← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 159

Sashe 28

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hurriya ta yi dariya mai sauti ta shiga Kitchen ta dauko tray ta dora ruwa da lemu a kai sannan ta fito ta dauki plate din abincin ta dora a tray ta dauka ta fice da sauri. A harabar Apartment din Hajiya Kaltume ta dawo ta zauna a balcony kusa da Hamad ta aje tray.

“Hamad zo mu ci abinci”

Ya kalli abinci sai ya bata rai.

“Waya ce ki hade? Waye zai ci abinci da ke to?”

“To ai ni ina sauri ne, Yaya Namra ta ce Momy nemana take zata min fada saboda ban karbi abun da bakonta ya ba ni ba”

“Toh ina ruwana ki je ki zuba wani”

Ya saka hannu ya dauke abincin da ba zai iya cinyewa shi kadai ba ta dora a cinyarsa.

“Idan ba zaka ci da ni ba, ba sai ka je ka debo na ka ba?”

“Ba zan ce ba, ni ki daina ba ni umarni”

“Wannan dai nawa ne ka ba ni abinci na Hamad”

Yayi mata kunne ne shege yana ta cin abinci ko kallonta be yi ba. Har ta tashi zata tafi debar wani sai kuma wata zuciyar tace mata Momy na nan falo, sai ta koma ta zauna ta dauki lemun ta sha tana ta kallonsa yana cin abinci. Ita ma dai kamar mantawa ta yi Hamad be cin abinci da kowa kuma be cin ragin kowa har da na Appansa da na Amma. Hakura ta yi ta saka masa ido ta can kuma ta ji ba zata iya ba tunawa da ta yi baya son gashi idan yana cin abinci sai ta cigaba da sifar kan tana kallonsa wai ko zai ji kyama ya aje abinci. Instead of yayi haka sai ya kifar da plate din ya riko gashin kan nata a daidai lokacin da Mota ta faka harabar Hajiya Kaltume. Da wani irin karfi yake fisgar gashi da karfi bata san lokacin da ta fara ihu tana rike hannunsa ba. Da sauri Fadeel ya bude motar be ko tsaya kashewa ba ya fito ya nufi inda suke daker ya banbanre hannun Hamad Hurriya ta koma bayansa da sauri tana kuka.

“Kai wannan ai sai ka tsinke mata gashin ka rage mata sadaki, miya hada ku?”

Hurriya bata iya magana saboda kuka, Hamad kuma ba gwanin maida magana ba ne daman sai cika yake kamar wani zaki. Hajiya Kaltume tana kawowa kusa da su ta ce

“Ai haka suke, uwa daya uba daya amman baya raga mata, basa zaman lafiya kamar Annabi da Kahiri suke”

Cikin mamaki Fadeel ya kalli Hamad.

“Wai kanwarsa ce yake mata wannan jan gashi haka?”

“Ita ce yayar ai, dan ka ganshi da girma shi ne kanen ai, baya ragawa kowa a gidan”

Hamad ya juyo yana watsawa hara Hajiya Kaltume dake korawa Fadeel bayani saboda ta tabo shi tun da ta ce be ragama kowa.

“Idan ba kai ba, wake fada da mata? Ba yayarka ba ce?”

Ya juyo ya kalli Hurriya da ta boya bayansa.

“Ke kuma ki rika kiyaye, yi hakuri ki daina zama babu dankwali ba kyau”

“Ai Allah yasa ma aljannu da ifiritai da shaidan duk su tattara su shige a cikin kan nata, ita ma ai ba karamar marar jin magana ba ce”

Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume dake fadar haka tare da yin gaba da bar su a gurin. Ta share hawayenta ta kalli Hamad sannan ta kalli Fadeel.

“Ina wuni”

Dariya yayi.

“Lafiya Kalau, Allah ya tsare gaba Hurera ko?”

“Hurriya”

Ta gyara masa.

“Yeah ki rufe kanki”

“Toh”

Ya juya ta sauka balcony din ya nufi motarsa dake kunne har lokacin sai da ya shiga motar daga mata hannu sai kallonta yake sannan yayi reverse ya fice.

Two Week Later....

Hajiya Fatee ta gyara zama ta kalli kawarta kamin ta kalli Malamin da suka sauka a garage din gidan.

“To yanzu Malam akwai yadda za'ayi a danne cikin nan kar ya bayyana? Kuma wannan tofe tofen yawun da kin cin abinci da nake ga kasala duk na daina shi?”

Malamin dake sanye da babbar riga ya kalli Hajiya Fatee yana murmushi.

“Za'a iya sosai kowa, ba yau na saba ba, za a iya danne cikin nan har tsawon shekarun da kike so”

“Alhamdulillah, ina son a danne min shi har nan da shekara dari, na san dai ba zan yi shekara dari a duniya ba”

“Ko kuma nan da lokacin da zaki yi aure ba, Hajiya yadda kike da surar nan Maa Shaa Allah, ai sai idan mutum be samu dama ba, shekarunki ba ba za a ce kin yi ba, ai na san ba za a rasa namema ba ko?”

Maganar yake yana dariya kamar wata abokiyar wasarsa.

“Aa kai aure kuma? Wake ta aure yanzu? Aa mun bar wa yara, ni dai yanzu bukatata a fara danne cikinki, idan an samu nasara hakan yayi sai a shiga yi Farraqu tsakanin yaron nan Fadeel da Matarsa Afrah domin ina kwana da bakincikinta a kullum Wallahi”

.“Babu Matsala Hajiya, za a danne ciki, matukar ba a daga dutsen da zamu saka layar mu rufe ba, cikin nan ba zai taba tashi ba har abada, amman fa zaki zuba kudi kam”

“Karka damu zan biya ka ko nawa ne, ammam dan Allah a saka dutsen a inda ba za a iya dagawa ba”

“Aljannu za mu saka su yi aikin, karki damu”

Hajiya Fatee ta kalli Kaltume suka yi murmushin jindadi sannan Hajiya Kaltume ta kora da nata bayanin.

“To ni Malam na ji shiru, kasan na baka kudi akan za ayi ma Iyami aiki ina son komai nata ya lalace amman har yanzu ba labari, kuma ni yanzu so nake a mallake min kowa a gidan nan daga mijina har Nafisa ikon kowa ya dawo karkashina, ina son Alhaji ya zama be iya aiwatar da komai sai abun da na fada masa, kuma ina son a shiga tsakaninsa da yaran nan, ya maida su banza a cire masa su a rai, ya ji baya bukatar ganinsu ma, domin na ji yana zancen fitar da su waje karatu, kuma ko be fitar da su ba, ita wannan da take da kokari na san gwanati ko wasu za su iya kaita waje karatu, so nake a lalata karatun nata, kai ni duk wani abu da zai saka Iyami farinciki bana sonshi a toshe komai Malam”

“Hajiya, aiki ai mun aiwatar jefa muka mata kuma yana nan yana tafiya kin san jifa wani lokacin tana dauka lokaci kamin ta isa, amman kuma da zarar ta isa zaki sha mamaki ba dan karami ba, sai kin tabbatar da ba ki min biyan banza ba, mijinki kuma zaki mallake shi a hannu, sai dai wannan Nafisa kishiyar taki fitinanniyar mace ce akwai yan ƙwanƙwanmai a kanta, kin san mai yawan masifa da mai addu'a asiri be cika saurin kama su ba, amman zamu gwada”

“A gwada Malam zan biya ko nawa ne karka ji haufi”

Malam ya san washe baki. “To Mallada ai mu haka muke so”

Hajiya Fatee ta ce.

“Toh ni Malam ya za'ayi na gane idan cikin ya dannu?”

“Idan na yi aiki, zaki ji motsi sosai a cikinki idan motsin be daina ba har safe, to cikin ne dannu ba wata kila sai mun sake yi, idan kuma kin ji motsin kadan to aiki yayi kuma zaki daina duk wasu dabi'u da kike na masu ciki, cikin kwana biyu”

“Alhamdulillah, ni da zaka cire cikin ma ni ka dauki cikin na bar maka, ko ina da aure me zan yi da mugun iri? Balle kuma an kwana biyu har na kai ga jikoki”

“Komai zai wuce Hajiya karki samu damuwa”

A ranar da farinciki Hajiya Kaltume ta dawo gida, saboda ta samu fadawa bokanta abun da take so kuma ya tabbatar mata da zai iya. Wani karin abun farincikin ma sai da babbar yarta Mace mai bin Yasir wato Umm Kaltoon da ake ma inkiya da Maamata saboda sunan Hajiya Kaltume mata albishir da mai cewar mai son ta zai zo ya gaishe da Hajiya da Appanta sai Hajiya ta rasa ina zata saka kanta dan dadi, daga ita har Hajiya Fatee sun kwana da farinciki a daren kowa da bukatarsa da kuma burinsa, Hajiya Fatee bata da burin da ya wuce a danne cikin nan kuma a raba Fadeel da matarsa Afrah saboda ta tsokane mata ido.

Washe gari...

A tare da Hamad Hurriya ta fito bangaren Momy da far'arta tana hira da Hamad, kai ka rantse ba sa fada da juna labari take ba shi na wata class mate dinta da ya sani sai dariya yake. Sai da suka fara zuwa gurin Appa suka karbi na na su lemun da Chocolate Hurriya ta masa godiya, sannan suka nufi box din dake kai su makaranta suka shiga. A makarantar ma sai suka wuni kamar ba su ba, daman tare suke breakfast amman kowa da abincinsa dabam, a ranar duk abun da Hamad ya siya sai ya iskota har cikin ajinsu ya bata, kasancewar ajin maza dabam na mata dabam. Misalin karfe daya da rabi suka tashi suka tafi Masallaci suka yi sallah sannan suka tsaya jiran direbansu dake zuwa karfe biyu daukarsu gaba dayansu yan gidan. Biyu da mintuna ya iso suka shiga box Hurriya tana can baya Hamad kuma yana a inda ya saba zama, wato front seat babu mai zama a gurin sai shi kuma baya zama da kowa sai shi kadai. Kilometers kadan ne tsakaninsu da Family house dinsu wata bakar motar ta shiga gabansu ta tara musu har sai da direbansu ya tsaya gashi gurin babu mota ni motoci ma ba kasafai fa, shi ma direban yana biyo hanyar ne saboda ta fi saurin kawo su gida.

“Malam baka gani ne?”

Ya fada cikin tsawa ganin yadda yake masa ganganci kamar ba akan titi suke ba. Bude motar aka yi wasu maza hudu suka fito fuskarsu a rufe biyu daga cikinsu na rike da bindiga suka bude ma direban da tuni ya fara salati ya fito Hamad ma ya bude ya fito jikinsa na rawa suka sa ya zagayo gurin direban sannan suka bude gambun bus din.

“Kowa ya fito”

Kowa ya fito cikinsu na rawa suna ihu.

“Ku yi shiru ko na halbe mutum yanzu”
Chapter 28 · 0% Book details