← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 159

Sashe 57

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ai fa akwai iya kukan kamar yar drama, ba a dai taba sata a gidan nan ba sai yanzu, kuma babu wanda yake bangaren nan sai ke, sai dai kuwa masu aiki, ko da yake bari na rufe bakina ai ita wannan yar karuna ba a mata gwaninta, ni ma bata raga min ba ni din ma da na fi karfin shekara biyu rabona da kofar falonta”

Momy ta dago tana harar Hajiya Kaltume ta ce.

“Kwarai kuwa, a gidan nan ba a shaidar kowa, domin kowa shegen kansa ne, rufin asirin da Allah yayi min na san ai tsonewa wasu ido”

Hajiya Kaltume ta nunata da hannu.

“Ina arziki yake? Me kike da shi Nafisa? Babu abun da Allah ya baki wanda be bani ba, zan iya siye abun da kike siye to miye zai saka ma na aika a dauko min wani abu dakinki saboda gaki diyar Bill Gates ko?”

“Karya kike yi Wallahi, ki ce me nake da shi, ai ke kin san na fi karfinki sai gani sai hange, ni ba irin Iyami ba ce, ahe”

Appa ya daka musu tsawa rai a bace.

“Miye haka wai? Na taraku a nan ne saboda ku fara sa'insa? Musamman ma ke Nafisa kin fi kowa fitina a gidan nan, na fara gajiya da matsalalolinki”

“Allah ya raba ni da matsala, ka ga Matsala can”

Ta nuna Hajiya Kaltume sannan ta cigaba.

“Kuma daman ai dole ka ce ni ce mai fitina saboda ita wa'eh ta mallakeka baka ganin kowa sai bakar kaza, daman idan ta shiga akurki bata barin kowa ya shiga, idan ka gaji da matsalolina sai ka san yadda zaka yi da ni, amman ina mai tabbatar maka zama daram dam dam dam, domin babu inda zan tafi na barwa wata makira yar kasan wuta ta samin hannu a yaya”

Khairi ce ta yi karaf ta ce.

“Momy ba dai Hajiyarmu ce yar kasan wuta ba Wallahi sai idan ke”

Tana rufe baki Namra ta mayar mata da martanin.

“Ba dai Momy ba, sai dai ke Khairi yar shaye shaye kawai mai banzayen abokai”

Appa step on his feet ya sake daka musu tsawa sai da falon yayi tsif.

“Ku tashi gaba daya ku fice min daga falo, saboda kun raina ni, ku yi sa'insa a gabana yaranku ma su yi ko? Toh wannan ya zama na karshe, kuma daga yau sai yau kar wanda ya sake dorawa yata sata, ni na haifi Hurriya ko mahaifiyarta bata fini sanin halinta ba, Hurriya ba zata yi sata ba, Nafisa ki tafi can ki nemi wanda ya shiga dakinki ya dauki sarka da kudi, ki bincike masu aikinki amman Hurriya ba zata aikata haka ba, duk abun da nake yi ma Hurriya ina mata ne ba dan bana kaunarta ba, kuma haka ba yana nufin kowa ya kwaso shararsa ya watsa mata ba”

Ya kalli Hurriyya With Angry face.

“Hurriya tashi ki yi tafiyarki”

Hurriya bata san lokacin da wani sanyi ya ziyarci zuciyarta ba, hawayen da suka banbanta da na dazun suka zubo mata. A nan kam ta samu courage din yin magana.

“Na gode Appa”

“Ba zata zauna a bangarena ba”

Momy ta fada cikin zafin rai da daga murya. Appa ya watsa mata harara.

“To sai ki hada komai na ki ki bar mata bangaren, domin duk wanda ke gidan nan yana karkashin iko na ne”

Hurriya ta mike tsaye tana share hawayenta ta fice daga bangaren tana jin kamar an watsa mata ruwan kankara a kunar da zuciyarta take mata.

_____________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

*HURIYYA*

𝐊𝐇𝐀𝐃𝐄𝐄𝐉𝐀 𝐂𝐀𝐍𝐃𝐘

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

𝐏𝐚𝐠𝐞 1️⃣5️⃣

“Sam Sam Sam ni hukuncin da Alhaji yayi a gidan nan be yi min ba”

Cewar Hajiya Kaltume da shigowarta falonta kenan. Khairi ta yi karaf ta ce.

“Ba ke kadai ba Hajiya, ni Wallahi na dauka ma korar Hurriya zai yi, domin zata iya satar kudin nan”

Hajiya Kaltume ta zauna tana fadin.

“Ai ba nata ne ya ban mamaki ba, na Nafisa ne, yadda ta ci mutunci na ta dora min sata ban ji ba ban gani ba, amman ace Alhaji ya kyaleta ba tare da yi mata wani hukunci ba? Ni wane irin rashin godiyar Allah ne zai saka ni sata a bangarenta, ni ban ma san ta fita bangaren ba, amman da yake ta raina ni haka ta laka min sata, saboda bata da ta ido har da wani aiko masu aiki wai su zo duba mata bangarena, haka fa matar ta taba dora min laifin fasa tayar bakinta, ta maida ni kamar wata karamar yarinya”

“Wallahi Hajiya abun da Momy take yi a gidan yana wuce gona da iri, da zarar an taba ta sai tace ita mai kudi ce, mu gaba daya ganinmu take kamar wasu awaki ita kadai ce mutum”

Hajiya ta kara kashe ido domin laka mata sata da Momy ta yi da kuma kyalewar da Appa yayi be yi komai ba ya fi komai bakanta mata rai.

“To wai waye zan tura ya shiga ya dauki kudin a bangarenta, idan ma ba wanda yake bangaren ba waye zai san gurin da take aje kudinta, da sarka har a dauka, ko dai masu aikinta ko kuma ita wannan mai siffar macizan ce”

“Ni fa zuciyata ta fi yarda ma ita ce, amman kin ga yadda ta wani sha jinin jikinta sai kuka take ita munafuka, har Appa ya tausaya mata, wannan yarinyar da film take da ta kwashi kudi dominbta iya acting”

“Bar shi ai sai na masa magana akan haka, dan yau yaushe za a shaideshi ne, har da wani cewa wai duk abun da yake mata ba sonta ne ba shi ba, kin ji min wata maganar banza”

Sai da Khairi ta kalli kofa domin tabbatar da babu wanda zai shigo sannan ta kalli Hajiya Kaltume ta ce.

“Ya Yasir ma da wani ne sai yayi masa dukan mutuwa kamin ma a gane gaskiya, amman kin ga da yake Hurriya ce uffan be ce ba, balle har ta kai ga ya doketa, ai Wallahi Salma ta huta da tafi yin masters dinta a waje, Maama kuma ta yi aure babu mai shan wahakarsa sai ni, daman ni ya tsaneni a gidan nan”

Hajiya Kaltume ta daga mata hannu.

“Ni yanzu ba ta Yasir nake ba, maganar nan ba zan bari ta wuce ba, ba a dora min sata da kurciyata ba yanzu da yayana ba za a dora min sata na kyale ba, kuma Wallahi sai na bawa Nafisa mamaki sai na maidata abar tausayi”

Khairy ta dan kalli wayarta da sakwannin ke appearing saman screen din wayarta, ta dan bata fuska kadan da alamar damuwa sannan ta fara taba wayar tana reply kaminnta mike tsaye ta nufi dakinta. Hajiya Kaltume kamar tashinta take jira sai ta tashi ita ma ya nufi nata dakin ta dauki wayarta ta kira aminiyarta da bata iya boyewa komai, sai dai ga mamakinta sai da wayar ta yanke har sau biyu ana uku Hajiya Fatee ta amsa cikin wata murya dake bayyana damuwarta.

“Toh sawun giwa ya take na rakumi aka ce na kira na fada miki damuwata kuma na jiki a cikin wata damuwar lafiya Hajiya Fatee”

“Ina lafiya anje gyaran kai an kare wuya, Hajiya Kaltume ina nan cikin matsalar cikin nan, jiya da shekaranjiya ko bachi ban iya yi ba, na rasa madafa”

“Subhanallahi, baki sake kiran Malam ba? Ba na ce ki kira shi ba?”

“Na...”

Har zata yi subutar baki ta fada ma Hajiya Kaltume yadda suka yi da Malam sai kuma ta tuna gargadin da yayi mata.

“Toh zan kira shi, ni tsoron kiransa nake kar ya fada min wani abun da zai daga hankali na, domin na lura kamar akwai matsala”

“Aa ki kwantar da hankalinki Hajiya Fatee, kuma ki nuna masa damuwarki, kuma ki bi duk wani abu da zai fada miki, na san ba zai wuce kudi ba, ko kuma ya ce sai kin siya mishi wani abu, komai dai minene karki yarda cikin nan ya bayyana Hajiya Fatee domin bayyanar cikin nan matsala ce da ko mun mutu sai mun bar abun fada, duk tsanani karki yarda sirrinki ya bayyana”

Shiru Hajiya Fatee ta yi na dan lokaci kamin ta amsa.

“Toh Hajiya Kaltume, abun kunya ne kam sosai amman kuma idan ya fada min wani abun da ba zan iya yi ba fa?”
Chapter 57 · 0% Book details