← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 159

Sashe 132

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sauke wayar ya sake komawa Whatsapp dinsa yayi masa sharing din video. Ya sake kiran wani yayi requesting irin abun da ya bukata a gurin Nafi'u shi ma ya tura masa video sannan ya koma ya kwanta. Bayan kamar minti talatin ya ji an bude kofar dakin sai ya sake bude idonsa Rukkaya ta fara daga kai ta kalli sake kallon kofar dakin domin ta tabbatar nan din ne sannan ta kasara turo kofar dakin tana sallama.

“Sallamu Alaikum”

Be amsa mata ba domin be san ta ba, be kuma san manufar shigowarta ba har sai da Hurriya ta bayyana a bayanta.

“Oh My god”

Ya tashi zaune da sauri farinciki ya cika fuskarsa, hannu ya saka ya kashe ruwan ya cire a hannunsa  ya rufe gurin da jinin zai iya biyowa sannan ya mike tsaye ya gyara rigarsa kamar ance masa Hurriya tana ganinsa. A tsakiyar dakin Rukkayya ta ja ta tsaya tana kallonsa.

“Direban Appan Hurriya ne ya ce mana nan zamu shigo, dan Allah ko kai ne Jamal?”

“Yes... Angon Hurriya”

Ya fada yana nufar Hurriyar dake bayanta tana rike da hannun Rukaiyah. Hannunsa ya kai ya kama dantsen hannunta ya rikata yana kokarin fitowa da ita bayan Rukayya.

“Assalamu Alaikum”

Hurriya ta fada tana jin tsoron da wani yanayi na dabam, domin wani be taba kaiwa a jikinta haka ba a take jikinta ya fara rawa. Murmushi Captain yayi Rukaiya ma ta yi murmushi tana mamakin a yadda ta samu Captain domin dukansu ba su saka ran namiji ne mai kyau da tsari da cikar kalama ne ba irin Captain.

“Ban san ya kike da Hurriya ba, dan Allah ce ta sake hannunki ko kuma ke ki sake hannunta”

Ya bukaci haka ne saboda Hurriya ta ki yarda ta saki hannu Mama Rukaiya.

“Ni kanwar Mahaifiyarta ce”

“Oh Ashe mamanmu ce, sorry ban amsa sallamarki ba, a yafe min Momy”

Rakayya ta yi murmushi ta saki hannun Hurriya, Captain ya mika hannunsa ya rika hannun da Rukkaya ta saki ya jata har gurin gadonsa ya zaunar da ita. Sannan ya nunawa Rukkayya kujera.

“Bismillah”

Ta karasa ta zauna tana masa ya jiki.

“Alhamdulillah, ko da aka daura auren ba ni da lafiya shi ya hana ni fita ko'ina balle na je na gaisa da ku mu san juna”

“Idan ka samu lafiya ai sai ka yi Allah ya kara afuwa”

“Amin thank you”

Ya zauna kusa da Hurriya yana kallonta. Baya bukatar tambaya ya san wannan duk shirin mahaifinsa ne, dan haka ya dauki wayarsa yayi ma mahaifinsa text.

“Thank You, you're the best Dad in the whole world”

Ya aje wayar a gefensa ya maida hannunsa a gurin Hurriya dake matsawa a hankali domin tana jinsa daf da ita.

“Ya jikin?”

A madadin ya amsa mata sai ya kalli dan space din dake tsakaninsu yayi murmushi, wani kalar nishadi da farinciki ne zuciyarsa na ganin matarsa labarin zuciyaa tambayi fuska in ji hausawa, sai yake jin ya warke daga fever ma. Rukayya ta mike tsaye tana rike da wayarta.

“Bari na jira a waje”

“Dama dai kin wuce gida zai fi, domin Hurriya ba yanzu zata koma ba sai dare”

“Gwaggo bata ce na barta ba, cewa aka yi mu zo mu dubaka mu koma, direban ma yana waje”

“Wacecw Gwaggo?”

“Kakar Hurriya mahaifiyata”

Captain ya dariya.

“Ashe ma kaka ce, idan kin koma ki fada mata mijinta ya riketa, daman ya fi Kaka iko da ita”

“Zata min fada”

“Fada kadai zata miki ashe, Wallahi Hurriya ba zata koma yanzu ba, akwai maganar da zan yi da ita so ki tafi kawai karamar uwa madaukar zunubi”

Babu yadda Rukayya ta iya bayan yi masa fatan samun lafiya ta fice daga dakin Hurriya na ji kamar ya ce mata kar ki tafi. Captain ya matsa kusa da Hurriya jikinsa na taba nasa daman ficewar Rykayya kawai yake jira.

“Ni kike gudu?”

Ta yi shiru tana jin kunya na rufe ta, sai ta ji dakin yayi mata girma daga ita sai shi daman tana jin alamar kamar su kadai ne a ciki. Ya saka hannayensa biyu ya zafaye ta ya dora wuyansa a kafadarsa.

“Fada min ya kike?”

“Lafiya kalau”

Ta amsa da sauri, tana kin bashi hadin kan tsuma yatsunsa a cikin nata. Ya sumbanci kuncinta ya kalli gefen fuskarta yana kai dayan hannunsa ya taba Lips dinta

“Ki yi hakuri na mari dukiyata na fasa bakin nan da kaina, ban jidadi ba I'm sorry”

“Ba komai ya wuce”

Ta mike tsaye tana jin wani iri, ya sauke kansa kasa yana murmushi kamin ya mike tsaye ya koma gabanta ya tsaya ya dafa kafadarta.

“Alhamdulillah komai ya wuce a yanzu ko?”

“Ya wuce a cikin gida, amman yana nan a duniya za'ayi ta kallona da abun ko da na bar duniya”

Ya kura mata ido kamar mai kokarin kure kallonsa. A hankali ya zaunar da ita ya zauna gefenta ya saka hannunsa a cikin nata ya kwantar da kanta a jikinsa.

“Abu mai muhimmanci a yanzu, mahaifinki be yarda kin aikata mahaifiyarki ma haka, Ubangijinki ma ya san baki aikata ba, mijinki ma haka duk wanda zai zargeki a bayansu ba shi da amfani”

“Kai ma ka yarda ban aikata ba?”

Yayi dariya marar sauti ya dagota daga jikinsa ya fuskance yana kallon kyakkyawar fuskarta.

“Na yarda amman ban tabbatar ba”

“Zan iya rantse maka da kur'ane kamar yadda na yi ma Appa”

“Ban karyata ki ba ai, zan tabbatar da kaina, na gaba kadan”

“Yaushe? Me yasa ba saka tabbatar a yanzu ba?”

“Kin matsu ne?”

Ta daga mishi kai a bakin gaskiyarta, sai ya saki hannunsa ya mike tsaye yana murmushi domin ya fahimcin bata gane dawon garin ba. Kofar dakin ya nufa ya bude ya leka hagu da dama sannan ya dawo ya tsuguna a gabanta hananyensa a cinyarta yana kallon fuskarta a dora, sai fara kokarin mikewa tsaye tana ture hannayensa.

“Babu wanda zai ce wani abu a nan, ni mijinki ne, halak malak, ni zan bawa duniya shaidarki daga yanzu har karshen rayuwarki”

Ya kama yatsansa yana murzawa a hankali.

“Mai tsada na yi yadda zan iya na ga mutunci ya karu a idon duniya, na iya kokarina na saka an goge hotunan wadanda suka wallafa hoton sun goge, sai dai wadanda ban sani ba”

Ya sumbanci hannayenta duka biyu ya saka su a fuskarsa.

“I will fix what they broken, zan zama zama hasken da zai haska duhun dake rayuwarki, zan yaye miki damuwarki, zan saka ki yi alhari da ni a matsayin miji, da ace zan iya sauya lokaci na koma baya da na rayu da ke tun kurciya har tsufa, saboda ina bukatarki a rayuwata, i will spend every hour of the day keeping you safe Hurriya, na miki wannan alkawarin Hurriya, zan baki wata duniya mai cike farinciki, duniyar da babu kuka babu damuwa babu tashin hankali babu tsana babu kiyayya....” 

Hawaye ke sauko mata jikinta yayi sanyi, ba a taba siyeta da kalamai masu dadin irin na yau ba, wani be taba yi mata kalam kwantar da hankali kuma ta ji hankalinta ya kwanta ta samu natsuwa irin yau ba.

“Is Okay is alright....”

Ya mike tsaye ya zauna kusa da ita ya share mata hawayenta.

“Ban taba fada miki wannan ba Hurriya, bari na fada miki yau.... I LOVE YOU... INA KAUNARKI HURRIYA fiye da duk wani namiji da ya nuna miki soyayya a duniyar nan”

Wasu hawayen ne suka sake zubo mata, sai ya kai bakinsa ya sumbanci hawayen nata ya hade goshinsa da nata yana goga mata hancinsa, numfashinsa da nata yana tarayya.

“Ina jin wannan din ma kamar mafarki ne”

Ta fada cikin sautin kuka, sai ya dora bakinsa akan nata ya rufe ido.

“Gaskiya ne... Zahiri ne wannan Hurriya... Lokacin da Daddy yace min mai tsada ta zama taka sai na ji kamar ba a taba bani farinciki irin na ranar ba, saboda ke ce Hurriya”

Yana maganar lips dinsa na taba nata, kamin ya bude idonsa yana kallon nata idon dake rufe. Sannan ya sumbanci banki ya sumbanci hancin ya mike tsaye ya dauko wayarsa ya dawo kusa da ita ya zauna.

“I have another surprise for you”

Ya kunna mata video sanin bata iya gani sai ya kara mata muryar a kunne. Kamin ta gama saurare hawaye ya jika gaban hijabinta, sai ta kasa jin farinciki kuma ta kasa jin bakinciki ta tsaya a tsakiya tana jin ba gaskiya ba ne.

“Taya yar'uwa ta jini da uba mai daraja ya hada su, zata aikatawa yar'uwarta wannan abun? Ko dai sheri yake mata? Na san Yaya Khairy bata shiri da ni amman wannan yayi muni, mai kiyayya da ta yi zurfi da kai ne kawai zai iya aikata wannan! Idan ma bata raga dan ni ba ai ta rangwanta ko dan mutuncin gidanku, a karkashin inuwa daya muke da ita wannan abun ya taba mutuncin kowa a gidan bata gane ba? Na ma kasa yarda ita ce ta aikata haka”

Captain ya rumgume ta, domin kukanta a yanzu yana daga masa hankali.

“Zamu kara tabbatar da hakan nan gaba kadan, gaskiya zata kara bayyana”

Hurriya ya rushe da kuka a kirjin mijinta ta kamkame shi.

“Na tuna... Na tuna ranar da ta fita da ni... Ranar da tace na raka ta gidan kawayenta, Yaya Khairy ta cuce ni yar'uwa ta cutar da yar'uwarta ta jini, me na mata amman me na mata”

Captain ya dagota jikinsa da sauri ya rike fuskarta da hananyensa.

“I know this not easy, baki mata komai ba Hurriya, makiyinka baya bukatar ka yi masa laifi sannan ya hukuntaka baki mata komai ba”

Ta saka hannu ta rufe bakinta tana girgiza kai, yayi mata nauyi yyi mata muni ace yar'uwarta ce ta aikata haka. Ya sake rungume.

“Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii wannan ya wuce yanzu, ita ya kamata ta yi kuka ba ke ba”

Be dagota daga jikinsa ba sai da ya tabbatar ta daina kukan. Sannan ya dagota daga kirjinsa ya kalleta.

“Kin rame wannan abun ya saka miki damuwa sosai, yaushe rabon da ki ci abinci”

Ta kasa yin magana. Ya shafa fuskarta.

“Kina bukatar cin wani abu?”

Ta girgiza kai.

“Kwanta a nan ki huta”
Chapter 132 · 0% Book details