← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 159

Sashe 98

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta furta muryarta can kasa sosai. Shi ma sai ya bata amsa da muryar mai dadi da ta fi kama da rada ya ce

“Idan wannan ne farincikinki... Ni ma ina fatan haka Hurriya... Duk wani abun da zai yaye miki damuwa ya sakaki a cikin farinciki ina fatan ki same shi”

“Kana da kirki kana damuwa da ni, thank you for understanding me”

Kamar wata kwarariya haka ta yi masa magana muryarta a kasa fiye da yadda ta muryar shi take a lokacin da yayi mata magana.

“We all need that someone who get us like no one else, a right when we needed the most, you need shoulder to cry on...”

hura mata iskar bakinsa mai kamshi a fuskarta, atak, sai ta lumshe ido, murmushi ya fadada fuskarta hawayen bakinciki da suka rikide mata zuwa farinciki suka kawata kyauta. Kamar wanda ta tuna wani abu murmushin fuskarta ya bace bat, sai ta matsa baya da sauri ta bude idonta ta juya da fice daga kitchen din. Murmushi yayi ya taka backwards yana shafa kansa, ya daga gorar ya sha ya aje, sannan ya kai hannunsa saitin da aka aka yi gurbin zuciyarsa.

“Ajiya ce wannan, please ki ba ni hadin kai, saurin fushi breaking up with so many girls wannan duk na yafe miki, karki raba ni da wannan she's special na gane haka from DAY 1 na san ke ma kin san haka... ”

Ya rufe idonsa ya sauke dogon numfashi, ya kai ma zuciyarsa duka a hankali yana aje mata sako.

“Idan kika raba ni wannan ni da ke duka zamu cutu, wata kila mu salwanta in one way or the other, so try to be strong please, ki ba ni hadin kai i hope you understand me”

Zuciyarsa ta buga da karfi tana raba sakon da yayi aika mata ga sauran sassan jikinsa da suka kasance mukarraban aikinta. Ya bude idon yana murmushi, sai farinciki yake kamar wani sabon ango, ba shi da kwashe kwashen mata, amman idan ya ga wanda hankalinsa ya kwanta da ita ya kan tallata mata soyayyarsa, sau uku ya taba yin haka, sau biyu aka yi nasarar saka ranar aurensa aka fasa saboda rashin hadin kan da zuciyarsa take ba shi. Falo ya fito ya zauna yana kallon tv sai dai gaba daya hankalinsa ba a gurin tv yake ba. Ya kusan minti goma shabiyar da zama sannan Appa ya sauko Momy na bayansa waya a kunnesa.

“Gani nan zuwa”

Ya fice tare da twins dinsa, sai jan rigarsa suke. Momy ta zauna tana mamakin ganin Captain domin Appa be fada mata tana da bako ba, ko da yake ba zata kira shi da bako ba a yanzu daman tuni ya zama dan gida. Namra ma da ta haura sama da bacin rai bata fada mata Captain ya zo ba.

“Ban san ka zo ba?”

“Saboda Appa yana nan ne, tun dazun na zo ai”

“Maa Shaa Allah yau dai na san babu aiki yau Sunday, kuma na ga farinciki a fuskarka a yau fiye da ko yaushe, kana albishir ne?”

Yayi murmushi shi kansa ya san fitowarsa daga kitchen zuwa zamansa a falon nan ya banbanta da kullum, and baya bukatar wani ya fada masa yana farinciki ya fahimci haka tun a lokacin da sexy voice din Hurriya ya huda kuunnesa har ya karya dokokinsa, ga kuma numfashinta da ke masa yawo a saman hanci har yanzu.

“Wata kila nan gaba kadan na yi albishir, farincikin kuma ina fatan ya daure har abada”

“Allah ya tabbatar maka da shi”

“Ameen Momyna that's why i love you kina son farincikina”

“Kai dan gatan family mu ne Captain, idan wani be so farincikinka ba, to be so Familynmu ba”

Ya bude baki ya rufe yana murmushin gefen baki. Daga bisani ya kalli Momy ya aika mata da tambayar abin da ya tsaya masa a rai.

“Momy me yasa kannen Hurriya ba su taba zuwa gidan nan ba sai yau?”

Momy ta dan tabe baki.

“Alhaji ya juya musu baya tun da aka haifesu, ni kaina na yi mamakin yadda yau ya shigo min da su dakina ya dorasu har kan gadona yana wasa da su”

“Why?”

“To Allah masani Captain, wata kila shiga tsakani ne”

“Kuma mahaifiyarsu ba ta yi tunanin ta kawo su ba?”

“Ta ina? Ka manta na fada maka bata da lafiya? Aiko hannu bata iya dagawa, bata magana bata iya komai nan gaba kadan ma wata kila bara zata koma, domin dai ance duk abun da take da shi ya kare, daman talakawa talas shiyasa kwadayi ya ja ta auri Alhaji, yanzu kuma ta auren ya kare sai ta koma babu komai, ita fa wannan Hurriya kaskantacci ne uwarta ga aiki ta yi, ta zo gidan ta bangare Kaltume daga aiki ta aure Alhaji shiyasa Kaltume bata kaunarsu ko kadan ai, kara ni ina da zuciyar imani ina ragama mata amman can ba ta sha da dadi ai”

“Mahaifinta mai kudi ne i guess to me ya kawo zancen kaskanci?”

“Ai wannan talauci da uwarta take ciki ba zai taba gogewa ba a ido, kuma ba zai taba barin mutane irina su ga kimarta ba, ba gashi nan ta koma a kwance ba, da ynzu tana da arziki zata tsaya jinya haka ne? Shekara hudu yanzu ana fama da abu daya, ko Kaduna ba su taba kaita ba balle a fitar da ita, kuma wani lokacin da tana da kudi ai ba za'ayi ma yarta ko ita ba, yanzu ka hada ta ni? Ko ka hada Hurriya da Namra? Ai ba za su tana haduwa ba har abada, ka ga fa gidan nan kowa yana karatu wasu sun kare amman ita tun da ta gama SSCE ubanta ya aje ta gefe ko kallonta baya son yi, ya ki sakata makaranta da uwar tana da kudi ai ba za a yi ma yarta haka ba, ko kuma ta dauki matakin shari'a ta karbe yarta ta saka ta makaranta mai kyau”

Jawabin da Momy ta kora masa, be kara masa komai ba sai tausayin Hurriya, bayan kalubalen da take fuskanta a gidan ga damuwa na rashin uwa da dan'uwa a kusa, ga kuma rashin lafiyar ido, yanzu kuma ya kara jin halin da mahaifiyarta take ciki, talaucin da ya hana su ganin kimarta a gidan, ya kara mata martaba da tausayi a idonsa.

HURRIYA POV.

Ta rufe fuskarta da tafi hannayenta har lokacin kamshin iskar bakin Captain da ya hura mata be bar hancinta ba, bata taba samun kanta a yanayi kamamancin wannan ba, murmushi take kamar wata sabuwar mahaukaciya a rufaffun idanuwanta bata ganin komai sai fuskar Captain, all the good things da yayi mata suna ta dawo mata, bata da wani abun fada akansa sai khairy yana da kyakkyawar zuciya da tausayi ba kamar yadda ta ke tunani a baya ba. Bude ido ta yi ta sauko kasa ta zauna ta bude kwalin da ta dauko a falo tana duba abubuwan ciki, chocolate ne da sweet candy mai dadin nan, sai kuma gasashen kifi dake ta kamshi, tashi ta yi ta wanke hannunta sannan ta dawo ta zauna ta bude kifin ta fara ci. Bata fito dakin ba sai da dare shi ma saboda Yayanta Yasir ya shigo dakin ne ya bukaci ta fito su tafi kai Twins gida saboda Rukkaya ta matsa masa ya kawo yaran Gwaggo ma sai da ta kira da kanta, tsoronta duk be wuce na irin wulakanci da musgunawar da za'ayi ma yaran a gidan ba, ta fito tana sanye da green hijab dinta ta kama hannun yaran dake falo ta fice da su. Sai da suka isa bangaren Hajiya Kaltume sannan suka shiga motar Yasir yayi mata key ya fice daga gidan suka dauki hanyar gidan Gwaggo.

“Hurriya”

“Na'am”

“Dan Allah ki bawa Rukayya hakuri, kuma ki lallaba Gwaggo kar ta yo fushi, ni kaina ban jidadin abun da ya faru ba, gaba daya na rasa gane abun da ke min dadi gidan nan ya rikice, mun rasa Salma, Hajiya ba zata karbi soyayya ta Rukayya ba, Hajiya kuma tana asibiti yanzu haka? Gaba dayana rasa ina zan saka kaina na ji sanyi”

“Asibiti bata da lafiya?”

“Suma ta yi, amman da sauki gobe ma Appa yace ba za'ayi zaman gaisuwa ba, shiyasa aka yi addu'a uku a yau”

An yi addu'an uku kuma bata sani ba? Ta tambayi kanta.

“Ban san an yi ba, kuma ban san an kai Hajiya asibiti ba”

“Kina cikin daki koda yaushe Hurriya ya za'ayi ki sani, kin zaman dabam”

“Bana jindadin shiga cikin mutane ne, wani lokacin ina tsarguwa”

Ta dora hannunsa biyu a sitiyarin motar.

“I understand your situation now...”

Daga haka be kara cewa komai ba, har suka isa gidan.

“Ki aje su ki dawo na maida ke”

“Toh”

Ta amsa sai a lokacin ta tuna da siyayyar da Captain yayi musu bata ba su ba, kuma bata isa tace Yasir ya koma su dauko ba. Haka ta shiga cikin gidan tare da yaran ta mika su hannun Gwaggo tana fada mata abun da Appa yayi musu a jiya, Amma ta kalleta yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa da magana mai yawa a tare da ita amman babu bakin fada.

“A da yardar Allah komai zai warware, sai ta ga Iyami ta tashi da idonta, amman zaman aure kam ko da ya dawo yace zai maida Iyami ba zan yarda ba, aure ya kare kenan Allah ya bata na gari, wannan wahala da ta sha ta isa haka, amman wai duk wannan abun Rukayya bata gani ba saboda rashin hankali da tunani take kokarin daukar kanta ta jefa a gurin Kaltume? Me ake da Kaltume me ake da jininta? Har abada ko ba ni da rayuwa Rukayya ba zaki auri Yasir ba, sai dai ki mutu babu aure, na Iyami ma kaddara ce da ba mu isa mu kauce mata ba”

Rukayya ta mike tsaye ta fice daga falon gudun hawayen da suka tarar mata kar su zubar mata a gaban Gwaggo ta sha fada, daman tun jiya take mata masifa har yau da dare. Hurriya ta kalli Gwaggo cikin yanayin rashin dadi ta ce.
Chapter 98 · 0% Book details