← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 159

Sashe 2

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsoron Hajiya Kaltume da duban level din arzikinsa da nata ba daya ba, ya karya mata guiwa gurin amsa masa bukatar da ya zo mata da ita. Sai dai kuma rabo idan ya rantse dole komai sai ya afku, rabon samun Hurriyya da Hamad da kuma karamin cikin dake jikinta ya saka Alhaji Haruna yayi nasarar lurar da ita cewar tana cikin irin matan da yake so tare da nuna mata shi ma a da can talaka ne kamar ita, kuma a yanzu zai saka zane ya tare duk wata ƙura da zata taso.

Kwadayi irin na talaka ya leka gidan mai arziki da kuma burin son taimakon iyaye da samun rayuwar jindadi ya saka Iyami ta amince da bukatar Alhaji Haruna. Sai aka shirya auren a boye sai bayan da da Hajiya Kaltume ta tafi Ummara sannan aka daura auren, Amarya ta tare da Mahaifiyarsa Hajiya Binta, daga lokacin ne sunan ya tashi daga Iyami wanda ta taso da shi tun kirciya ya koma Amma domin a lokacin ta wuce ƴaƴansa su kirata da sunanta Iyami dole su sakaya saboda mahaifinsu.
A lokacin da Hajiya Kaltume ta dawo sai zaman lafiya ya gagari Amma da mijinta saboda fitina irin ta Hajiya Kaltume da gori da wulakanci saboda tana ganinta yar aikinta, gashi kuma Momy ma da take ganin kamar ita aka yi kishiyar bata raga mata, ba ita kadai ba kusan duk wanda ya san ta yi aiki a gidan kuma ya ji ta aure mai gida zai jefeta da kalmar cin amana.

Wannan abun ya tabata matuka sai dai samun Hajiya Binta wato mahaifiyar Alhaji Haruna ya wanke mata rabin damuwarta domin tana sonta fiye da yadda take son abokan zamanta Hajiya Kaltume da Momy, domin Amma tana yi mata biyayya gwargwadon hali, ta dauke ta tamkar uwa da ta haifeta, ta rike da mutumci abun da sauran matan suka gagara yi mata. Tana jin dadi zama da ita kamin Hajiya Kaltume da Momy su ta da fitinar cewar sai dai ya hade su guri daya, suna ganin kamar ita Iyami da ya ware dabam ya hade da mahaifiyarshi ya fi bata jindadi fiye da su, hakan ya saka shi gina babban gida a unguwar Millions Quarters cikin rukunin manyan gidajen da ake ta gasar ginawa a unguwar.

Na shi gidan ya fita dabam saboda kyau da tsari da aka yi ma katon gidan. Bayan haihuwar Hurriya Alhaji Haruna ya tare a gidan tare da Iyalinsa, a lokacin Amma tana da tsohon cikin Hamad, bayan tarewa gidan da wata daya ta haifo ďanta Hamad mai shekara goma da daya a yanzu, tun daga lokacin kuma sai haihuwar ta yi mata shiru tun tana damuwa har ta daina, ta rumgume yayanta biyu da Allah ya bata Hurriya da Hamad. Amma ba mace ce mai yawan shige shige ba wannan ya saka a duk lokacin da aka ce ta nemi taimako sai ta ki, domin bata san gurin waye zata duka ta tara hannu ya bata magani ba, sai Allah.

A yanzu kuma da Allah ya tashi bata haihuwar sai ya kawo cikin na uku daman da kurciyarta a yanzu ne take cin nata lokacin ba kamar abokan zamanta da mijinta da suka bata kusan shekara goma sha biyar biyar ba, mijinta kuma ya bata kusan shekara ashiri. Domin yarta ta farko Hurriya a yanzu tana da shekara goma sha biyar ne, a yayinda ita kuma take da shekara goma sha shida da auren a gidan Alhaji Haruna Mai Yadi wanda shi ne mijinta na farko. Hajiya Kaltume da Momy kuma duka last born dinsu shekarunsu goma sha bakwai ne a yanzu. Iyami ta sha wahala sosai a gurin abokan zamanta na makirci da tukgu irin na kishiyoyi, yarta Hurriya kuma ta sha wahalar yan'uwa wadanda suke uba daya tun tana karama har girma, suna yawan hantararta da gori ga duka kamar ita din ba ďaya take da su ba.

Hurriya kyakkyawa ce sosai irin kyau nan mai matukar daga hankalin wanda ya san kyau da sirrin kyau, irin kyau da ke shiga cikin ido ya afka a kwakwalwa ya zauna a zuciyar mai yinsa, irin kyau da idan ka kalleta sai ka sanar da zuciyarka tabbas tana da kyau, irin kyau da sai bakin ya bawa dan'uwansa labarin kyauta, ko kadan bata dauko mahaifinta a baki da muni ba, domin kowa ya san Alhaji Haruna ya san ba kyakkyawa ba ne, wasu har kirari suke masa ba dan kudi ba da sai bola, shiyasa a lokacin da aka yi aurensu da Iyami kowa yake cewa ta bi kudi shi kuma ya bi kyau. Hurriya mahaifiyarta ta dauko sai dai ta dara mahaifiyarta kyau nesa ba kusa ba, ta fita haske ta fita komai hakan ya saka ta fita dabam kamar ba yar gidan ba, domin yaran Momy ma da suke da kyau ba su kai Hurriya kyau ba balle kuma yaran Hajiya Kaltume da suka dauko ta wasu kuma suka biyo mahaifinsu, ba laifi suna da nasa kalar kyau, domin ko wace halitta ta Allah kyakkyawa ce.

Duk tarin kyau da haibar da Hurriyya take da shi tana da wata lalura da aka haife ta da ita ta rashin gani, bata iya tantance komai sai da gilashi, idan babu gilashin ido a tare da ita wato medical glasses bata iya banbance fuskar kowa sai dai ta yi amfani da murya, tana iya ganin abun da ke gabanta ko gefenta haka ma ta kan iya banbance mace da namiji ta hanyar sifar da tufafin jiki, sai dai ba zata iya fadar yadda fuskarsu take ba, domin dishe-dishe take gani, kusan eyeglasses shi ne rayuwarta bata iya komai sai da shi idan yana a idonta tana ganin komai clearly kamar yadda kowa zai gani ko ma fiye da haka, idan kuma babu bata iya karatu bata iya ganin kyau ko munin mutum, hakan ya saka bachi kadai ke rabata da gilashi.

An nema mata magani har an gaji amman babu sauki babu alamarsa, wani gurin ma a madadin samun sauki sai idon ya kara dishewa, tsoron kar ta rasa idon gaba daya ya saka aka daina nema mata magani Alhaji Haruna ya saka likita kwarare ya duba idonta ya fadi kalar gilashin da zai dace da ita mai kyau da tsada, mahaifinta ya saka aka kera mata har guda biyar a lokaci daya.
Biyu daga cikin gilasan da mahaifinta ya saka aka kera mata ne suke hannunta, sauran ukun suna gurin Yayanta Yassar ya aje mata a bangarensa gudun kar su bata, domin tasu ta zo daya shi kadai ne take jin sanyinsa a cikin Yayan Hajiya Kaltume ya ke sonta da nuna mata kulawa tsakani da Allah kamar kanensa da suke uwa daya uba daya, Yassar kam ya fita dabam kusan ya fi sabawa da Hurriya ma fiye da sauran yara da suke gidan, yana sake mata fuska tana wasa da shi kamar ita da shi din abokan wasa ne. Idan yana gidan bata da hutu ga tsokanarta da yake yawan yi. Yassar yaro ne mai mutunci da kamanta gaskiya, domin yana ba wa Amma da Momy dukanin girmansu sam baya biye hudubar da mahaifiyarsa take masa, be taba yarda ya hau turbar da take dorashi ba, Munib da Miwan suke kan gaba gaba gurin taya Momy kishi dama da hagu har sun fi yar'uwarsu maace taya mahaifiyarsu kishi.

*** *** ***

Wannan Kenan, shimfida ce da share fagen yadda labarin zai tafi, labari ne mai ƙayatarwa da sarkakiya da kuma ƙulla-ƙulla sannan yana dauke da darasi na rayuwa. Allah ya sa mu amfana da shi kuma ya ba ni ikon gamawa lafiya kamar yadda na fara. Sannan ina son ku sani labarin nan ban yi shi dan wani ko wata ba, idan ma ya yi daidai ko ya ci karo da rayuwar wasu, to arashi aka samu. Tare da fatar za ku tara hannu biyu ku karɓa kamar yadda kuka saba karɓar labaraina cikin farinciki da ɗauki, sai a taya ni da addu'a na baku abun da kuke so, ma'ana na faranta ranku fesss 😀

Masoyana Asallamu Alaikum mun sake haɗuwa a wata sabuwar tafiya, Allah ya sa mu wanye lafiya kuma mu kai karshenta cikin farinciki da Amince.
Sakon gaisuwa da fatan Alheri daga taku mai son farincikinku Khadeeja Candy🥰 08036126660.

https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1

☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

𝗣𝗮𝗴𝗲 2️⃣

Ta aje plate din hannunta da sauri ta zari tissue ta goge bakinta.

“Amma na tafi kar na yi latti”

Amma dake kokarin jefa tawul a ruwa ta ce

“Kya ji da shi, kullum ke ce uwar yan latti sai an jiraki, ga kokari ga buga latti”

Hurriya ta dauki jakarta ta makaranta da sauri ta goya tare da daukar lunch box dinta ta fice daga falon da gudu, kamar zata fadi haka ta isa bangaren Appanta sai haki take kamar wadda aka yi yakin duniya tare da ita. Hannu ta mika jikin window falon kamar yadda sauran yan mata sa'aninta da wandanda suka girmeta suke mika na su hannu suna karbar karamin hollandia da chocolate da yake raba musu, tana son karba yan'uwanta na tureta tana yin baya har sai da suka gama karba sannan ta samu karba daga gurin mahaifinta, kyautar wani abun ci da ko abun sha a kowace safiyar week days wani abu ne da ya sabawa yaransa da shi tun suna kanana.

“Na gode Appana”

Ta fada tana murmushi jindadi, shi ma murmushin yayi yana kallon kyakkyawar yarsa, mai yawan yi masa godiya da nuna masa jindadinta a duk lokacin da yayi musu kyauta komai kankantar kyautar domin haka mahaifiyarta Amma ta koyar da ita, kusan ita ce karama a cikin yayansa mata a cikin maza kuma kanenta Hamad ne karami ƴaƴansa na jini amman ya fi sauran yayansa godiya da yabawa idan yayi musu abu.

“Allah ya miki albarka Hurriya, ga ladabi ga basira”

Ta yi yar siririyar dariya mai sauti.

“Appa haka Uncle dinmu yake cewa, har da cewa yayi wai akwai wata gasar da zan sake shiga”
Chapter 2 · 0% Book details