← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 159

Sashe 49

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_________________
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo...

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻

𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

𝐏𝐚𝐠𝐞 1️⃣1️⃣

Hajiya Kaltume na tsaye rumgume da Hanayenta Yasir ya faka motarsa ya fito, sannan Hurriya ma ta fito sau daya ta kalli gurin da Hajiya take ta dauke kai ta fice daga apartment din ta nufi na Momy, wata kalar harara Hajiya take watsawa Yasir har ya iso.

“Ina ka fito?”

Ya juya ya kalli Hurriya da tuni ta fice daga bangaren sannan ya kalli mahaifiyarsa.

“Mun sauke Rukayya ne”

“Kun sauke Rukayya kamar ya?”

“Hajiya dare yayi shiyasa na kaita gida a mota, daga can Hurriya ta duba Amma”

“Ita bata san dare yayi ba ta kama hanya ta zo? Kasan ma a ina ta fito? Wace yarinya mai tarbiya ce zata fita yawon dare?”

“Hajiya Stop...”

Ya fada yana kokarin danne bacin ransa.

“Ba sai ka min turanci ba, daman yaran zamani ne ku ai, sai ka zage ni ban sani ba, amman dai bari ka ji na fada maka ka fitar sapgar Rukayyar nan ba yarinyar kirki ba ce”

“Hajiya please karki munanawa Rukayya zato, yarinyar nan tana da hankali da tarbiya, na san wacece ita, saboda ta yi dare baki san dalilin da ya saka ra yi haka ba, ki daina fadar bata da tarbiya bata min rai kike, yanzu da wani yayi abun da Khairi ta yi da yanzu kin zage shi, amman kin tsallaketa kina ganin laifin yar wasu, dan Allah wannan ya zama na karshe da zaki fadi wata magana marar dadi akan Rukayya”

Yana gama fadar haka be tsaya jin abun da zata fada ba ya wuce ciki ya barta a gurin tsaye da mamaki.

“Ikon Allah baka son a fadi wata magana marar dadi akan Rukayya saboda Rukayya kanwar uwarka ce? Anya dai Iyami bata Zuba maka ka sha ba, kai duk wani abu da ya shafeta sonshi kake, daga kan Hurriya har Iyami yanzu kuma abun ya koma kan kanwarta, eh lallai tun da ka ga farar fata, to Wallahi baka isa ba ba Rukayya ba ko keya ce sai na ga bayanta, wato ma wani abu ne a cikin zuciyarka da har idan an fadi sunanta da mugun abu ranka yake ba ci, har da wani tashi ka kaita gida kai ga Sharukhan baban Soyayya, to da ni kake zancen”

Ta juya ta bi bayansa tana masifa, a falo ta zame shi zaune yana lasa wayarsa yana ganinta yayi saurin tashi ya nufi stairs dan ya san fada zata masa, da kallo da bishi har ya haye sama.

“Ba shakka, wato ubanka ya dandana nan bakin cikin Iyami shi ne kai ma zaka gwada naka ko? Dadin abu kai haihuwar ka na yi ba aure ba, baka da ikon kanka sai ikon da ake da shi akanka”

Ta zauna a inda ya tashi tana jin zuciyarta na wani irin zafi, domin bata da makiya a yanzu kamar Iyami da iyalinta...

HURRIYA POV.

Da sallama ta shiga falon Momy ta dago ta kalleta ta dauke kai, Namra kuma dake kwance cinyar Momy labarin da take da Momy ya hanata amsa mata.

“Ni Wallahi tausayi yake ba ni gaba daya ya koma kamar ba shi ba, dan murmushin da yake da yanzu duk ya daina”

Momy ta shafa goshinta.

“Fadan kuma ya karu ba, sai bakar zuciya da ganin laifin kowa”

“Ai dole”

Hurriya ta risina tana yi ma Momy sannu da dare.

“Ina kika fito?”

“Tare da Yaya muka fita ya aje Mama Rukayya a gida ne, ni kuma na duba Amma”

Hurriya ta amsa tana jin kamar ace ita ce take kwance a cinyar Amma, Amma na shafa kanta yadda ta shigo falon ta tararda Momy da Namra abun ya burgeta sai ya kara mata kewar mahaifiyarta sosai. Namra ta tashi zaune

“Wayyo ban sani ba da naje dubata ya jikanta Hurriya”

“Da sauki”

“Allah ya kara sauki”

Hurriya ta amsa da amin sannan ta mike tsaye ta, Momy ta bita da wani kallo kamar na tuhuma tana tsire baki. Hurriya ta shiga dakinta ta cire hijabin jikinta ta nufi gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, sai hawaye suka fara zubo mata. A take ta sauke kanta kasa tana kallon hannayenta.
Rayuwar baya take tunawa lokacin da take cikin farinciki, Amma na kusa da ita Appa yana kaunarta ga dan'uwanta abokin fadanta kuma mai tare mata fada. Ta tashi kamar marar lafiya ta nufi gadonta ta zauna sannan ta cire gilashin idonta ta kwanta. Bata farka ba sai asuba, bata fito dakinta ba sai 12pm shi ma kuma saboda yunwa ta matsa mata lamba ne daman bata son fita ko'ina sai idan tana bukatar abinci, yanzu ba irin da ba ne da take zuwa makaranta balle fita ta zame mata dole, tun bayan da ta kammala Secondary school ta samu yancin zama a gida domin Appa be yi making wani effort da zai nuna yana son ta cigaba da karatu ba. Ita kuma tana tsoron yi masa magana sai dai ta yi ma yayanta shi kuma idan ya tunkari Appa da maganar sai yace masa akwai abun da yake jira. Daga Momy har Hajiya Kaltume kuma babu wanda ya damu da karatunta da ta yi da kar ta yi duk daya suke a gurinsu, Momy da yaranta take da kanta daman rayuwar wani bata dame ta ba, Hajiya Kaltume kuma bata son Hurriya da alheri ta ina zata damu da karatunta.
A hankali ta sauko kasa tana sanye da doguwar riga kanta babu dankwali, gashin kanta a dan yamutse saboda rashin gyara shi da bata yi ba after ta yi wanka.

“Yauwa Hurriya dan Allah ki shirya anjima kadan zaki raka ni Mall na siye wani abu”

Ta juya ta kalli saitin gurin da Namra take zaune tana shafa abu a fuskarta.

“Toh Yaya Namra”

Sannan ta juya ta shiga Kitchen din ta hada tea ta fito ta nufi dining ta zuba abun da zata iya ci ta dauka ta sake dawowa dakinta ta zauna a kasa ta nade kafafuwanta ta fara ci, bata wani ci sosai ba ta fi ta koshi sai ta ja komai gefe ta aje. Tana zauna a gurin har aka yi azahar, bata sake fitowa dakin ba sai da Namra ta tura kofar ta leka ta.

“Kin shirya kuwa?”

Sai ta sauko saman gadon ta nufi gurin madubi ta dauka ta gyara kanta ta saka ribbon ta dauki mayafin abayar ta rufa.

“Eh mu tafi yanzu”

Namra ta yi dariya ta girgiza kai sannan ta juya ta fita tana fadin.

“Shiyasa lokacin zuwa makaranta kike late ba zaki shirya ba sai a lokacin da ake jiranki”

Murmushi kawai ta yi ta jira tare da Namra suna sauka tare, Hurriya na ganin Momy ta yi saurin risinawa kamar yadda ta saba gaishe da manya.

“Momy barka da yamma”

Momy ta watsa mata harara.

“Sai yanzu kika ga damar gaishe ni, ba kin san ina cikin gidan ba? Me yasa baki gaishe ni ba sai yanzu”
Chapter 49 · 0% Book details