← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 159

Sashe 72

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya ta mike tsaye har lokacin dariya take, sai da ta shiga ta aje wayar ta sako hijabinta sannan ta fito tana gyara talkamin kafarta.

“Mu tafi yar gidan Gwaggo, ke ko kishinki bata yi sai fada take min ban raka kishiyarta ba”

“To idan ma ba yar wuta ba, wace kishiyar ce zata yi kishi da Hurriya baiwar Allah, kifi musulmin nama”

Hurriya ta yi dariya, ita kanta Gwaggo dake maganar dariyar ta yi, kamin ta raka da addu'a, Amma kuma ta bita da kallo tana dan murmushi kadan. Tare suka isa da Rukayya har titi suna tafe suna hira, Rukayya sai tambayarta take wai halin Hajiya Kaltume na nan ko ta daina.

“Me zata daina kuwa Mama Rukayya ni dai arzikina, daya bana gidan yanzu duk wani abun da zata fada ko ta yi ba zai shafe ni ba”

“Wallahi kin huta, ai kara da Hajiya Binta ta dauke ki, kika rabu da wannan bakar kalwal mai bakar zuciya”

Hurriya ta kalleta tana murmushi.

“Amman dai Mama Rukayya wasa kike so? Hajiya fa mahaifiyar Yaya Yasir ce”

“And so what? Ke baki ga yadda ta maida Amma ba? Ta mallake Appanku baya jin maganar kowa sai nata? Ni fa da zan samu sa'arta sai na dauko fansar duk abun da ta yi mana, saboda tana tsaye nan a makoshi?”

“Toh kuma ki yi Yaya da Yaya Yasir?”

“Wai ke ina ruwanki da Yasir din ne? Ke fa wata rana kamar munafuka haka kike”

Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba.

“Mama Rukayya ke dai yi a hankali, dan kin san Yayana fa, shi yake zane mu idan muka yi laifi”

“To ni sai ya dake ni? Ke yarinya kama kanki, ai ko kirana yayi ban daga ba sai kin ga yadda hankalinsa yake tashi, idan kuma ya zo ya karbi wayata ko ya gan ni da wani ya fara kishi kenan, ni Rukayya i no dey carry last, haba ni ba halin Amma ne da ni ba, kowa ya ce min kule chasss zan ce masa”

A karo na barkatai Hurriya ta yi murmushi, ta tsayar da mai napep ta shiga bayan ta fada masa unguwar da zai kaita.

“Toh Allah ya tsare, damo sarkin hakuri”

“Amin Mama Rukayya na gode”

Mai napep yaja suka dauki hanya. A bakin gate ya sauke ta ta ba shi kudinsa sannan ta shiga cikin gidan, tana yin arba da daya daga cikin motocin da mahaifinta ya fi yawan hawa gabanta ya yanke ya fadi, tun a nan ta fara rage tafiyarta, hakalimlnta be tashin ba sai da ta kunna kai cikin falon ta yi arba da Hajiya Kaltume da Appanta, Hajiya Binta kuma tana zaune saman kujera.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

𝐊𝐇𝐀𝐃𝐄𝐄𝐉𝐀 𝐂𝐀𝐍𝐃𝐘

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

𝐏𝐚𝐠𝐞 2⃣2⃣

“Hurriya an dawo”

Far'ar da Hurriya ta gani a fuskar Hajiya Kaltume lokacin da take fadar haka ya fi daga mata hankali fiye da ganinsu da ta yi a gidan. Cikin rashin kuzari da faduwar gaba ta karasa kusa da Hajiya Binta ta zauna a kasa, sannan ta mikawa Appa gaisuwa.

“Lafiya Kalau”

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Kaltume na murmushi tana kallon Hurriya irin murmushi na murnar ganinta, bayan kuma a kasan zuciyarta ba haka ba ne.

“Hajiya Ina wuni?”

“Lafiya Kalau mutan aljanna, an dawo? Tun dazun muke nan ai, Hajiya ta ce kin tafi duba Iyami ya jikin nata”

“Tana jin sauki?”

“Sosai?”

“Eh”

“Maa Shaa Allah...”

Ta kasa cewa Allah ya bata lafiya, saboda hausawa suna cewa addu'ar fatan alheri ta makiyi karbabbiya ce, wai idan yayi maka sai an karba. Hurriya ta juya a hankali ta kalli Hajiya Binta dake zaune fuska ba yabo ba fallasa.

“Hurriya an dawo?”

“Eh Hajiya sannu da gida”

“Sannu dai yar Albarka, kin yi Sallah?”

“Aa ina tahowa ne aka yi kira”

“To tashi ki shiga ciki ki yi Sallah ki”

Hajiya Kaltume ta ce

“Ai da ta bari sai mun tafi sai ta yi sallah a can”

“Babu inda Hurriya zata tafi, ai na fada miki tun da ya koreta ta dawo nan kenan idan kika ga ta bar gidan nan to bana raye ne”

A take Hajiya Kaltume ta saka kukan munafurci.

“Haba Hajiya yanzu duk hakurin da muka yi ta baki baki hakura ba, ita dai Hurriya na san bata da matsalar komai kuma ko yanzu zata so komawa gidan ubanta domin babu kamar gidan uba a duniyar nan”

“Nan da take ai daji ne, da bata da alaka da kowa, ke ni kar nake ganinki, halinki babu wanda ban sani ba Kaltume, tun kina da kurciyarki har yanzu da kika yi yaya, saboda na aika muku da shi ne kika taso mijinki gaba kuka ta so wai azo a kalailaye ni da dadin baki a tafi da Hurriya ku karasa kasheta a can ko?”

“Wallahi ba manufata kenan ba, ni taya zan ce na kashe rai balle kuma Hurriya haba Hajiyaba zan iya aikata haka ba, kawai maganar da kika fada mana ne, na lura da haka ya kamata na yi kasancewa uwa, a wacan lokacin idona ya rufe ne ni da Alhaji shiyasa har ya koreta, ni kuma na kasa dakatar da abin amman na bashi hakuri Hajiya, ita kanta da zata fadi gaskiya ta sani”

Cikin kuka Hajiya Kaltume take maganar da hawaye shabe shabe a fuskarta. Kukanta ya bata ran Appa har yayi sanadin da ya watsawa Hurriya wani kallo daya saka ta sauke idonta kasa da sauri.

“Hajiya, ki yi hakuri haka ba zai sake faruwa ba”

“Ba fa zata koma ba, daman can ni bana son zamanta a gidan nan, ba za a kula da ita ba yadda ya dace, gashi ba iya magana take ba fa ma Hamad ne shi ne mai iya magana da fadar abun da aka yi har ma ya rama, amman ita ba zata fadi komai ba, ko a lokacin da aka ce taje ta yi gulmarka a wani guri ai be kamata ka yarda ba, domin idan akwai wanda ya san halin Hurriya ciki da waje a duniyar nan kai ne, yadda ta shaku da kai bata shaku da mahaifiyarta haka ba”

Appa ya sauke kansa kasa har lokacin hakuri yake badawa yana neman yafiyar Hajiya.

“Ni na yafe maka amman tabbas da baka zo ba kam, ina nan rike da wannan abun a raina kuma ba zai maka dadi ba saboda ni uwa ce, ko ban fada ba idan raina ya bace zaka iya gani a al'amurranka ko a jikinka ma”

“Toh a yafe min Hajiya hakan ba zai sake faruwa ba, kuma dan Allah ki bar mu mu tafi da Hurriya”

“Ba za a tafi da Hurriya ba, idan ka ga ta bar gidan nan to a dayan biyu ko dai ta yi aure ko kuma na mutu”

Hajiya ta sake fashewa da kuka, ita kanta Hurriya ta tsorata da yadda Hajiya take son komawarta a gidan har da hawayenta. Cikin kukan Hajiya Kaltume ta kalli Hurriya data kasa tashi a gurin da take zaune ta ce.

“Subhanallahi, ki yi hakuri dan Allah, kuma ki sak baki Hajiya ta hakura ita ma, wannan maida magana baya da ake ba shi da dadi, takas mahaifinki ya zo saboda ya tafi da ke, dan Allah ki yi hakuri Hurriya”

Hajiya Binta ta yamutse baki.

“Hurriya bata da ikon kanta, ikonta yana gurin mahaifinta da mahaifiyarta sai kuma ni, dan haka ki daina saka Hurriya a cikin maganar nan”

Hajiya na fadar haka Appa yayi karaf ya kalli Hurriya ya ce.

“To idan haka ne, Hurriya ina baki umarni a matsayina na mahaifinki ki koma gida cikin yan'uwanki, idan ba haka ba zaki yi mamakin abun da zai biyo baya...”

Appa na gama fadar hakan ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.

“Tashi mu tafi”

Sannan ya mike tsaye, Hurriya ma ta mike tsaye da sauri, cikin karfin hali na tsufa Hajiya Binta ma ta mike tsaye ta rike hannun Hurriya.

“Hurriya ba zata koma ba, gaba daya ka canja tsoho ta ya zan yi umarni kuma ka yi kokarin karya wannan umarni? Anya kana cikin hayyacin Tsoho?''

Ya kada kansa kasa.

“Hajiya ba umarninki nake kokarin karyawa ba, bana son zaman Hurriya a ko'ina sai a gida, sanin kanki ne tun kamin yau kin ce na baki ita ban baki ba, saboda bana son kowa ya rika min da”
Chapter 72 · 0% Book details