← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 159

Sashe 105

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya ta fada sannan ta mike tsaye ta fice, Hurriya ta bi bayanta bayan ta gaisa da kawar mahaifiyarta. Hindu ta zauna kamar yadda ta saba tana ta hira da Iyami, sai dai kai kawai Amma take iya daga mata ko da girgiza ko ta tabe baki, wani zubin kuma ta yi hawaye, sai dai bata iya cewa komai saboda an rike maganar. Hurriya bata bari Magariba ta yi mata ba ta yi ma Amma sallama da Gwaggo, Rukayya ta rakota har bakin Titi ta samu abun hawa ta hau ya kawo ta gida, a ranar Hurriya bata gwada cin abincin dare ba domin ta san za su iya samun matsala da Momy ko Namra ganin yadda kowa ya kullace akan Captain, daman kuma kamin ta fito gidan Gwaggo sai da ta ci abinci, a daki kuma sai ta dora da dan abun tabawar da Captain ya bata da be kare ba har lokacin.

*** *** ***

Ranar Friday Misalin karfe goma sha daya daya da rabi, Hurriya ta fito wanka tana daure da tawul ta tsaya gaban madubi tana tattara kitson dake kanta ta daure da ribbon sannan ta ya dauki tissue ta cire gilashinta ta goge sannan ta zauna ta fara shafa mai, slowly ta ji an bude kofar dakin, ta cikin madubi ta hango Captain tsaye yana kallonta immediately ta mike tsaye ta juyo ta kalleshi, facing cap din dake kansa ya cire da hannunsa na hagu ya rike yana kallonta, da sauri ta nufi gurin da Hijanbinta yake ta dauka sai a lokacin ya kawar da idonsa.

“Subhanallahi what is happening here”

Da sauri Hurriya ta nufo kofar dakin dake bude ta rufe sannan ta dawo gabansa cikin tashin hankali.

“Me kake yi nan?”

Ya kalleta sai yayi murmushi sai kuma ya nufi gadonta ya dora karamin kwalin dake hannunsa, daga bisani ya saka dayan hannunsa aljihu ya ciro wani box.

“Wannan zan baki”

“Minene?”

Ya bude box din ya ciro wani abun hannu na azurfa ya duka ya aje kwalin.

“Kawo hannunki”

“Yaya bana so dan Allah”

Ya daga kansa sama ya rufe ido. A take ta fara masa kukan tsoro da shagwaba a lokaci daya.

“Ina bindigarka take?”

“Tana mota”

Ya amsa ba tare da ya bude idon ba, domin kokarin kwantar da fushinsa yake that's why ya amsa mata kai tsaye, if not dauke ta zai yi da mari a gurin kuma bata isa ya tsaya yana neman ta yi abu tana masa wasa ba.

“Na san baka maimaita magana amman idan Momy ko Yaya Namra suka ga wannan abun a hannuna zai iya zame min matsala”

Ya bude idonsa ya kalleta.

“Baki murna da dawowarta Hurriya? Baki min sannu da zuwa ba, ban ga shaukin murnar dawowa ta a fuskarki ba why? A madadin haka sai tambayar kike me ya kawo ni dakin nan?”

“Baka saba shigowa nan ba, be kamata ka shigo ba idan Momy ta gani zata min fada, kuma Yaya Namra zata ji babu dadi kuma ko wacece ba zata jidadi ba ace saurayinta yana kula wata”

“Saurayinta...!?”

Ya fada as question as surprised.

“Ita tace miki ni saurayinta ne?”

Hurriya ta sauke idonta kasa.

“Na gane”

Ya fada yana dan hade rai, domin ya fahimci idan yana yi mata magana da sakewar fuska ba zata amsa masa yadda ya kamata ba.

“Ba ni hannunki”

A take ta fara masa kuka.

“Zata yi fada idan ta gani”

“Ba ni na baki ba? Wallahi wannan ba daga ni ba ne?”

“Waya ba ni Salim?”

“Come-on ya za'ayi Salim ya ba ni abu ya ce na baki kuma na baki har na bukaci ki saka”

“To ya ba ni”

Har yayi kamar zai yafa mata bakar magana sai kuma ya ji ba zai iya ba.

“Wani ne ya ce na baki, na ba shi labarinki yadda kike da kirki da tarbiya da kokari, sai ya yaba halinki kuma ya bukaci na baki wannan as gift kuma yace na gaishe ki”

“Ban san shi ba....”

“Ba dole sai kin san kowa ba....”

Ya daka mata tsawa.. Sai ta matsa baya ta fashe da kuka. Hannu ya kai ya dafe kansa.

“Please please ki daina min musu, idan ni na baki abu ba zan ji kunya ko tsoron fada miki ba, kuma ba zan miki karya ba”

Hannu ta miko masa, ba dan tana so ba sai dan tana tsoron wani ya tarar da shi a dakin. Matsawa yayi ya bude abun hannun ya saka mata ya rufe da abun rufewarsa. Ta kai dayan hannunta ta taba awarwaron da aka rubutawa sister a jiki, ta ji gabanta ya fadi wani tsumayi ya saukar mata.

“Na gode”

Domin al'adarta ce yin godiya a duk lokacin da aka yi mata wani abun alheri.

“It's my pleasure... Daga Ethiopia na zo miki da shi”

Kallonta yake kamar zai fada cikin idonta, tana jin kamar motsi a jikin kofar dakin sai ta dago da sauri ta kalleshi a razane.

“Wani zai shigo”

Tsoron kar Momy ko Namra ta shigo dakin su ganshi ya manta ita haramci da halarcin taba jiki ko hannun da ba muharraminta ba, bata san lokacin da ta kama hannunsa da sauri taja shi zuwa bandakinta ba, shi kuma ya bita kamar wani hoto, hannu biyu ta saka ta turashi ciki ta rufe bandaki, ta dawo da sauri zuciyarta na rawa ta bude kofar dakin ta leka, ganin babu kowa ya saka ta rufe kofar dakin ta dawo ta bude kofar bandakin.

“Fito babu kowa”

Ya fito kamar yadda ta bukata sai ta rufe kofar bathroom din ta kalleshi a kunyace.

“I'm sorry bana son wani ya same ka a dakin ne”

“Okay”

He said sannan ya nufi kofar fita sai kuma ta yi saurin dakatar da shi.

“Aa karka fita karka fita”

Ya juyo ya dawo ya tsaya gabanta yana kallonta, hakan sai ya kara tsanananta bugawar da zuciyarta ke yi fiye da kima, musamman da ta daga kai ta kalleshi sai idanuwansa dake kanta suka fada a cikin nata idon. Ta dan matsa baya shi kuma ya nufi gadonta ya zauna yana kallonta

“Aa karka zauna idan wani ya same ka a nan na shiga uku”

Ta fashe da kuka sai ya mike tsaye ya nufo kofar fita, sai ta kara sautin kukan da take wanda ya fi kama da shagwaba har da buga kafa a kasa, ba kuma ta yi dan shagwabar ba sai dan ta rasa yadda zata yi.

“Karka fita”

Ya juyo ya kalleta.

“Ya kike son na yi? Kin ce kar na zauna kuma yanzu kin ce kar na fita what do you want to do?”

Ta share hawayen ta nufo kofa.

“Ka tsaya a nan zan sauka falo na duba idan babu kowa sai ka sauko”

Samun kansa yayi da amsa masa.

“Okay...”

Ta nufi kofar ta bude sai kuma ta juyo ta kalleshi.

“Karka sake shigowa nan dan Allah, idan ba haka ba zaka saka ni a matsala”

A nan kam be ce mata komai ba kallonta kawai yake.

“Idan ka ji na yo tafi sai ka fito”

Nan ma be ce komai ba, ita bata jira abun da zai ce ba ta fara lekon waje tana takawa a hankali kamar wanda zata yi sata, murmushi yayi ya bi bayanta. A hankali ta fara saukowa stairs tana karewa falon kallo tana duba Dinning sai ta hango Momy da Namra zaune suna kallonta, juyawa ta yi da sauri sai ta bugu kirjin Captain dake bayanta ba tare da ta sani ba, kamar a rikice haka ta juyo da sauri ta sauko stairs din gaba daya, shi ma ya biyo bayanta ya sauko. Ta dago ta kalleshi kadan ganin hawaye ya taru a idonta ya saka shi juyawa zai taka stairs din ya koma tun da bata bashi umarnin saukowa ba ya biyo bayanta gashi kuma yanzu zata yi kuka.

“Captain....”

Momy ta kira shi sai ya juyo amman ba Momy ya kalla ba Hurriya yake kallo. Hurriya ta kalli Momy da sauri hawayena sauko mata ta ce.

“Daman dakin Yaya Namra yake nema sai ya fada dakina”

“Kamar ya Namra nake nema na fada dakinki? Sai ka ce wani kwarto ko dan'iska? Already sun san zan shiga dakinki ai, yau na dawo na kawo musu tsabarsu na tambaye ina kike aka ce kina dakinki shi ne na shiga na kai miki taki tsabar dakinki da kaina, you can't lie”

A take ta fashe masa da kuka domin dai yaja mata fitina a gurin Momy kuma yanzu ya saka ta yi karya a gabansu.

“Yaya miye haka? Ba kyau me yasa ka bari na yi karya?”

Ta nufi stairs din tana kuka sosai domin bata shiryawa tashin hankalin Momy da Yayarta Namra ba. Binta yayi da kallo yana jin kamar ya bi bayanta ya rumgume ta rarrasheta. Momy ta taso daga dinning din da take zaune ta nufo da mamaki karara a fuskarta.

“Yaya? Na dauka baka son kowa ya kira da wannan sunan?”

Ya juyo ya kalleta.

“Ita ai bata sani ba, shiyasa da ta kirani da Yaya ban hana ta ba”

“Abun da mamaki, yarinya har ta samu damar tambayarka me yasa ka bari ta yi karya? Tun yaushe wannan abun ya fara?”

“Ni ma ban sani ba Momy kawai tsintar kaina a duniyar”

Ya sauke ajiyar zuciya ya nufi cushion ya zauna.

“To ya zama na karshe daga yau, karka sake shiga sha'anin Hurriya, ba tsaraba ba ko kallonta bana son ka sake yi?”

“Saboda ita nake yawan zuwa gidan nan Momy? Me ye illar kula Hurriya?”

“Saboda ita din ba ajinka ba ce, bata kai macen da za mu bari ka so ba balle kuma har ka aura idan ma wannan abun kake tunani to ka farka tun wuri”

Da mamaki yake kallon Momy da ranta a bace har wani cika take tana kallonsa kamar wani wanda ya aikata abun kunya

“Tana da kyau ai”

“Ba daga hallita ba ne”

Ya rausayar da kai sai kuma ya sake kallonta

“Tana da tarbiya”

“Ba daga tushe ba ne”

“Tana da mutunci da kamun kai, ta san ya kama”

“Ba daga martaba ba ne”

Da kakkausar murya take amsa masa tana jin bacin rai akansa wanda bata taba ji ba.
Chapter 105 · 0% Book details