← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 159

Sashe 140

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Kisan kai fa ke nan zaka aikata Captain?”

“Ammy idan idona ya rufe bana gane me zan aikata sai bayan sun bude nake ganin abun da na aikata, kin san wannan tun ina karami kuma dan Allah ina rokon alfarmar karki sake cewa zaki alakanta ni da Salim”

Yana kaiwa nan ya nufi hanyar dakinsa. Ammy ta bishi da kallon tsoro, har lokacin jikinta rawa yake, bata tsamanin tsamanin fushin ďanta ya kai haka ba sai yau.

“Aikin soja ma be dace da kai ba, ba zan bari ka cigaba da aikin nan ba, idan ba haka ba wata rana zaka kashe wani ka bar mu da aiki”

Ta juya ta dauki wayarta ta shiga kiran Daddy. Captain ya zauna a kujerar dakin yake yana jin zafin kalaman Salim kuma yana mamakin kansa da be canja masa kamanin ba. Ya mike tsaye ya halbi kujerar da kafa, ya cige bakinsa sosai yana jin kamar ace Salim din ne a gurin. Ya nufi bandaki ya wanke fuskarsa ya fito sai ya fito daga dakin gaba daya ya shiga kitchen ya bude fridge ya dauko ruwa ya zuba ya daga cup din sama yana sha...

“Amman karka manra har yanzu ina da sauran amfani a gurinka, be kamata ka manta wannan ba”

Kalaman Salim na karshe sun dawo masa, sai yayi sauri aje cup din ya lalaba aljihunsa babu wayarsa da gudu ya fito Kitchen ya nufi wayarsa ya dauka ya kira wata number.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

“Alhamdulillah Thank you so much i trust you”

Ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya a lokaci daya. Kamin ya taba komai kiran Daddy ya shigo wayarsa ya daga kira Daddy ya rufe da fada duk yadda Captain ya so ya wanke kansa be samu haka ba a gurin Daddy domin be tsaya ya saurare shi ba.

“Amman Ammy bata fada maka abun da Salim yayi min?”

“Ko miye yayi maka be kamata ka nuna shi da bindiga ba, ran mutum ba abun wasa ba ne kuma a yadda kake tare da Salim be kamata ace kana barin Sheidan ya shiga tsakaninku ba, kana jami'in tsoro amman kake wasa da rayuwar wani wanin ma abokin aikinki, da wani mugun mutum ne zai iya amfani da wannan damar yayi against dinka, kuma idan ba zaka sauko daga wannan zuciyar ba ta ina zaka iya uba kuma mai gida? Nan gaba matarka idan ta maka laifi sai ka ce zaka yi mata, ko kuwa ba zan lamunci wannan ba, ban wahalar da mahaifiyarka ba zan yarda ďana ya auro yar mutane ya wahalar da ita ba, dan haka tun yanzu ka zubar da hallayen nan naka bana son su”

“Zan kiyaye Daddy amman baka san Salim ba ne ya... ”

“I don't care what Salim did to you, ko zaginka yayi be kamata ka yi wasa da rayuwarsa ba, be kamata ka nuna rayuwarsa bata da muhimmanci a gareshi ba, hankalin mahaifiyarka ya tashi wane irin abu ne wannan?”

“Yi hakuri Daddy”

Yadda Daddy ya kashe wayar kadai ya isa ya bayyana maka har lokacin ransa a bace yake, abun da Captain yayi kokarin aikata laifi ne babba a dokar kasa kuma laifi da zai iya sakawa a hukunta mutum ko a koreshi daga aiki ma a dokar aikin soja, idan ma ace ya aikata matsalar su zata fi shafa fiye da Captain din. Kansa ya dafa ya runtse ido ya bude shi kansa yayi nisa abun da ya aikata a gaban mahaifiyarsa a yau, be taba aikatawa wani haka ba sai Salim kuma shi ne karo na biyu, haka yake jin kamar ba zai iya rike kansa ba a duk lokacin da wata magana marar dadi ta fito daga bakin Salim zuwa kunnensa akan Hurriya. Tashi yayi ya nufi hanyar dakin da mahaifiyarsa take sai ya same ta zaune ta kifa kai da guiwa tana kuka. A take hankalinsa ya tashi daman kukan uwa shi ne tashin hankalin ko wane ďa na gari, ya duka a kusa da ita yana kallonta idonsa har sun fada tsabar tsoron da ya kama shi.

“Ammy lafiya... Kuka kuma? Me ya faru?”

Ta dago ta kalleshi hawaye na zuba a idonta.

“Zuciyarka tana ba ni tsoro ni ba zuciya ba, mahaifinka ba zuciya ba kai ban san a ina ka dauko wannan rayuwar ba, ban san me zaka aikata a gaba ba, idan babu kowa wata rana zaka iya kashe wani, zuwanka garin nan ya bata abubuwa da yawa na farinciki na Jamal, soyayyarka da yarinyar nan ya lalata akala da Hajiya Nafisa a yanzu, saboda tana ganin zan iya cilasta ko kuma na yi fadi tashin hana tarewar nan amman na gaza, Namra muka so ka aura Jamal ba Hurriya ba, idan ba zaka so ta gida ba ka nemo ta waje mai mutunci mana ba wannan ba, yanzu kokarin tarewa kake da ita, ka bata da abokinka kuma nuna shi da gun miye amfanin haka? Duk akan yarinyar nan fa”

Zaunawa yayi a gurin ya nade kafafuwansa ya duba mahaifiyarsa duba na tsanaki.

“Mutum baya aure sai matarsa Ammy ya kamata ki gane wannan, Allah ya rubuta ni da Hurriya zamu yi aure ko duk duniya za su taru ba za su iya tare wannan ba, zuwan da nake a gurin Momy ban taba zuwa saboda wata rana rana na so Hurriyya ba, haduwata da ita wani abu da Allah ya kaddara domin ban san da ita a gidan ba har sai da Mahaifiyarta ta fita, na san akwai yayan mijinta amman ban rike fuskar ko daya ba, Ammy ya kamata ki duba wani daura auren da aka yi ma bada sanina aka yi ba, amman duka Allah ya rubuta faruwarsu, farkon haduwarmu da yarinyar mari ne, na mareta da hannuna saboda ta taba ni ba ta gani ba, daga lokacin da Namra ta fada min bata iya gani sai da gilashi sai ta ba ni tausayi, ban tabbatar da ina tausayin yarinyar nan ba sai ranar da na je zan shiga dakin Momy da kunne na ji yadda take magana da Hurriya akan cewa zata musgunawa yarinyar nan kuma ba tare da ta mata komai ba, su kan hana ta abinci wani lokacin sai da taimakona take samu ta ci, kamin zuwa yanzu mahaifinta ya tsane ta aka kashe dan'uwanta ta koma bata da kowa a gidan Allah, ga mahaifiyarta ba lafiya, and now aka yi mata wannan abun yanzu a haka Ammy duk bata ba ki tausayi ba?”

“Ta ba ni, amman ai bata dace da kai ba, ina magana ne akan dacewa”

“Ta ina kike ganin bata dace da ni ba?”

“Baka ga yadda hotunan suka yadu a duniya ba? Kuma bata gani”

“Rashin gani kar ya dame ki, ina da wani yakini cewar Allah ba zai kunyata bawansa ba, da yardar Allah idon Hurriya zai bude, yada hotunanta kuma ba ita ta aikata ba aikata mata aka yi saboda a bata mata suna, kuma an yi nasara tun da gashi matar da ya kamata ace ta fi kowa kaunarta ta tsane ta, abun da zai baki mamaki ma yar'uwarta ce ta aikata mata abun Ammy, hakan ya nuna yarinyar nan tana fuskantar kalulabe na rayuwa kala kala, ke kuma kina kara taya Momy kishi ne kawai shiyasa kike tsanar Hurriya da yawa, na tabbatar da Namra ce haka ta faru da ita Momy ba zata so na guje mata ba haka ne?”

Ammy ta daga kai.

“Amman saboda Hurriya ba yarta ba ce shiyasa take fushi dake ni ma take yi da ni, a gabanki ta fadi cewar laifi ba nawa ba ne ni kadai har da Daddy, saboda tana ganin ya aura min yar kishiyarta ya bar yarta”

Captain yayi shiru na dan lokaci idonsa na cika da hawaye.
Chapter 140 · 0% Book details