← Book details Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 48

Sashe 6

Rabo Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Alhaji basheer tsugune yana gyara canvas din kafarshi cikin shigar blue nd white track suit,
mikewa yayi bayan ya gama ya kalli matarshi zeenatu dake gyaran gadon da ya tashi yace to ni na fita training, tace to a dawo lafiya yallabai,
yace Allah yasa sannan yasa kai ya fita,
Zagaye ya dinga yi yana jogging cikin farin ciki saboda yadda sanyin safiyya ke kaďashi,
yayi zagaye na tara yana yi yana hutawa, a zagaye na goma ne ya hango wani shima jogging din yakeyi dai2 gurin wata katuwar kwata kafarshi ta gurďe ya tafi zai faďa alhj basheer yayi saurin rikoshi yana fadin subhanallah sannu,
mutumin ya ďago yana gyara kafarshi yace yauwa nagode sosai gaskiya ka taimake ni, alhj basheer yayi murmushi yace mu gode ma Allah, mutumin ya mika ma alhj basheer hannu yace sunana Bara'u ina nan zoo road, "BB close" opp gidan alhj Basheer Balarabe,
Alhj basheer yayi dariya yace ni kuma sunana Basheer Balarabe (BB) nima ina zaune a zoo rd BB close cikin gidan Alhj Basheer balarabe,
Alhj Bara'u yayi dariya sosai yace ikon Allah alhj basheer, kaga yadda Allah ke abunshi ko, .
alhj basheer yayi dariya yace kai gaskiya bamu fitar da hakkin makobtaka in ba haka ba ga gida ga gida ace bamu san juna ba,,
Alhj bara'u yace ko 1week banyi da tarewa ba kuma nasa ayi min magana da duk makota na kai kaďai ne Allah baiyi zamu hadu ba saboda ance min baka gari,
alhj basheer yace kwarai kuwa ban daďe da dawowa ba, to ya unguwar tamu da fatan dai baka samun matsala,
Alhj bara'u yace walhy babu matsala unguwar cike take da mutanen kwarai naji dadin kasancewata cikin ku, Alhj basheer yayi murmushi suka fara tafiya yace to ya iyalin fa, Alhj bara'u yace tukunna dai har ansa rana jiranta nakeyi ta karasa skull zuwa nan da 3monts sai ayi in shaa Allah,
Alhj basheer yace Allah ya nuna mana kai kadai ne a cikin gidan kenan, alhj bara'u yace eh ni kadai ne amma weekends a daura nakeyi saboda rashin iyali, alhj basheer yace hakan yayi Allah ya taimaka yace ameen har suka karaso gida suna hira cikin kankanin lokaci suka saba da juna, a dai2 kofar gida sukayi sallama kowa ya shiga gida,
kanshi tsaye yake tafiya cikin gidanshi yana amsa gaisuwar masu musu hidima, yazo gab da shiga parlo yaji wata muguwar faďuwar gaba,
juyawa kanshi ya fara yi sosai ya dafeshi ya karasa parlon dakyar ya zauna kan kujera, zeenatu na can kitchen bata san halin da mijinta yake ciki ba,
runtse idonshi yayi siffar Oyiza ta dinga mishi yawo a cikin kwakwalwar kanshi, buďe idonshi yayi da sauri da ya tuno da oyiza gaba daya yaji wani abu ya tokare mishi kahon zuciyarshi, ga wutar son ganinta da ta ruru a zuciyarshi kamar wacce aka iza da petur,
mikewa yayi da sauri ya shiga bayi yayi wanka sharp2 ya fito ya shirya da gaggawa ya feshe jikinshi da turare ya debi kudi a sv dinshi na gida masu yawan gaske sannan ya wuce kitchen ya sami zeenatu,
Cikin rashin fahimta tace tafiya weekend kaiko ina zaka, yace abuja zeena alheri ne yake kirana,
tayi murmushi tace to Allah ya kawo mana alkhairin tare,
yace ameen yar matata sai na dawo, tace to Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya, yace ameen ya fita da sauri,
biyoshi tayi da gudu tace na manta ban fada maka ba, dan Allah zan shiga gidan Malam atiku gurin Ma'u tayi min kitso, yace to adawo lafiya tayi miki mai kyau fa, tace karka ji komai in dai kitson ma'u ne, yayi murmushi ya fita ya tafi...

Da kyar ya gane restaurant din, yana isa ya fito cikin farin ciki,,
tsayawa yayi turus saboda ganin gurin da yayi a rufe, jingina jikin motarshi yayi ya rasa me ke mishi daďi yanzu wa zai fara tambaya inda take anan gurin, ya kusa 30mins kafin ya shiga motarshi da niyyar tafiya,
kamar daga sama ya hango john yana bude gurin,
fitowa yayi da sauri kamar wanda akayi ma albishir da gidan aljanna, karasawa yayi yana kiran yaron, john ya juyo rai a bace saboda yadda yaji ana kiranshi ganin alhj basheer yasa john jindadi ya fito da gudu ya tsuguna a gabanshi ya gaishe shi,
alhj basheer ya amsa suka shiga ciki,
ya kalli john yace ina madam dinku, john ya raunana fuska yace madam is no more alhj tun ranar da kazo washe gari ta mutu, alhj basheer ya girgiza kanshi cikin tausayin oyiza yace Allah ya jikanta to ina yarta oyiza,
john yace tana gida dama tace idan kazo in kaika can gida, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi dan a tunaninshi kafin mahaifiyarta ta rasu tayi mata bayanin komai, tashi yayi suka fito shi da john suka shiga mota suka wuce gidansu oyiza...

Bayan ya gama yi mata gaisuwa yana rarrashinta saboda kukan munafurcin da take yi ita a dole tayi rashin uwa,
tausayinta sosai ne ya ratsashi ya tambayeta ko mahaifiyarta tayi mata bayaninshi,
tayi kasa da murya tace eh a daren ranar ta fada min komai kuma tace in ka dawo zata yarda ka aureni, ta fashe da kuka tace ashe bazata ga auren ba,
alhj basheer zuciyarshi ta kara narkewa yace kin yarda to zaki aureni, tayi kasa da kanta tace ko banaso zan yarda tunda shine last will din mahaifiyata, alhj basheer yace haka ne naji dadi sosai da kuka amince dani, yanzu ina son cikin satin nan a gama magnar komai muyi aure in tafi dake,
wani daďi ya ratsata tace to ba matsala bari in turo maka kanin babana kuyi magana, mikewa tayi ta shiga ciki ta turo mishi kanin babanta da wan mamanta,

Kudin da alhj basheer ya wankesu dashi da kuma nuna yanason ya auri oyiza saboda yana tausayinta shi kadai yasa suka yarda da auren suka sa rana ya biya sadaki da komai, sannan ya tafi cikin farin ciki,
A daren ranar ya fita da oyiza yawo ya siyo mata duk wani abu da mace zata bukata na aure,, sun daďe tare har suka saba sosai kafin su rabu,
Tana shiga gida ta dinga tsalle tana murna nan ta shirya ta wuce gurin chummy yin godiya....

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 9⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Cikin satin aka ďaura auren alhj basheer da Safiya oyiza a okene, shiri na musamman chummy tayi ma oyiza ta haďata da special kayan tsafi a cewarta su zasu taimaketa ta zauna lafiya saboda wannan matar tashi mai yawan addu'a,
Chapter 6 · 0% Book details