← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 159

Sashe 152

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ni na saka aka dauke shi Wallahi... Ni na ce a sace Hurriya su kuma suka dauke shi ina ta murna asirina yana rufe sai kuma ka ce min wai Hamad ya dawo? Gidan yari zan tafi kenan? Gidan yari zani Yasir?”

Ya rike rigarta yana kuka, ya dago ya kalli kenansa.

“Akwai wanda ya san wani abu a cikinku...”

Cikin kuka Ruma ta ce.

“Eh gaskiya ta fada, ita ta saka aka sace Hamad, kuma Hamad da ni duk mun ji muryarta lokacin da take magana da su, Har yake cewa Hajiya me na yi kika ce a kawo mu nan? Idan na dawo sai na fadawa Appa, sai ta fara fada tana cewa ya ji muryarta zai tona mata asiri, bayan ta kashe wayar ne suka buga mishi karfe akai kan ya fashe yana ta jini, Hamad yana ta ihu yana kiran sunan mutane har da ni, suka fitar da shi daga dakin suka bar ni daga nan ban san me ya faru ba...”

“Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'u ײ”

Yasir ya furta har sau biyu sannan ya mike tsaye ya rike bakinsa. Khairy kuma ta fadi zaune tana kuka domin bata taba jin wannan ba sai yau. Hajiya Kaltume kuma bata fasa tonawa kanta asirin abun da ta yi ba, tana ta firgar rigar jikinta da zanenta.

“Hajiya me yasa baki ki tunanin makomarki ba da ta mu kamin ki aikata? Wane irin abun kunya ne wannan? Har yaushe zuciya zata bushe ki aikata hakan ga dan mijinki dan be miki komao ba, be tare miki komai ba? Idan ma kishi kike da mahaifiyarsa shi meye nasa a ciki? Gashi har kina fadar sanadinki Salma ta mutu...”

Hajiya Kaltume ta kyalkyale da dariya ta buga kafa. Ta janyo jakarta ta ciro maganin da ta dawo da shi ta zube a gurin.

“Ai ba Shikenan ba, ni na saka Khairy ta dauke gilasan da suke dakinka na Hurriya, ni na yi ma Hurriya da Appanta farraqu, aka saka masa tsanar Hurriya, ni na saka aka saki Iyami Yasir ni na yi mata wannan asirin kuma na ce a kwantar da ita ciwo, kuma na ce ayi mata asiri kar wani ya ganta ya aureta, yanzu wannan maganin shi kuma bokan ya fada min idan na yi amfani da shi Alhaji zai zo Jiki na rawa ya maida aurensa, kuma Fadeel zai dawo ya auri Khairy... Kawata Hajiya Fatee ita take kai ni ko'ina ita ma kuma tana can da ciki cikin haihuwa wanda ta saka malam ya danne, na biyawa Malam makka saboda na jidadin aiki, na mallaka Alhaji sai abun da nace yake min... Tabbas na aikata Hamad kuma ni na dauke shi ni ce nan na aikata, kuma na yi shiga gaban Alhaji da Sapna na kawar masa da ita a zuciya ya fita maganarta na shashantar da ita a zuciyarsa...”

Kusan duk wani abu da Hajiya Kaltume ta aikata tun cancan da har zuwa yau sai da ta fadawa yaransa da wanda suka sani da wanda ba su sani ba. Yasir sai ambaton Allah yake be taba tunanin mahaifiyarsa ta yi nisa haka ba sai yau be taba tunanin ita ce sanadin barin Amma a gidan ba sai yau, be san ita ta shiga tsakanin Hurriya da Appa ba sai yau, be san ita ta aikatawa Hamad haka ba sai yau. Ya rasa ta ina zai fara ya rasa ina zai saka kansa ya samu sassaucin rayuwa.

“Ku shiga da ita cikin daki ku rufe karku bari ta fito”

Ya fada sannan ya share hawayensa yana jin kamar ace ya mutu kamin yau. Ruma ta kalleshi tana kuka.

“Yaya yanzu idan da gaske Hamad ya dawo gidan yari za a kai Hajiya Kenan?”

Ya cije baki ya saka cewa komai sai hawaye ke sauko masa. Tashi yayi ya fice daga falon ya nufo bangaren mahaifinsa ya zauna a gurin yana jin wani bala'in gabas da na yamma yana hade masa, da ma ace wata ce daga cikin kannensa zai ji sauki amman uwarsa? Abun yayi masa muni gaba daya ma sai ya rasa abun da zai yi, tun farko be ga dalilin Hajiya na aikata hakan ba, domin bata rasa komai a gidan Appansa ba idan ma ta tasa me yasa ba zata barwa Allah ba. Yanzu wa gari ya waya? Karshenta jifan akan wa ya dawo? Waye yayi mummunan karshe? A yanzu ya kara jin kaunar Amma a ransa domin ita da ta wakkala ga Allah gashi yayi mata mafita kuma yana kan mata, Hurriya ma haka, Amman Khairy gashi ta girbi abun da ta shuka tun abun be yi nisa ba, Hajiyarsa ga abun na kokarin taba hankalinta ko ma ya taba.

Allah kawai yake ambato ya rasa me zai yi, wa zai tunkara da maganar ya rasa ina zai bullowa lamarin. Yana zaune a gurin har la'asar, sallamar ma yana yi ya sake dawowa gurin ya zauna tunani yake amman tunanin ya ki tsaya masa ya tasa wanda zai ba shi shawarar abun da ya dace ya aikata. Asibiti zai dauki Hajiya ya kaita? Ko kuma dai ya sanar da Iyayenta da kanenta domin babu iyaye a yanzu, ko kuma dai ya samu mahaifinsa da maganar. Daga balcony din da yake zaune ta bangaren Appa ya hango shigowar motar Maama, hakan ya saka shi tashi ya nufi bangaren mahaifiyarsa, a dakin ya sameta tare da sauran yan'uwanta Khairy da Ruma suna kuka har lokacin Hajiya Kaltume bata daina tonawa kanta asiri ba.

“Ku kira su Hajiya Fanna da Mama Zainab ku fada musu halin da ake ciki, idan asibiti za a kai ta sai mu tafi...”

Maama ta juya ta kalleshi tana hawaye

“Haka Jarabawar ta zo mana Yaya? Ni gidan aure babu dadi Hajiya kuma nata auren ya kare, Khairy an fasa yanzu kuma wannan ya biyo baya?”

Yasir ya daka mata tsawa kamar zai daketa.

“Laifi duk na waye ba naku ba? Idan ta kauce ko zata aikata wani abun da ba daidai ba kun fi kowa sani, me yasa ba zaku nuna mata illar hakan ba? Amman ke kuke zugata kuna tayata kishi ku nuna abunda take daidai ne, ke Khairy lokacin da kika aikatawa Hurriya haka bata ma sani ba, saboda zuciyarku babu kyau, ke kuma idan abun kwarai ne gashi yanzu kin yi aure kin girba, kar wanda ya sake saka min baki akan lamarin uwata kar wanda ya sake wata magana ku bar ni na ji da zafi daya”

Ya share hawayensa ya fice daga dakin, ya sauko kasa wayarsa tana ringing da ya duba sai yayi arba da number Appa, and for the first time sai ya ji ba zai iya amsa kiran ba, a yayinda wayar yake rike a hannunsa tana ringing. Ya jingina da kofar falon ya cije bakinsa ya buga ginin ya girgiza kai. A karo na biyu wayarsa ta sake yin ringing ya dago ya duba wayar Appa ya sake kira wannan ya dauka sai dai yana kara wayar a kunnesa sai ya fashewa Appa da kuka kamar mace.

“Subhanallahi... Yasir.. Lafiya kana ina?”

“Ina gida Appa.. Amman ba lafiya, ji nake kamar na bar garin nan kamar na tafi a inda babu kowa na rayu a yau, duk na ji duniya ta isheni”

“Toh gani nan zuwa gidan”

Appa ya sauke wayar yana jin karin wata damuwar, daman ya kira ya fada masa yadda suka yi daman ya kira ne ya fada masa yadda suka yi da Amma da kuma Captain sai dai jin halin da dansa yake cike har yana kuka ya saka shi jin babu dadi domin be san Yasir da bayyana damuwa idan ma akwai.
Yasir ya share hawayensa yana kokarin ganin yayi halin maza wajen hana kansa kuka da jin tsanar duniya da halin da yake ciki, ya nufi bangaren Appa, a Balcony ya zauna kamar dai dazun yana jiran Appa, sai dai Yayyun Hajiya Kaltume da Maama ta kira ta fada musu halin da ake ciki sun riga Appa zuwa, hakan kuma be saka Yasir tashi ya koma bangaren ba, domin baya son ya sake kallon mahaifiyarsa a cikin wannan halin. Direban Appa ya fakawa Yasir ya mike tsaye Appa kuma ya fito mota da sauri yana kallon Yasir.

“Mu shiga ciki”

Yasir ya wuce gaba sannan Appa ya bi bayansa, a babban falonsa suka fara zaunawa Appa ya dubi ďansa cike da damuwarsa ya ce.

“Lafiya Yasir? Me ya faru..?”

Nauyin furucin da kunyar abun da mahaifiyarsa ta aikata sai ya saka shi kasa furta komai a gaban Appa.

“Yasir daga kanka ka kalleni mana fada min damuwarka ni kaina da nake mahaifinki wani abun ai kai nake samu mu tattauna balle kuma kai da kake ďana me yake faruwa?”

“Appa a game da Hamad ne... Dazun ban mun gama magana da kai na shiga cikin gida na fadawa Hajiya abun da ya faru...”

Ya kwashe abun da ya faru ya fadawa Appansa domin be san a inda zai bude damuwarsa bayan nan ba. Appa ya mike tsaye yana ambaton Allah yana jin kamar duniya zata rikito ta fado masa tsabar tsorata da abun da Hajiya Kaltume ta aikata.

“Yanzu da saka hannun Kaltume aka dauke ďana? Da sa hannunta a rabuwata da Iyami? Me na... Me.. Mena rage ta da shi? Akwai ta inda na canja mata ne bayan auren nan? Ba Iyami da yayanta kadai ba har da Sapna? Ita me ta yi mata? Wace irin mata ce Kaltume? Me yake damunta? Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”

Duk yadda Yasir yake tunanin abun ya gigita shi sai ya tarar ya gigita Appa fiye da shi domin sai da ya tsorata da yadda Appa ya rike kirjinsa ya dafe saitin da zuciyarsa take, tsoron rasa mahaifinsa ya saka shi nadamar sanar masa abun da yake faruwa.

“Appa dan Allah ka zauna”
Chapter 152 · 0% Book details