← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 48

Sashe 30

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan hajja ta gama rarrashinta ta zuba mata abinci ta karba ta fara turawa da sauri saboda azabar yunwar da takeji,
cikin tausayawa hajja ta fara bata baki cikin hikima da kalamai masu taushi,
sai da ta tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ta tashi tafi gida cike da tausayin yar jikarta da ta fara dandana rayuwar duniya, dan da sam Afeeyah bata san bacin rai ba kullum cikin farin ciki take in ka ganta tana kuka to na shagwaba ne, babu wanda zai taka ta ta barshi bare har ya daura mata bacin rai duk wanda yayi mata take zata mayar mishi ta wuce hankalinta kwance..

Haka rayuwar Afeeyah ta kasance cikin kunci da bauta,
wulakanci kala2 babu wanda bata gani,
sam bata bari Affan ya ganta ko yazo yana bubbuga kofarta bata budewa,
ba karamin tausayi yake bata ba in ya fara buga kofar dan baya bugun hankali yana bugata yana ihu wani lokacin ma harda kukanshi,
abinci kuwa saidai hajja ta kawo mata dan bata nasu,
duk wannan wainar da ake toyawa alhj basheer bai sani ba saboda baya gari,

A ranar da ta cika sati uku a gidan tana tsaye tana mopping dining room,
oyizah da suwaiba suna zaune cikin parlon suna gulmarta,
suwaiba tace lallai yarinyar nan ashe duk iskancin da take mana guri ta samu,
ji yadda take muku bauta kuma duk zagin da kuke mata ta kasa tabuka komai,
oyizah tayi dariya tace ay wargi ma guri ya samu,
ni yaushe kamar wannan yarinyar zata tsaya min a gaba, ai wallhi kema suwaiba harda laifinki,
suwaiba tace ai da dinma daurin gindi ta samu to yanzu mai shagwabatan ya mutu shiyasa shegen bakinta ya mutu,
oyizah tace ai ko shugaban kasa ne ya tsaya mata bata isa ta min ba bare wannan tsinannan yaron mai shegen girman kan tsiya..

Afeeyah ta yar da mop din hannunta ta runtse idonta zuciyarta na tafarfasa,
muryar salma taji a bayanta cikin isa da gadara tace
kee..
je kiyi min pepper soup mai yaji sosai yanzu nan ki kawo min,
Afeeyah bata juyo ta kalleta ba ta tsalleke ruwan da take mopping dashi ta kama hanyar side dinta,
da sauri salma ta bita tana huci taja rigarta ta baya har saida wuyan ya yage tace ke dan uban--- Afeeyah ta juyo cikin azama ta dauketa da gigitaccen marin da ya hanata karasawa yasata sakin Afeeyah bata shirya ba....

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah

A firgice oyizah da suwaiba suka yo kan salma dake rike da kunci idonta yayi jajur,
fuskarta oyizah ta ďago tana shafawa ta kalli Afeeyah murya a sarke tace m-ari,
suwaibah ta jinjina kai a munafurce tace tabdijam, lallai yarinyar da tsaurin ido kike, ki kalli girman salma ki dauketa da irin wannan marin,
Afeeyah taja tsaki ta juya zata wuce oyizah ta saki salma ta janyota da karfi tana huci,
ihun da Afeeyah ta saki yayi daidai da shigowar alhj basheer parlon,
da sauri ya karaso yace subhanallahi lafiya safiya, me tayi miki,
oyizah ta saki Afeeyah da sauri ta juyo ta fara hawaye tace alhj ace kamar yarinyar nan ta dubi salma ta tsinka mata mari,
Afeeyah ta durkushe ta fashe da kuka tace dan Allah daddy ka kaini gurin hajja, wallhy kasheni zasuyi, dukana sukeyi kullum, yanzu ma dukana suka gama yi har suka yaga min riga,
dan Allah ka kaini gurin hajja,
kafin alhj basheer yayi magana mahmud dan suwaiba ya shigo rike da kular abinci a hannunshi,
ta gefen ido Afeeyah ta hangoshi cikin muryar kuka tace mamu kai min daki ka dauko kular jiya,

alhj basheer cikin mamaki yace meye a cikin kular nan, Afeeyah tace abincin rana na ne,
alhj basheer cikin tashin hankali yace duk abincin dake gidan nan sai an kawo miki abinci daga gida,
oyizah da ta gama tsurewa tace umm al--- Afeeyah ta katseta da sauri tace sunce abincin gidan nan ba na talakawa bane wai ban saba cin irin shi ba saboda haka kar in taba musu,
oyizah ta sankare cikin mamakin sharrin da Afeeyah ta lafto musu,
alhj basheer ya juya ya kalleta cikin tuhuma tayi saurin cewa wallhy karya take min alhj, ya za'ayi in hanata abinci,
alhj basheer ya kalli mahmud yace kai tun yaushe kake kawo ma Afeeyah abinci, mahmud yace kullum nake kawo mata da safe da rana da daddare,
alhj basheer ya saki salati yace kin kasheni safiya,
kin tozarta ni a unguwar nan, yanzu kowa ya gama sanin sirikata daga gidansu ake kawo mata abinci,
oyizah tace wallhy alhj kar---rufe min baki ya fadi cikin daga murya,
ya dago Afeeyah ya kalli wuyan rigarta yace yi shuru ki share hawayenki karki kara cewa zaki je gida sannan yau ďinnan zan siyo miki komai na abinci ki dinga girkawa kina ci a dakinki,
salma cikin kuka tace daddy marin da yarinyar nan tamin taci bulus kenan,
alhj basheer ya juyo yakai mata wani marin a baki yace in mafaďin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane,
yaya za'ayi Afeeyah ta iya daga hannu ta mare ki,
salma cikin kuka sosai tace na rantse da Allah daddy ta mareni,
ta kalli Afeeyah suka hada ido ta sakar mata gwaloo hade da murmushi salma ta kara tunzura tayo kanta zata duketa alhj basheer yace wallhy tallahi kika taba yarinyar nan sai na lahira ya fiki jin dadi,
oyizah dai tana tsaye kamar gunki mamakin Afeeyah ya hanata cewa komai, haka suwaiba,
Affan ne ya fito da gudu jin muryar mahaifinshi, rungumeshi yayi iya karfinshi yace daddy ka dawo,
alhj basheer yace na dawo Affan kana nan lafiya ko,
Affan ya noke wuyanshi ya haďe rai yace daddy nayi fushi da Afeeyah bazan kara mata magana,
alhj basheer yayi murmushi yace me tayi maka,
Affan yace batason wasa dani kullum sai su anty salma suyita sata aiki ta goge can, ta goge nan, tayi girki da yawa kuma ita bata ci, kuma sai ta rufe kofa ta hanani shiga inyita bugawa taki buďewa,
alhj basheer ya harari salma da oyizah sannan ya kalli Afeeyah yace meyasa bakya bude mishi kofa,
oyizah tayi saurin cewa dan Allah alhj kabar maganar nan muje ka huta anjima sai ayita,
alhj basheer bai kalleta ba yace Afeeyah dake nake magana,
Afeeyah ta dago kanta ta kalli oyizah da zufa ya jikata tace daddy saboda shan maganinshi ne na dare, kafin lokacin yayi nayi bacci bana sanin yana bugawa,
oyizah ta saki ajiyar zuciya a hankali..

alhj basheer yace wannan ba hujja bace daga yau ma duk magungunshi ke zaki dinga bashi,
Affan ya kalli oyizah yace mummy wai ita zata dinga bani magani?
Oyizah ta haďiye miyau tayi murmushi tace eh hakan ma yafi, Affan ya kalli Afeeyah yace zaki dinga bani magani dakyau yadda mummy take bani,
Afeeyah tayi murmushi ta saci kallon oyizah tace sosai ma, kasani ma ko in fita iya baka da kyau,
yayi tsalle ya rungumeta yace to muje mu dauko magungunnan mukai dakin mu ko,
alhj basheer yayi dariya yace banason shirme ka bari mummynka zata kawo maka har ďaki,
ya kamo hannun Afeeyah yace zo muje muyi wasa irin na rannan,
Afeeyah tayi saurin fisge hannunta ta wuce daki cikin jin kunya, ya bita a baya da gudu,

alhj basheer ma daki ya wuce ba tare da ya kalli oyizah ba,,
suwaiba tace kinga abinda nake faďa miki game da yarinyar nan ko,
oyizah tace uhummm kawai ta wuce daki salma ta bita har lokacin kuka takeyi,,, suwaibah taja gyalenta itama tayi waje...

Karfe huďu na yamma alhj basheer ya dawo gida motarshi cike da kayan abinci,
masu aikin gidan maza su suka shiga da kayan lokacin Oyizah na zaune a parlor tana ta tufka da warwara, ko kallonsu batayi ba har suka gama shigewa da kayan suka fita,
shigowar alhj basheer ne yasata mikewa da sauri tana mishi sannu da zuwa, bai amsa mata ba yace kin kai wa Afeeyah magungunan,
oyizah tace yanzu zan kai mata alhj, dan Allah ka fahimceni wallhy--yayi saurin dakatar da ita da hannu yace babu abinda zaki fada min in yarda,
tsakani da Allah safiya a bani amanar yarinya ku hadu ke da yayanki ku dinga kuntata mata,
oyizah ta fashe da kuka tace wallhy alhj sharri tayi mana, kaima kasan abinda zanyi da wanda bazanyi ba,
yace in ke baki mata ay yayanki na mata kuma bakya tsawatar musu,
Oyiza ta kara tsananta kukanta tace dan Allah kayi hakuri wallhy zan dauki kwakwaran mataki akan su,
dakyar alhj basheer ya hakura kuma yasa ta kira su salma yayi musu concrt warning akan Afeeyah...
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah
Chapter 30 · 0% Book details