Sashe 130
Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Babu wanda ya sanar min da cewar za'a daura, mahaifinsa ya shigo gida ne kamar haka ya sanar mana sun je jaje kuma yin nemi aurenta an ba su har an daura, yarinyar da bata gani ma amman idonsa ya rufe ya rantsa sai ya zauna da ita”
Salim ya sauke ajiyar zuciya ya saka hannayensa aljihu.
“Yarinyar nan bata cancanci Captain ba ko kadan ko da kuwa bata aikata ba, ya kamata ya lura da yadda duniya take kallonta a yanzu, amman kin san Captain ba a masa daidai, kawai dai mu saka masa ido zai fi”
“Kai ma dai ba zaka iya ba kenan...! Babu wanda yake iya fahimtata”
Ta cige baki tana kallon wani ward din dake facing dinsu, Salim ma gurin yake kallo sai dai kowa da kalar tunaninsa. After Salim ya fice Captain ya tashi zaune
“Ina fatan dai ba wata matsala ta ja rashin lafiyarka ba?”
“Aa rashin lafiya ne kawai babu wata matsala Daddy”
“Ma Sha Allah, daman ina da niyar kira na maka albishir sai kuma Ammynka ta sanar da ni ciwonka a take tawun giwa ya take na rakumi”
“Akan Adam ne?”
“Ka ga video ne?”
“Aa zan sauke kenan ka kira ni, amman Salim ya fada min Adam din ya aikata abun da ake bukarta ya aikata”
“Ya aikata yayi kamar yadda muke bukata, mahaifinsa ya turo min da video, domin ya kara kira bayan ya tafi gurin mahaifin yarinyar be yi nasara saboda na yi waya da shi na fada masa duk irin magiyar da za su masa kar ya aminta da su, sai kuma ya dawo ni ma yana rokona sai dai ban bashi wata amsa ba bayan wanda ka bashi, kuma na tabbatar masa a jibi Monday za a shiga kotu, sai gashi yau ya turo min da video”
“Na jidadin hakan Daddy thank you very much, da goyon bayanka ne na samu wannan nasarar, zan yada video, na san hakan zai wanke yarinyar nan ko da ba gaba daya ba, zata yi farinciki idan ta ji i wish ni zan fada sanar mata ma saboda na mata wannan alkawarin”
Daddy yayi murmushi.
“Yaron ma abun tausayi, kaddarori ne kawai da rashin tunani irin na yaran yanzu, jiya ma na yi waya da Hajiya nake tambayarta zuwa yaushe ne ya kamata ace Hurriya ta tare saboda damuwa a yanzu matsalar idonta ne, ina son ta dawo karkashin ikonmu ne gaba daya sai a nema mata maganin hakan zai fi armashi da ace tana gidansu za'a nema, sai dai Hajiya tace min mu daga kafa zuwa nan da kwana biyu zata tafi ita da Hajiyar Maru sai su yi maganar tarewar domin abun ne da ya danganci mata, kuma na bata sako ta fadawa iyayenta mu dai yarinya muka aura ita muke so, ba dan mun raina arzikin ubanta ba, amman ba ma bukatar komai daga garesu zamu zuba komai daga nan garin da zata zauna har zuwa inda aiki zai kaika”
“You're best Dad ever samun irinka Daddy sai an tona, Hurriya ta yi sa'ar samunka a matsayin suruki”
“Akan kawo mana neman taimakon auren wasu ma mu yi balle kuma naka? Jamal ba dan kana son yarinyar nan ba no a kashin kaina yarinyar ta ba ni tausayi na halin rayuwar data samu kanta, ina tunanin idan da ace yata ce ya zan ji, yarinya karama an bata mata rayuwa da suna akan abun da bata aikata ba”
“Akwai matukar tausayi Daddy, amman Ammy ta kasa gane haka”
“Zata gane Son.. Zata gane.. Matsalar da aka samu Ammynka mace ce mai matukar son riya da alfahari ba irin wannan auren take son ayi ba, kuma su mata suna da wannan dabi'ar da rike abu balle kuma bata son yarinyar, dole sai ka yi hakuri with time zata fahimceka..”
“Ina fatan haka”
“Bari na barka ka huta, zan aikawa mahaifinta da video yanzu, na san ba zai masa dadin kallo ba, amman ya kamata ya san gaskiya kuma ya san matakin da zai dauka ko dan nan gaba, amman da zaka hakura da yadawar wata kila zai fi, ya zai ji idan aka ce yarsa ce ta aikatawa yarsa haka?”
“Daddy idan video be fita ba taya za a wanke Hurriya? Cikin alkawarin da na yi mata na fada mata cewar sai na yada wanda yayi mata wannan abun fiye da yadda aka yada hotunanta”
“All the best... Get well soon”
“Thank you Daddy”
Ya fita daga video call din ya sauke video da Salim ya turo masa yana kalla, a take ya ji kamar an yaye masa ciwon dake damunsa saboda farincikin yadda Adam ya bada labarin komai a video kamar yadda ya fadawa Captain da iyayensa banbancin wacan video da wannan, wannan video shi ya dora shi da kansa a shafinsa na tiktok kuma yana sanye da tufafi na kamala har da hula kamar mutumen arziki. Bayan ya gama kallo ya jira Ammy a wayar sai ta amsa tana shigo dakin domin tana daf da kofar dakin ne a lokacin da ya kira wayarta.
“Lafiya? Allah yasa ba jikin ba ne”
Ta karaso gurinsa da sauri. Captain dake jin kamar yau ce ranar angoncinsa ya mikawa Ammy wayar yana dariya.
“Ba shi ba ne, duba wannan ki gani”
Ta karbi wayar ta kunna video ta kalla, sai ta tabe baki ta zauna.
“Still dai ba zai goge hoton tsiraicin Hurriya da yake idanuwan mutane ba, kuma hakan ba zai hana ace kasan yarinyar nan da aka yada hotunan ta da wani saurayi ba? To Captain take auren yaron Engr A A Turaki ba”
Far'ar dake fuskar Captain sai ta soma disashewa, doman yayi tunanin hakan zai cire wani abu daga tsanar da Ammy take ma Hurriya.
“Tun farko kina kiyayya da ita ne saboda kina taya Momy kishi ne kawai saboda tana yar mijinta kuma Momy bata son Hurriya, Namra ma bata sonta, da kunnena na ji komai Ammy, kiyayyar da kike yi ma Hurriya ba na abun da ya faru ba ne kawai idan saboda shi ne ai kaddara ce da bata wuce kan kowa ba”
“Haka ne, shiyasa mahaifinka zai yi mata komai ai, da yar wani mai arzikin ka aura kamar mahaifinka, ai ba zai yarda da wannan ba”
“Shi ma ai be riga ya yarda ba, domin ba a taya masa ba kuma babu tabbacin zai amsa ko akasin haka shi ma yana son yarsa...”
Ya koma ya kwanta ya rufe idonsa...
*** *** ***
Cike da girmamawa Appa ya amsar wayar sukirinsa ta bangaren biyu, suka gaisa cikin mutunci da far'a Daddy ya tambaye shi rayuwa da kuma kasuwa suka ya amsa masa da hamdallar Allah.
“Daman na kira ne akan maganar Hurriya...”
Daddy ya dan yi shiru.
“Akan maganar tarewarta ne?”
“Eh to...ba makasudin kenan ba, amman saboda ka fadi hakan bari na ce har da shi da na bar mata su yi wannan aikin ne”
Appa yayi murmushi.
“Daman ina da niyar na yi maka magana akan hakan, saboda ina neman Alfarmar ka daga mana kafa har zuwa ta samu lafiya, yanzu haka na fara shirye shiryen abun da ya dace ayi ne akan idonta, abun ba zai yi kyau ba amarya da makanta...”
Daddy yayi hanzarin tariyar numfashinsa.
“Ka kawar da wannan maganar, yanzu neman lafiyarta da cinta da shanta a abu ne da ya rataya a wuyan mijinta, kusan shi ne makasudin da ya saka nake son ta tare ai, saboda ya zama tana hannunmu mu zamu yi mata komai, ba lafiyarta kadai ba Alhaji Haruna har wata hidima da zaka yi akan Hurriya tun daga kayan daki har koma mun dauke maka”
“Aa aa aa sam ba zan karbi wannan ba, na san kan yi kokari amman wannan bangaren kan a bar min shi, yarinyar tana daya daga cikin yaran da nake alfahari da su, kuma idan ban sakawa Hurriya na yi mata hidima mai kyau ba da me zan saka mata? Ni zan yi ma yata komai idan ka yi min haka ai kamar ka raina nawa arzikin ne ko kuma na ganin zan gaza ni kuwa zan baka mamaki”
Daddy ya ce.
“Ba wannan ba ne duka na so na yi hakan ne saboda kyautatawa, amman ba zan hana ka Allah yasa hakan ne mafi alheri”
“Ameen na gode sosai Allah ya bar zumunci”
“Ameen Ameen. Akwai video da zan aje maka a whatsapp yanzu, video ne da Adam yayi yake ba da hakuri na abun da yayi kuma yake fadar gaskiyar abin da ya faru, wanke Hurriya sosai a video”
“Maa Shaa Allahu Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah na gode maka Alhamdulillah”
Appa yana ta maimaitawa cikin farinciki.
“Sai dai bana son Hurriya ta ji a yanzu, kuma ina rokon Alfarmar ka kai Hurriya a asibiti yanzu ta duba mijinta ba shi da lafiya yana can kwance an saka masa drip”
“Subhanallahi, me yake damunsa”
“Ba wani serious ciwo ba ne fever ce kawai”
“Toh ranka ya dade zan yi hakan, kuma ni ma zan je na duba shi anjima”
“Na gode”
Daddy ya yanke jiran, Appa kuma ya shiga whatsapp dinsa ya kama number Daddy yana ta jiran sakonsa. Dilll sakon ya fado a wayar video ya fara bude kansa, daga kasan video kuma address din asibitin da Captain yake ne.
Natsuwa sosai Appa yayi yana kallon yadda Adam ya fara bada hakuri da neman yafiyar Hurriya hannunsa da dauri, kana ganinsa ka san baya cikin farinciki kuma ya sha wahala domin jikinsa ya nuna haka, daga bisani ya koro da bayanin yadda abubuwan suka faru. Appa na zaune a office dinsa sai gashi a tsaye yana kallon video cikin firgici da mamaki yana jin duniyar gaba daya kamar mafarki.
“Khairy... Umm Khairi... Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”
Ya koma ya zauna, yana ta neman daukin Allah ta hanyar ambatonsa kamin ya sake mikewa tsaye ya maida video baya ya kalla, ya sake kalla ya sake kalla.
“La'ilaha Illallahu... ”