← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 48

Sashe 2

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana shiga ta tarar da kausar na buga k'ullun alale, sam kausar bata kula da shigowarta ba sai saukar wata sanda taji akanta da karfi, zafin ya gigita ta sosai tasa ihun da ya fito da inna suwaiba da hajja daga ďaki,
cikin rudewa inna suwaiba ta kama kausar tace kausar meya faru, kausar ta kasa magana sai kuka takeyi hannunta rike da gurin jini na fita,
hajja ta kwace sandar hannun Afiya tace yanzu ke saboda tsabar mugunta wannan murďaďďiyar sandar kika buga mata,
Afiya ta turo baki tace hajja fa baki san abinda tayi min bane shiyasa,
inna suwaiba cikin fushi ta saki kausar tace uban me ta miki, Afiya ta murguďa baki tace gata nan ki tambayeta,
inna suwaiba tace lallai yau za'a haifi ďa mara ido a gidannan wallhy,
Afiya tace a haďa harda mara hanci ma a haifa,
hajja ta bige bakinta tace ke wai wace irin yarinya ce da baki jin maganar kowa,
Afiya tace to wai hajja ita baki tambayeta me tace mana ba, ce mana fa tayi yan iska, inna suwaiba tace ay kunfi karfin ya'yan iska saidai na guguwa, wallhy yau saina miki shegen duka a gidan nan sai na tabbatar wannan tsinannan bakin naki yayi laushi,
Afiya tace Allahn da halicci baki na shi kadai zai iya sashi yayi laushi ba wata ca--- hajja ta toshe mata baki tace na shiga uku ni Giďe, yanzu ke Afiya bazan miki magana kiji ba, inna suwaiba tace hajja ki wuce daki ki barni da yarinyar nan wallhy yau sai na mata lahani a gidannan, Hajja tace kiyi hakuri suwai--- karki bani hakuri ki cuceni hajja kullum mu kenan a cuce mu a taushe mu, to wallahi bazan dauka ba,
ji yadda jini ke zuba a kan kausar ay dan tasan kuna daure mata gindi ne ke da malam shiyasa take abinda takeso, in ba ta raina mutane ba ay kausar ba sa'arta bace,
hajja tace kiyi hakuri dai nace suwaiba, Afiya ta harari hajja tace wai hajja hakuri kike basu ni baki bani hakuri ba sai su da babu abin ma da nayi musu,
inna suwaiba ta hassala sosai tayi kan Afiya ta cakumota, hajja ta riketa tace wallhy suwaiba karki taba min marainiyar Allahn nan,
wallhy kika kuskura kika sata kuka sai ranki yayi matukar baci,
inna suwaiba tace ay ko sai dai ya baci ta kaima Afiya duka ta goce tana kicikicin kwacewa,
kausar dake jin kanta kamar dutse ta mike tazo ta bayan Afiya ta kai mata duka, Afiya tayi kukan kura ta kwace jikinta a gurin inna suwaiba ta haye kan kausar inna suwaiba na jibgarta ita kuma tana jibgar kausar, hajja na gefe tana kuka ita sam bata ma ga dukan da afiya kema kausar ba ita dai tafi jin dukan da akema Afiya,
dakyar da taimakon shigowar malam faďan ya rabu kowa na maida numfashi, kausar bayan inna taje ta boye tana kuka sosai saboda taji jiki, Malam Atiku cikin bacin rai yake ma inna faďa itama cikin fushi take mayar mishi,
yace yanzu in banda ke babbar kwabo ce meye na shiga faďan yara, wai ke in an barki ga mai ýa ko, kin gama zubar da mutuncinki a idon karamar yarinya, inna cikin fushi tace faďa min mai mutunci a idon wannan shegiyar yarinyar,
hajja ta fashe da kuka tace wallhy ba shegiya bace, Danbaba ni na gaji da zaman gidan nan kullum sai sun tsokani yarinyar nan ita kuma Allah bai ďiga mata hakuri a ranta ba gara muyi nesa dasu su zauna su kadai a gidan,
malam Atiku yace babu inda zaku hajja, baku da inda yafi nan, zan dauki tsatstsauran mataki akan wannan alamarin,
inna suwaiba tayi tsaki ta hararesu tace ka daďe baka ďau mataki ba, wannan yarinyar wata rana saita dauko muku na barin gari, ta kama hannun kausar suka wuce ciki tana masifa zuciyarta na ķuna saboda Afiya, ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun nasara akan Afiya,
zama tayi bakin gado idonta yayi jajur dan ba karamin caza mata kwakwalwa Afiya keyi ba,

Can kuma dakin hajja fada sosai suke ma Afiya akan rashin hakuri, malam atiku yace ni wallhy na rasa inda yarinyar nan tayi gadon wannan halin hajja ko kadan bata da hakuri komai aka mata tace saita rama kuma rayuwa bazata taba tafiya haka ba,
Allah na tuba kayi hakurin ma ya ka kare a wannan zamanin bare kuma bakayi ba, hajja tace ay ni yanzu inaga nawa ido tsakanina da Afiya dan gani sukeyi kamar goyon bayanta nakeyi ni take ďaura ma bakin jini dan kawai taga banason abinda zai bata mata rai shiyasa takeson a dinga ci min mutunci,
Afiya ta fashe da kuka tace dan Allah hajja kuyi hakuri in shaa Allahu ko duka na zasuyi bazan kara tanka musu ba,
hajja tayi tsaki tace ke ďin ce zaki faďi magana in yarda, malam atiku yace hajja muyi mata addua babu mamaki bazata kara ba,
Afiya tace Allah abba bazan kara ba,
hajja tace to Allah yasa da gaske kikeyi, duk suka ce ameen, nan suka cigaba da yi mata nasiha akan rayuwar duniya cikin dabara suke mata nuni da illar rashin hakuri,
Afiya jinsu kawai takeyi dan ita bataga rashin hakurin da aketa ikirarin tana dashi ba ita dai tasan ko manzon Allah s.a.w yace in aka bata maka ka rama dai2 yadda akayi maka, to ita kuwa akan me zata yarda tanaji tana gani a taka ta, bazai yiwu ba,, har suka gama nasiharsu Afiya tana gyada kai kamar taji abinda suka ce sai gab da magriba malam atiku ya fita suma suka tashi suka je yin alwala...

Tun daren ranar take zuba idon ganin jabeer shiru har kofar gida ta fito ta tsaya tana kallon kofar gidansu ko zata ga fitowarshi amma ko giftawarshi bata gani,
kullum ta dawo skull sai ta tambayi hajja ko yazo, in hajja tace bai zo ba nan zata fara sababi tace hajja kawai ki fadamin ko kin fita yazo baki nan ko kuma kina baccinki bakisan yazo ba,
hajja saidai tayi tsaki tayi banza da ita ta cigaba da abin da takeyi,
Afiya ta damu sosai da rashin ganin jabeer ji takeyi kamar ta mutu saboda rashin ganinshi haka kawai zata zauna taki cin abinci tayi ta kuka hajja bata ko kallonta bare ta rarrasheta..

Yauma kamar kullum a cikin sati biyun da tayi bata ga jabeer ba tana zaune ta haďa kai da gwiwa tana rero kuka hajja ta ajiye mata abinci a kusa da ita ta zauna gefenta ta kira sunanta, bata dago ta kalleta ba ta cigaba da kukan da takeyi, hajja tace to shikenan tunda bazaki saurareni ba dama jabeer ne,,, ta ďago kanta da sauri tace me ya sameshi hajja,
hajja tace yana nan cikin koshin lafiya baki ga yadda yayi kyau ba, dazu kina makaranta yazo yace in faďa miki yana gaisheki in ya samu lokaci nan da wata daya bayan kin gama jarabawa zai zo ku gaisa,
idonta ya ciko da kwalla tace hajja wata daya? Hajja tace eh mana, ba yace kince ya tafi gaba da birnin sin ba,
to ba wasa nake mishi ba afiya ta faďi haďe da fashewa da kuka, hajja tace ay ko shi da gaske ya ďauka,
Afiya ta maida kanta cikin gwiwoyinta cikin kuka tace shikenan kar ma yazo din dama nasan so kawai yakeyi ya kasheni,
hajja ta gimtse dariyarta tace kull kar na kara ji, duk laifinki ne meyasa in yayi miki magana bakya ji,
Afiya tace to ba nace na daina ba kema shaidace yau sati biyu kenan banyi fada da kowa a gidan nan ba kuma suna tsokanata meyasa baki faďa mishi haka ba, da wani abun nayi da yana zuwa zaki fada mishi amma saboda nayi abun kirki shine kika ki fada mishi,
Hajja dariya taci karfinta sosai ta mike ta fita tana dariya ita kaďai,
Afiya ranta ya kara baci ta kwanta tanata kuka harda sheshsheka tana tausayin kanta dan tasan in bata ga jabeer ba nan da kwana biyu to tabbas zata iya mutuwa,,,
muryar hajja taji tana kwalawa Mahmud kanin kausar kira,
ya taho da gudu yana buga ball yace hajja gani, tace Gidan Alh Bara'u zan aikeka,
Afiya ta mike zubur ta dakko hijab dinta ta fito tace zanje hajja, hajja ta kalleta tace da wannan kumburarren idon zaki shigar musu gida,
Afiya tace eh dashi zan shiga ni dai ki fada min sakon,
hajja tace to ay sai kije ki shiga din mu gani zonan mamu kaji ta miko mishi kullin magani tace kace a aikawa Asiyah nayi mata bayanin amfaninsu,
ya karba yace to hajja, bin bayanshi Afiya tayi ta hađe rai tace bani, jikinshi na rawa ya mika mata hajja tace Afiya karki fita gidannan haka ko uniform baki cire ba, bata saurari hajja ba ta fita dan so kawai takeyi yau ko ta halin k'ak'a taga jabeer....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣
By Aysha Ya'u Kurah
Chapter 2 · 0% Book details