← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 159

Sashe 37

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hindu na rufe baki, masu gadi suka bude gate motar da aka je dauko su Hamad da ita ta kunno kai cikin gidan, gaba daya sai hankali ya koma can Hajiya Kaltume, Salma, Maama Khairi suka fito daga bangaren Hajiya Kaltume da gudunsu har Hajiyar da jiki ya hana ta walawa yadda take so, Namra ta shiga bangarensu da gudu kiran Momy. Appa ma ya fito da waya a kunne sai dai fuskarsa babu annuri ko kadan, ba irin da wanda ransa ya bace ba, rashin annuri ne irin na wanda ya rasa wani abu fuskarsa ma gaba daya launinta ya canja. Amma ta fito daga cikin motar ta nufi motar da Yasir ya sauko yana hawaye Ruma kuma na rutsar kuka.

“Ina Hamad? Ina Hamad?”

Amma ta tambaya domin yaronta ne kadai bata ga ya fito daga cikin motar ba. Aka rasa mai ce mata komai har ta isa gurin ta tsaya tana kallonsu murmushin dake fuskarta na kokarin gushewa.

“Yasir ina Hamad? Dan Allah ku amsa min...!”

“Amma sun kashe shi, sun kashe Hamad...!!!!!!”

Ruma ta fada da karfi tana kuka. Momy ta dora hannu saman kai tana fadin Innalillahi. Amma kuma ta yi baya baya kamar mai tafiyar baya sai Hindu ta rike ta, runtse ido ta yi ta kai hannunta ta dafa cikinta dake zillo ta durkusa a kasan guiwoyinta ta dafa kasa. Hajiya Kaltume ma kuka take ta nufi yarta ta rika hannunta da niyar rumgume sai Ruma ta buge hannun Hajiya Kaltume ta nufi mahaifinta tana kuka ta rumgume shi yana hawaye, kusan kowa a gurin sai da yayi hawaye.

“Su ba mu gawarsa mana to mu gani, idan da gaske ya mutu su ba mu gawarsa mu gani Wallahi be mutu ba, boye shi suka yi Hamad yana nan da ransa”

Hurriya ce take maganar tana kuka, Gwaggo ta rikota ta rumgume tana kuka.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya kin daukar kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

𝐏𝐚𝐠𝐞 5️⃣

Hurriya first lost her sight a jikin Gwaggon, before ta yi going blank aka kwasheta ita da Amma sai Asibiti. Amma aka wuce da ita dakin haihuwa Hurriya kuma aka kaita Emergency. After 49hours of labor Amma ta haihu tagwayenta biyu duka maza. A madadin ta yi murnar ta haihu ta samu yan biyu sai murnar ta koma mata ciki saboda tunanin Hamad bata da wani kuka sai na Hamad. The following day aka sallamo ta daga asibitin bayan sun mata dinki kuma sun dorata akan maganin da zata rika sha na hawan jini sannan suka hana ta wankan ruwan zafi domin jinin nata ya hau sosai irin hawan da ba dan Allah ya kawo sauki ba, da abu ne mai wahala ta fita lafiya.

Har lokacin Hurriya tana asibitin Hajiya Binta na jinyar tare da taimakon Rukayya, kwananta biyu bata san inda kanta yake ba a asibitin, kamin ta farfado sai kuma ta zama so weak sai da ta sha drip da manyan allurar sannan ta samu sauki, the following day ita ma aka sallame ta two days after an sallami Amma. Wani abun da ya bawa kowa mamaki ciki har da Momy kuma ya daurewa Amma da Hajiya Binta kai shi ne, kin lekawar Alhaji Haruna a asibiti ko gida da sunan duba Amma ko kuma duba yaran da ta haifa masa, yan'uwansa na nesa da na kusa duk sun je duba twins din kuma sun je duba Hurriya wasu ma ba su samu labarin abun da ya faru ba sai a da suka je barkar twins. Sai dai Appa be bar rashin zuwa duba yaran da kowa ke musu lale da zuwa duniya, ya hana shi kyautata musu ba, duk wata hidima ta ya kamata uba yayi ma yayansa Appa yayi tun daga kan tufafin mai jego Amma har na jaririnsa, sai dai Amma bata yi taron suna ba, duk kuwa da kasancewar ba ayi taron gaisuwa a gidanta ba, an yi zaman makoki a gidan Appa kuma an masa sallatul ga'if wato sallar da ake yi ma gawar da bata kusa. Ta ko'ina Appa ya karbi gaisuwar mutane ana ta jajanta masa. All those days, hour's Hurriya a daki take rayuwa, domin bata son ganin kowa, idan zata yi alwala sai ta shiga bathroom ta yi idan ta yi sallah ta kwanta, bata son ayi mata gaisuwar Hamad, bata fitowa idan mutane suka tambayi ina take, idan kuma aka shigo sai ta rufe kunnuwanta bata sauraren kowa, she's the only one da ta kasa yardar Hamad ya mutu, ranar sunan yaran ma sai da ta saka kowa kuka, domin ihu take ta yi me yasa Amma ta sakawa little one din Hamad yayan kuma Hamid.

“Amma da baki saka Hamad din ba, Wallahi Hamad be mutu ba, karya suke yi Amma dan Allah ki cire, ki saka masa wani sunan ba Hamad ba”

Tana kuka tana rokon Amma a canjawa jaririn suna, Amma ta aje Little Hamad ta kama Hurriya ta rumgume.

“Hurriya dole mu karbi wannan gaskiyar, tana da daci amman dole ne mu karbi kaddara, duk yadda kike son Hamad na fi ki sonsa domin ni na yi nakudarsa na haife shi, una jin fiye da yadda kike ji”

“To me yasa kika sama Amma? Why? Why?”

Amma ta girgita da karfi tana kuka.

“Saboda ya mutu Hurriya, baki daya Allah ya karba ya bamu biyu ba? Toh sai mu gode masa, yadda ya so haka yake aikatawa, Hamad ya tafi tafiya ta har abada ya kamata ki karbi wannan, wannan shekarar haka ta zo mana”

Hurriya ta saki jikinta sai ta lankwasa ta yi baya Amma ta sake ta ta fadi kasan carpet din. Ita kam ta kasa yarda dan'uwanta ya tafi ya barta, fadan da suke yawan yi yake damunta a yanzu, why take ramawa idan yayi mata abun? Ko wane motsi yana tuna mata da dan'uwanta ne, bata taba sanin tana kaunarsa ba sai a yanzu da baya kusa da ita, ina ma ita aka dauka ba shi ba haka take yawan ayyana a ranta. Kusan kowa a gidan sai da yayi kuka kuma aka kasa wanda zai rarrasheta sai Yayanta Yasir, domin shi kadai ya fahimci manufarta kuma ya mara mata baya cewar Hamad be mutu ba, domin karbar gaskiyar cewar ya mutum shi ne ƙarya a zuciyarta.

****   ****     ****    ****

“Hajiya ki yi haƙuri dan Allah, bana son ina musa miki akan abubuwa, amman yaran nan da Iyami ta haifa nawa ne, idan ina buƙatar ganinsu ba sai na jira wani ya ba ni shawara ba, ayukan ne sun min yawa a yanzu amman da zarar na samu lokaci zan je na duba su, idan suka yi ƙwari ma aka yayensu ɗauko su zan yi na dawo da su gidana domin zuciyata ta fi amintuwa da haka”

Hajiya Binta ta kalleshi tana mamakin yadda yake ita bude baki ya musa mata a duk lokacin da ta yi masa maganar zuwa duba Twins din da Amma ta haifa.

“Tsoho me yake damunka? Wani lokaci ne baka da shi akan iyalinka?”

“Hajiya kin san kasuwanci ba daya ba, kuma idan ina son ganin yaran nan ni zan je da kai na, ina cw dai na sauke duk wani hakki na uba?”

“Toh baka bukatar ganinsu kenan? Haka kake nufi? Toh ni da nake bukatar ganinsu zan tafi, ko miye ya rufe maka ido ka kasa taka kafarka gidan Iyami Allah ya yaye maka shi tsoho, yau sati daya da haifa maka yan biyu kyautar Allah amman ka kasa taka kafarka ka duba yayanka”

“A gaishe su, Hajiya zan leko in Shaa Allah, kuma idan kin tafi ki fada mata next week Hurriya zata dawo zan aiko da mota a dauke ta saboda makaranta”

Yana maganar yana mikewa tsaye abun da be saba yi ba, ko magana Hajiya Binta take masa baya iya daga kai ya kalleta tsabar biyaya amman a yanzu duk ya canja mata, abun da be yi mata da kurciya ba a yanzu da girma ya kama shi yake canjawa. Baki saki Hajiya Binta ta fi danta da kallo har ya fice sannan ta girgiza kai hawaye na cika idonta.

“Allah ka shirya bawan nan naka, Allah ka karya duk wani abu da aka yi masa Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”
Chapter 37 · 0% Book details