← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 159

Sashe 117

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Fatee ta yi murmushi.

“Ai ni dole na zo na same ki Hajiya Kaltume shiyasa da Fadeel na kira cikin na ce ya zo ya kawo ni gidan nan, amman Hajiya gajin hakuri kika yi ne har kika aikata mata haka?”

“Ina fa wai ni? Wannan ai can ya fito tsakaninta da dan'iskan saurayinta, wata kila matsala suka samu shiyasa ya watsa hotunan, ai ni ya biya ya hutar da ni wannan kadai ya isa ya hana Hurriya aure, domin babu wanda zai daukarwa yayansa uwa irin wannan? Sai dai a samu dan baro can ko masu gyaran talkama a hada su, idan ma ta samu domin babu mai auren makauniya”

“Kuma kika ce ta rantse da kur'ane?”

“Haka Khairy tace, wata kila kuma wani ne acan waje yake taya mu fadan, kuma shi ma yaron nan ta yi masa wulakanci ba, kuma abun da zai baki mamakin idan ba su saba haduwa ba a ina ya samu hotunanta”

Hajiya Fatee ta kyalkyale da dariya ta bawa Hajiya Kaltume hannu suka tabe.

“Ai wannan abun yayi dadi Wallahi ana ganin yarinya kamar ta kirki ashe ita ma yar banza ce”

“To kin gani dai gashi Allah ya tona asirinta, ko uwarta ai zaman banza ta so samu gurin Alhaji shi kuma da yake ba dan'iska ba ne sai ya bijiro mata da aure”

“Amman ni abun ya ba ni mamaki da kika ce Alhaji be koreta ba, ga irinsu nan da yawa ana kora da ya korata da mun huta ma”

“Ni ma abun da yasa na kira na tambaye ki kenan ko dai Malam be fara aikin nan ba har yanzu? Kin ga shiru fa ina zaune a gidan nan amman Alhaji be yi wani unkuri na maida aurensa da ni ba, jiya kuma Khairy ta fada min kuka yayi ta yi yana tsinewa wanda yayi abun nan”

“Zai yi wahala ace ba a fara ba, ya kamata dai mu kara hakuri kar mu yi gaggawa, domin tun ranar da aka tura kudin na kira shi na fada masa an tura kudin kuma yace min sun shiga ya gani, har na yace min anjima kadan zai shirya ya tafi gurin Malamin nasa ya kai masa kudin, tun daga ranar ban sake jin wayarsa ba, ko yanzu na kira bata shiga ba”

Ta sake gwada kiransa a gaban Hajiya Kaltume aka ce wayar a kashe take.

“Kin ji ko? Ina tunanin ko dai wayar tasa ta fadi ne, har wadda ta hada mu da shi na kirata tace ita ma bata samun wayarsa a yanzu”

Da mamaki Hajiya Kaltume ta ce.

“To kuma be siye wata ba? Ni fa jikina ya fara sanyi Hajiya Fatee”

“Karki ji komai, ni na yarda da Malamin nan dari bisa dari, mu kara hakuri idan aka kara kwana biyu ba mu ji komai ba ni zan shirya da kaina na tafi kauyen na bincika na ji”

“Allah yasa dai yayi mana aikin mai zafi, so nake Alhaji ya zo jiki na rawa ya roki yafiyata kuma ya maida aurensa, sannan a shafe masa Hurriya da uwarta a ransa kuma a hana shi auren nan da zai kara a mallaka min shi na juya shi yadda nake so”

“Wannan ai a rubuce yake, daman ya fada miki irin aikin zai yi kuma zaki gani, ke dai ki kwantar da hankalinki ba gashi kin fara gani ba, wata kila aikin ne ma ya saka hotunan nata suka yadu”

Hajiya Kaltume ta rike baki tana mamaki da dariya.

“Haka fa.. Kin ga gaba kenan sai kora, kuma da yardar Allah sai Hurriya da uwarta sun koma bara, tun da idon ya rufe ba zan bar Alhaji ya nema mata magani ba kuma ba zan bari ya maida uwarta ba, kin ga rayuwa ta kare musu kenan, daman na fada mata sai na dandana mata bakinciki kuma sai ta gani, ba za a ci amanata a zauna lafiya ba”

“Wani abun ma sai nan gaba”

Suka bushe da dariya, Hajiya Fatee ta mike tsaye ta dauki hijab dinta ta saka.

“Bari na tafi kar na batawa Fadeel lokaci aiki zai je na ce ya kawo ni na ganki ya maida ni direba na yayi tafiya”

Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta yi mata rakiya suka sauko kasa suna hirar, bacin rai dake zuciyar Hajiya Kaltume tuni ya yaye saboda kawarta ta karafafa mata guiwa kuma ta kwantar mata da hankali. Ganin Khairy zaune a falon ya ba wa Hajiiya Fatee mamaki

“Ah... Na yi zaton kina waje? Tare da Fadeel muke fa”

“Na sani bana jindadi ne shiyasa”

Ta amsa a kasalance tana sauke ido kasa kamar munafuka. Hajiya Kaltume ta ce.

“Wai ke kam me yake damunki? Tun jiya kike wani laude laude kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki”

Sai Hajiya Fatee ta daga hannu tana fadin.

“Wata kila abun yar'uwar ne ya shafeta kin san abun da ya taba gira shi ya kai ga ido har ya taba hanci, idan abun da ta yi karki saka kanki a damuwa kwana nawa ya rage miki ki har gidan ma, kuma wannan ai abun farinciki a gurinku, kowa be lalace ba sai Hurriya na tabbatar da Iyami tana lafiya ace wani ne a cikin yaran Hajiya Kaltume yayi haka farinciki zata yi ”

“Kwarai kuwa shiyasa ni ma bana fatan alheri ya same ta sai sheri”

Hajiya Fatee ta wuce gaba suka jera da Kaltume har wajen gidan, kamin Fadeel ya juya motarsa suka nufi karamin gate din gidan na bangaren Hajiya Kaltume. Daga inda suke tsaye suka hango shigowar manyan motocin na alfarma har hudu cikin gidan, duka motocin aka nufi bangaren Momy da su.

“To baki kuka yi kuma?”

“Ta yi dai ita yar karyar arziki, ita din ma ba barinta zan yi ba Wallahi”

“Aifa ki bari aikin Malam ya fara kawai sai wanda kika so zai zauna a gidan nan, ni na manta ban fada miki ba Afrah fa tana gidansu yaran suna gidana shi kanshi jiya gida ya kwana”

Hajiya Kaltume ta rike baki.

“Ki ce Allah”

“Ba kina wasa da lamarin Malam ba? Hmmmm”

Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara ganin girman Malamin da kwarewar aikinsa, Afrah da ta gagari Hajiya Fatee yau ace Fadeel ya kora Afrah gida. Babu halin yin wata doguwar magana saboda Fadeel ya faka mota a gabansu ya budewa mahaifiyarsa.

“Hajiya Fatee zamu yi waya”

Hajiya Fatee bata sake furta wani abu ba saboda Fadeel yana gurin sai dai ta yi murmushi mai sauti ta shiga motar, Fadeel ya ja bayan yayi ma surukarsa to be sallama.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

Da tunani kala kala Momy ta sauko falon Namra na bayanta.

“Yaya yau kai ne a cikin gidana?”

Daddy dake zaune akan kujera tare da sauran yan'uwansa yayye da kanne yayi murmushi.

“Nafisa mamakin zuwana kike ne?”

“Kwarai kuwa, Yaya tun da aka kawo ni gidan nan sau daya ka taba zuwa gidan nan fa, da Hajiya Turai ce ba zan yi mamaki ba, amman ganinka ya saka ni a fargaba Allah yasa ba Captain ya ce na yi masa wani abu ba?”

Alhaji Munzali yayi dariya, Daddy ma dariyar yayi ya ce.

“Saboda ba ni da kunya zai na taso na kawo miki takakka har gida?”

Ta yi dariya.

“Namra duk a firgicce take ita ma ta dauka Captain ya turoka, saboda jiya ya zo nan yana neman a kai shi gidansu Hurriya na hana Namra, wata kila hakan ya fusata shi ya kai karata a gurinka”

“Hakan da kika yi ai kin yi daidai, Ammy sa ma ta yi masa magana be so ma amman daga karshe dai ya fahimta kuma yace ya hakura”

Momy ta zaro ido tana dukan kirjinta.

“Ya hakura yaya? Amman ya kyautawa kansa daman can yarinyar bata dace da shi ba Wallahi, ni daman na san Hajiya Turai ba zata yarda danta ya auri yarinyar nan ba”

Daddy ya gyara babbar rigarsa yana kallon Namra dake jera musu abun karyawa.

“So jiya mun yi magana da Captain saboda ya shigar da kara DSS yanzu kuma yana son ya janye karar ne a hannata komai a gurin mahaifinta, ni kuma yau zan koma Kaduna, shiyasa na zo yanzu na san be isa fita ba ina son na yi magana da shi mu kai karshe”

“Hakan yayi, ban da Abin Captain na son wahalar da kai miye na wani shigar da kara, yarinyar nan fa makauniya ce ma idon za su bude ba za su bude ba Allah masani amman ya tsoma kansa a damuwarta har da ikirarin aurenta kamar wanda baya cikin hayyacinsa”

“Wannan maganar kuma ina tunanin ta wuce Nafisa, ki sallamawa mai gidanki zan yi magana da shi”

“Toh Yaya”

Ta tashi jikina na rawa ta nufi bangaren Appa, a nan Daddy ya samu gaisawa da Namra yana tambayarta ya karatu.
Chapter 117 · 0% Book details