ba ko,
ya sa hannunshi ya kankameta hade da lumshe idonshi yace mutuwa lokaci ne Afee babu wanda yasan ranar mutuwarshi,
ta dago kanta tace ni nasan lokacina yaya jabeer,
jabeer ya tallabi fuskarta yace wace irin magana kikeyi,
tace ni nasan duk ranar da ka mutu to nima zan mutu,
yace to ke waye yace miki zan mutu, tace ba kowa ina dai fada maka ne,
yayi dariya sosai yace to naji,
ta marairaice tace dan Allah yaya jabeer karka mutu kabarni kai kadai nake dashi a duk duniyar nan,
kai kadai kake understanding dina, kuma kai kadai kake tolerating dina, kai kake sani dariya kuma ka hanani kuka,
dan Allah ka dinga yi mana adduar in mutuwa tazo ta daukemu lokaci ďaya kaji,
yayi murmushi ya share kwallar da ta zubo daga idonta a zuciyarshi yace yaro yaro ne, ya kalleta yace naji amma ki daina kawo mana maganar mutuwa ke da zaki zama amaryata ranar Saturday,
kar in kara ganin hawayen nan kinji, tace too,
yace yauwa babynah, kin san meye, ta girgiza kai tace a'a,
yace banaso in faďa miki sai kin min alkawari,
tace alkawarin me, yace alkawarin bazaki yi kuka ba, kuma bazaki damu ba, kuma zaki min addu'a,
tace umm nayi alkawari Allah ya bani ikon cikawa,
yace ameen baby,
ina zanje daura gobe amma fa gobe zan dawo in shaa Allah,
Afeeyah ta karkatar da kanta gefe tace ni um umm wayau kamin wallahi na kwance alkawarin,
yayi dariya sosai yace ba'a kwance alkawari yarinya, dan Allah kimin hakuri gobe kawai akwai abinda zanyi mai muhimmaci, kuka ta fara yi tana bubbuga kafa tace wallhy ni bazan yadda ba saidai mu tafi tare, ya rike baki yace ina zamu tafi tare, tace daura mana,
yace haba Afee nah yanzu kinaso in ďaukeki mu tafi gurin su kaka liman tare, ay sai suce amaryar ma bata da kunya,
ta turo baki tace naji ay sau ďaya zasu ce, ya daura hancinshi kan nata yana gogawa a hankali yace haka zasu dinga faďa kullum,
jikin Afeeya ya mutu sosai saboda yadda yakeyi da hancinshi kan fuskarta, ta kalli idonshi dake lumshe ta fara kokarin kauda fuskarta,
hanata yayi ta hanyar daura bakinshi kan nata a hankali yace I love uu to d moon nd bck baby,
ta sunkuyar da kanta kasa tace I love u too yayana,
yace to tunda u love me ki barni inje I promise you komin dare in na shigo gari zanzo in ganki kinji,
ta kalli cikin idonshi tace ko biyu na dare ne fa zan jira ka,
yace na yarda baby kiyi fatan Allah ya kaini lafiya,
tace to Allah ya kaimun kai lafiya ya dawo min da kai lafiya, yace ameen Afee nah,
sun daďe tare a ranar suna hira kamar kar su rabu,
Da kyar suka rabu gurin 11 ya tabbatar mata zai shigo ya ganta kafin ya tafi,.
rakiyar kura suka dingayi har saida ya gaji ya kaita har cikin daki ya tabbatar ta kwanta sannan ya tafi gida cike da nishadi, ya yi matukar kosawa Afeeya ta zama mallakinshi, shi yasan auren Afeeyah shine lst dream dinshi, yasan yana aurenta ya gama samun komai a rayuwarshi,
da wadannan tunaninkan masu dadi bacci yayi gaba da jabeer da gidan Bara'u...

Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Tun 5 saura na asuba jabeer ya farka jikinshi duk da ya jike da zufa, duk sanyin a.c dana damuna basu hanashi yawan jin zafi a yan kwanakin nan,
bayi ya shiga yayi wanka da ruwan sanyi ya ďauro alwala ya fito yayi nafila ya zauna jiran a kira sallah..

Yana idar da sallah ya zauna kan kujera ya lumshe idonshi kanshi na kallon sama,
Allah kaďai yasan tunanin da yakeyi a wannan lokacin,
sai 8 ya mike jikinshi a sanyaye ya gama shiri cikin farar shadda, yayi matukar kyan da bai taba yin irinshi ba shi kanshi saida ya faďi da ya kalli madubi,,,
saida ya gama shiryawa tsaff har zai fita daga ďakin sai kuma ya dawo ya dinga kallon ko ina ko akwai abin da ya manta bai dauka ba, drawer ya buďe ya dauko driving licences dinshi har zai rufe drawer sai yaga wasu takardu,
daukosu yayi ya dubasu yayi murmushi ya mayar dasu mazauninsu ya rufe drawer yasa kai ya fita daga ďakin,

A parlor ya tadda babanshi zaune yana karyawa ya tsuguna ya gaisheshi, ya amsa da fara'a yace sammako zakayi kenan,
jabeer yace eh baba ina son in dawo da wuri ne shiyasa,
Abida ta fito rike da cup din kunun gyaďa da plate din alale ta zauna kusa da mijinta, jabeer yace ina kwana ummi,
tace lafy lau jabeer yau dai kaka liman yayi kira irin wannan sammako hka,
jabeer yayi dariya yace na kosa inje in ga uwargidana sarautar gida shiyasa,
ta gutsiri alalen ta kai bakinta tace kace ka kosa kaje kuyi faďa har ku gaji,
yayi dariya yace kamar kin sani,
dai2 lokacin Amirah ta shigo parlorn cikin uniform itama rike da break dinta a hannu ta gaisheshi ya amsa yace miko min naki kije ki zubo wani, Amirah ta turo baki tace yaya fa nayi latti dan Allah kasa Dayyaba ta zubo maka,
alhj bara'u yayi mata dakuwa yace gidanku, zubo abincin ne zai hana ayi miki dukan latti, ajiye mishi kije ki zubo wani,
Amirah ta ajiye tana kunkuni ta wuce kitchen ta zauna ta zuba wani kunun tana sha tana mita,
shima jabeer kaďan yasha kunun ko alalen ma bai taba ba ya mike yayi sallama da iyayenshi sukayi mishi fatan Allah ya tsare hanya,
har ya shiga mota yaji kamar ana kwala mishi kirah,
fitowa yayi ya nufi parlon yace gani baba, alhj bara'u yace ban kira ka ba jabeer saidai ko umminka,
Abida tayi dariya tace muna tare a zaune zan kirashi baka ji ba,
ta kalli jabeer dake tsaye yana kallonsu yana murmushi tace ni wai me ma zakayi a daura ne ka kirkiri tafiyar gaggawa,
alhj bara'u yayi dariya yace zuciyarki ce ta kirashi kenan dan tayi mishi wannan tambayar,
jabeer yayi dariya kamar zai faďa musu sai kuma ya fasa yace ziyara kawai zanje yi ummi,
tace to Allah ya bamu ladan tare, duk sukayi dariya haďe da cewa ameen,
kallon babanshi yayi yace baba akwai maganar da zamuyi dakai akan wasu takardu suna nan a ďaki na in na dawo in shaa Allahu zamu tattauna, alhj bara'u yace Allahumma yashaa ka gaida Baba da Goggo,
yace zasu ji sosai ya fita Amirah ta biyoshi da gudu tana mishi bye bye,
hararta yayi yace Allah yasa a fasa miki jiki da dukan latti,
tayi mishi gwalo ta shige mota tana dariya tana daga mishi hannu,
shima motarshi ya shiga ya tada ya fita yana gaisawa da baba ado da sauran masu aikin gidan..

Hanyar daura ya ďauka ba tare da ya tsaya yaga Afeeyah ba saboda yana gudun bata mishi lokaci da zatayi dan yasan in har ya shiga to bazai taba tafiya da wuri ba,,
Karfe 10 da mintina ya isa gidan kaka liman, bayan ya huta yaci abinci da furah suka dinga hira dasu Goggo, basu fara aiwatar da komai ba sai da sukayi sallar azahar sannan suka fita shi da kaka liman,
suna tafe yana mishi bayanin irin mugayen tsafin da akayi ma Affan wadanda aka binnesu a cikin gidan, kaka limann yace saboda rashin imani irin na matar nan har kafin fita gida tayi mishi dan kar ma ya fita wani ya ganshi yayi mishi addu'a ko ya taimaka mishi, sannan ta katangeshi daga dukkan adduar mutane ta mantar da mutane ciwonshi in ba waďanda suke kusa dashi ba,
jabeer ya jinjina kai yace ay ni ban ďauka zaluncinta har ya kai haka ba walhy kaka, amma in shaa Allahu karshenta yazo,
Chapter 19 · 0% Book details