← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 48

Sashe 27

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zubur Affan ya mike daga kan kujera ya karaso kofa yana faďin daddy na ya dawo, yana buďe kofar ya hangosu da Afeeyah suna tahowa ya rugo da gudu yana cewa oyoyo barbie, chakk" ya ďagata cikin murna yana jujjuyata ya karaso cikin parlon da ita yana fadin mummy kizo ga barbie nah daddy ya kawo min,
wani irin kuka Afeeyah ta fashe da shi yayi saurin sauketa yana nunama daddy hannunshi yana faďin ba ruwana daddy wallhy bani na sata kuka ba,
alhj basheer yayi dariya yace kai ka sata kuka nima babu ruwana bari ma in tafi kar ace har dani,
Affan ya zaro idonshi zaiyi ma oyizah magana tayi saurin jifanshi da mugun kallon da yasa shi ďauke kanshi ya ďago fuskar Afeeyah kamar zaiyi kuka yace ay bani na saki kuka ba ko,?
Afeeyah tayi banza dashi ta cigaba da kukanta,
alhj basheer yace zo nan diyata ki zauna rabu da shirmenshi,
Afeeyah taja kafarta a hankali ta zauna a kasa kusa da alhj basheer Affan ma ya biyota ya zauna kamar zaiyi kuka,
alhj basheer yace share hawayenki ki bude idonki ki gaisar da mamanki da kuma yayyinki,
oyizah tayi saurin cewa ta mayar da idonta abinda muna tare kullum yanzu,
alhj basheer yayi murmurshi yace haka ne,
ya kalli Afeeyah yayi mata yar nasiha ya kuma roketa da ta kula da Affan ta rikeshi amana sannan yace suje oyizah ta nuna mata ďakinta,
oyizah ta mike tace ma Afeeyah ta tashi suje,
kafin Afeeyah ta mike Affan ya mike yace barbie tashi muje ďakinmu,
Afeeyah ta mike tabi bayan oyizah da ya"yanta zuwa side din Affan,
saida tayi addu'a sannan ta shiga ciki ba tare da ta ďago kanta ba,
oyizah ta kalli Affan da ke binta a baya tace to bita zaizai wuce ka tafi daki,
Affan ya bata fuska yace ay nan ne yanzu ďaki na,
Salma ta daka mishi gigitaciyar tsawar da tasa shi fita da gudu, dariya suka watse dashi suka dawo da kallonsu kan Afeeyah,
oyizah ta ďago kumburarriyar fuskarta tana mata kallon banza tace "so called Amarya,"
farida ta kwashe da dariya tace su amarya man gyaďa,
salma ta hada rai tace kuna dariya ne, ay sai ta samu damar raina mu, mummy ki bata warning din da zaki bata mu wuce dan wallahi na mugun tsanar ganin yarinyar nan,
oyizah tace me kike ci na baka na zuba,
ta kalli Afeeyah tace nasan dalilinki na auren Affan bai wuce saboda dukiya ba, to kin makaro yarinya saboda ke da Affan kunyi ma juna nisa kamar tsakanin gabas da yamma saboda Affan is under my control sai abin da nace mishi,
Sannan kisa a ranki aikatau ne ya kawoki gidannan ba zaman aure ba,
salma tace gud mummy dama tunda "Gaje" mai aikin shegiyar mum din Affan ta tafi bamu kara samun mai aiki mai tsafta ba yanzu tunda mun samu wannan sai muyi manage,
oyizah kwarai kuwa, yanzu zan fara miki lissafin daily works din gidannan,
karfe 5 in kika tashi ba ruwana da sallarki in kinga dama kiyi in kinga dama ki barshi, fareeda tayi saurin cewa mummy wannan small gal din ma ay sallah bai wajabta akanta ba,
salma tace tell her ooo,
oyizah tace oho in taga zata wahalar da kanta tayi to tayi nidai amin aiki, girki shine first,
sai gyaran kitchen, gyaran ďakin yara, sai parlor,
tsakr gida da sauransu akwai maza masu yi,
Farida tace mummy wannan special secret flower bed din naki da nake bashi ruwa plss spare me ki kara mata shi a aikinta,
da sauri oyizah ta kai mata duka hade da yi mata dakuwa, farida ta toshe bakinta tace sorry mummy sannan ta fita da gudu,
oyizah ta gama lissafa wa Afeeyah duk aikin da zatayi a gidan hade da concrete warning na in ta saba aiki ko daya ne she will be in fr it,
Afeeyah dai gyada kanta kawai takeyi hawaye na kwaranya a idonta,
har sun sa kai zasu fita oyizah ta juyo tace lastly babu ruwanki da rayuwar Affan, ban yarda ku kebe tare ba bare har ki yaudareshi da wadannan shanyayun idanuwan naki,
salma tace haba mummy wannan mahaukacin meye zai rude shi,
oyizah ta harareta tace shi dutse ne ba mutum ba, mahaukata ma ay suna da feelings tunda akwai zuciya a kirjinsu, dan haka na horeki da kebewa dashi bare har--- ta yi saurin dafe kanta tace bana ma fata dan har abada,,,
salma tace har abada me, oyizah ta jata suka fita tace muje ďaki in faďa miki..

Suna fita Afeeyah ta fashe da kuka tana kiran sunan jabeer, kuka sosai takeyi har saida jiri ya fara dibanta sannan ta zauna bakin gado, saida ta gama tunane tunanenta sannan ta mike a zuciyarta tace Allah yasa yawan aikin da suka bani ya kasheni in huta,
drawer dake dakin ta bude zata sa akwatinta taga kaya masu tarin yawa wadanda ba dinkakku ba harda na bacci, cire hijab dinta tayi ta shiga bayin dake ďakin tayi wanka ta fito tana tsane kanta da towel,
tsawar da aka saki tayi daidai da bude kofar ďakin,
da sauri ta waigo tana kallonshi yana kokawa da mukullin kofar alamun yana saurin rufeta dan kar wani ya ganshi ......

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣0⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Kallonshi Afeeyah ta tsaya yi har ya rufe kofar ya waigo yana mata murmushi,
kau da kanta tayi ta janyo hijab dinta tasa ta zauna a gefen gado, karasowa yayi yana kaďa kanshi yana dariya ya tsuguna a gabanta ya daura hannunshi kan nata yace barbie yau kin dawo gidan mu ko,,
ta juyar da kanta gefe, ya taso ya zauna kusa da ita yayi narai2 da ido yace abokina ya faďa min kullum kina kuka da daddare meyasa kike kuka?

Afeeyah da idonta ya ciko da kwalla ta kasa ce mishi komai sai kallonshi da takeyi, hannu yasa ya share hawayen da ya digo a idonta yace ki mayar da hawayen nan dan Allah karkiyi kuka abokina zaice ni nasaki kuka in yazo,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka a zuciyarta tana mai tausayawa ranar da Affan zai san jabeer ya bar duniya,
kukan shima ya fara yi kamar karamin yaro yana share mata hawaye,

wata tsawar aka sake saki mai firgitarwa kamar zata rusa gidan saboda kararta,
da sauri Affan ya shige jikinta ya kankameta haďe da runtse idonshi,
wani abu mai wuyar faďuwa yaji ya tsarga mishi a cikin kwakwalwarshi,
wani irin shauki ya dinga ji a can cikin jikinshi,
shi kanshi ya kasa fassara yanayin daya shiga a wannan lokacin,
Turashi Afeeyah ta farayi tana kokarin mikewa tasa kaya,
kara kankameta yayi dan bayason ya daina jin abinda yakeji,

kallon fuskarshi tayi a hankali taga idonshi a lumshe yana fitar da wani irin numfashi, tausayi ya bata sosai saboda yadda ya koma cikakken mutum a haka kafin anjima ya birkice ya koma tababbe,

a hankali ya bude idonshi da ya fara canza kala ya saukesu kan nata,
da sauri ta kauda kanta tace dan Allah ka sakeni in sa kaya bacci nakeji,

sakinta yayi cikin muryar lafiyayyan mutum yace "muje in tayaki sawa" cikin mamaki ta zaro manyan idanuwanta tana kallonshi,
murmushi yayi mata ya mike tsaye ya bude drawer ya dauko mata cotton night gown ya mika mata,
kasa amsa tayi tana mishi kallon mamaki, ajiye rigar yayi a jikinta ya hura iska cikin idonta yace ko ni zan sa miki da kaina,
tayi saurin kauda kanta ta ďauki rigar ta faďa bayi tana tunanin canzawarshi lokaci Guda,

tsaye ta sameshi gaban mudubi yana zana kanshi yana dariya,
ta mudubin ya hangota ya juyo da sauri ya janyota yace zo kigani na iya drawing mutum a mudubi, tsaya anan kigani,
Afeeyah ta girgiza kanta tace bacci nakeji,
ya girgiza kai a shagwabe yace ni sai kin tsaya,
Afeeyah ta haďe rai ta juya ta wuce kan gado ta kwanta,
zama yayi a kujerar dressing mirror yana kumbure2 yana kunkuni shi a dole an mishi laifi,

Ko kallonshi batayi ba tayi kwanciyarta ta shige bargo tana karanto adduoi,

muryarshi taji saitin kunnenta yana faďin
Niko?
Niko?
Ya faďi haka yafi sau goma Afeeyah tayi tsaki ta yaye bargon zata fara masifa hawayen da ta gani kwance a kuncinshi ya hanata, ta kalleshi murya a tausashe tace me nayi maka kake kuka,
ya kwanta kan cinyarta yace bake bace kika ki tsayawa inyi drawing dinki ba kuma kika tafi kika barni baki bani hakuri ba,
sai na fadama abokina ince barbien shi ta daina kirki yanzu,

Afeeyah tasa hannu ta share mishi hawaye tace kayi hakuri gobe zan tsaya yanzu bacci nakeji,
Affan ya ďago kanshi ya kalleta cikin ido yace ni bana jin bacci zaki rarrasheni inyi bacci,

Afeeyah ta dafe kanta kwalla ta cika idonta a zuciyarta tace ni kuma kaddara ta kenan, kwanciya tayi ba tare da ta bashi amsa ba tana hawaye tana hango da yanzu fa tana gidan masoyinta abin kaunarta jabeer,
hawa gadon Affan yayi ya kwantar da kanshi a bayanta, nan ta fashe da wani irin kukan da yasashi saurin kankameta yana rarrashinta,
runtse idonshi yayi yana sake jin abin da yaji dazu,

a hankali kwakwalwarshi ta fara daukar caji ya shiga shinshina jikinta yana lumlumshe ido,
kara matseta yayi lokacin da hannunshi ya sauka kan kirjinta a take ya saki ajiyar zuciya yana wani irin nishi,
cire hannunshi ta fara kokarin yi ta kasa saboda irin rikon da yayi mata, yafi minti biyar a haka yana sauke ajiyar zuciya yana sauraron kukanta da yake jinshi kamar waka a wannan lokacin,

mirginowa yayi ya ďago fuskarta idonta a rufe ya fara share mata hawaye haďe da bata hakuri,
bata bude idonta ba kuma bata tsayar da hawayen ba, kwantowa yayi ya haďa fuskarshi da tata yana gogawa a hankali,
cikin kuka ta bude baki zata fara masifah yayi saurin tura bakinshi cikin nata,
duk yadda taso fitar da bakinshi ta kasa saboda sam ya hanata damar hakan,
Chapter 27 · 0% Book details