← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 159

Sashe 50

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi shiru ba dan bata da abun fada ba, sai dan ta san tana fadar wani abu Momy zata iya tsinka mata mari, kamar yadda bata isa ta shiga dakinta da sunan ta zo gaishe ta, sai dai ta tsaya jiranta idan ta fito ta gaisheta kamar wata yar aiki, wannan ne abin da Hurriya ta kasa yi, Momy kuma take jin haushinta.

“Momy mu dai mun tafi”

A take murmushi ya cika fuskarta tana kallon yar gudaliyar yarta mace daya tak data haifa.

“Allah ya tsare, ya dawo lafiya yar Auta”

Ta yi murmushi sannan ta yi ma Hurriya alama da ta tashi su tafi, Hurriya ta tashi suka fice tare. A tare suka shiga motar Namra na tuki Hurriya na zaune gaba tana sauraren sautin da Namra ta kure a motar idanuwanta kuma suna kallon wani gurin dabam har suka isa Sarauta Mall. A harabar Namra ta faka ta fito sannan Hurriya, after ta rufe motar suka nufi cikin Mall din tana fadawa Hurriya abubuwan da take son siya.

“Zaki iya daukar wani abu da kika ga kina so amman fa kar ya wuce 20k”

Fuskar Hurriya ta cika da murmushi.

“Na gode Yaya Namra amman ni ki ba ni kudin akwai abun da zan yi da su”

Da mamaki Namra ta kalleta tana kokarin kai hannu ta dauki turare.

“Me zaki yi?”

“Wani abu dai bana son na fada, amman yana da muhimmanci sosai”

“Shi ke nan to idan mun koma ki turo min account dinki sai na miki transfer”

Take a gurin Hurriya ta rumgume ta.

“Na gode Yaya Namra ke ma kina so na kamar Yaya Yasir”

Namra ta yi murnushi suka ci gaba da siyayyar after sun gama suka nufi gurin biya, Namra ta bude jakarta ta dauko cart dinta ta mika.

“Aa an biya muku Hajiya”

“An biya kuma?”

“Eh ba na yau kadai ba har ma da wanda zaku sake zuwa nan gaba ko da kuwa za ku yaye shagon nan ne gaba daya”

“Waya biya? Wanene wanda baya son kudinsa haka?”

“Gashi can bayanku”

Daga Hurriya har Namra juyawa suka yi kallon mai neman barar da kudi saboda be san kimarsu ba. Suna hada ido kowanensu ya gane waye. Shi kuma ya nufo inda suke idonsa na kan Hurriya.

“Kai ka biya kudi?”

Namra ta tambaya tana hade masa rai.

“Eh”

“Saboda me?”

Ya kalli Hurriya dake tsaye tana kallon ikon Allah.

“Saboda Hurriya”

“Miye tsakaninka da ita? Kuna da wata alaka ne?”

“Alakar dai nake kokarin kullawa, waye ke?”

Wannan karon Hurriya ce da kanta ta tari numfashin yayarta ta amsa masa rai a bace.

“Yayata ce, kuma daga yau karka sake nuna ka san ni domin ni ba yarka ba ce, kuma karka sake kiran Yayana a waya kana cewa a hada ka da ni”

Adam yayi murmushi.

“Ya fada miki kenan? Na kira Khairi ta ki hada ni da ke, the last kiran da na yi ma yayanki ma be saurare ni ba ya rufe ni da fada, Na gode Allah ma da na ganki a nan”

“Eh saboda basa son kana kirana kuma karka sake, sunana ya fita daga bakinka, mu tafi Yaya Namra”

Namra ta bita da kallo she never thought Hurriya zata iya bude baki ta yi masifa haka. Shi ma kallonta yake domin bata yi kama da irin yan matan nan masu masifa ba. Adam ya maida dubansa gurin Namra da ta mika hannu ta dauki ledar kayanta.

“Khairiyya ce ta ce muku ni dan'iska ne?”

Namra ta kalleshi sama da kasa at his age ba zai wuce 25-26 ba that's mean ya bata shekara daya kenan ko biyu.

“Malam Hurriya ba irin matan nan ba ne, dan Allah ka kama gabanka”

Ta dauki ledarta ta nufi kofar fita, suka bar shi a gurin kunya kunya ma'aikatan gurin na kallonsa. Ko da Namra ta isa gurin motar Hurriya na tsaye ta hade rai ya rungume hannayenta tana jiran fitowarta.

“Ashe kin iya fada”

“Ya bata min rai fa, jiya saboda shi Appa kamar zai dake ni, Kuma Yaya yayi ta fada sosai”

Ta fada ba tare da ta kalleta ba.

“Shiga muje”

Hurriya ta bude motar ta shiga, Namra ta fara tukawa. A motar Namra sai zaginsa take yana tsine masa tare da fadar daman irin samarin nan haka suke.

“Ni da na sani ma ba zan birthday din ba”

“Abun yar'uwa ace ba za aje ba? Ai dole ka je Khairy dai ta zama wata kalar mace daman tun kamin ta kare karatun na wata friend dinta ke fada mana tana shan shisha, kamar kar ta fara sami'ar nan sai ta hadu da friends din banza suka canja mata rayuwa gaba daya ta canja”

Tana maganar tana kokarin kwaucewa motar take gabansu. Overtaking take son yi amman mai motar ya hanata hanya, kasancewar titi express ne idan ta yi dama sai ya koma can idan ta yi hagu sai yayi hagu. Horn ta danna da karfi shi ma ya mayar mata, at first ranta ya baci har ta yi kamar ta bugu motar dake gabansu sai kuma ta danne zuciyarta.

“Mai motar nan lafiya yake kuwa?”

“Ko yayi shaye shaye”

“Maybe”

Namra ta rage gudun motar shi ma sai ya rage, the second thing she did was laugh irin abun yanzu kuma ya zama out of sence. Ta dan gwada kara gudun shi ma sai ya kara, ta sake raguwa sai ya rage. Tana samun sa'a ta yi overtaking ta wuce da gudu, shi ma sai ya danna a guje ya wuce, wannan karon har da Hurriya sai da ta yi dariya, Namra ta sake yin gaba ta wuce shi sai ta sauya hanya, ga mamakinta sai ya biyota a baya ya wuce, daga lokacin ne suka fara tseren gudu ita da shi ba dan sun san waye a motar ba. Ita dai daman gilashin motarta a bude yake daga ita har Hurriya ana kallon yadda suke shakar dariya su ne basa iya ganin wanda ke cikin motar. Da gangan Namra ta sake sauya hanya tana dariya tana kallon nearby mirror bata ga ya biyo ba, sai da suka kusa isa karshen Titi sai gashi ya bullo ta gabansu.

“Mun shiga uku Hurriya waye mutumen nan?”

Hurriya dariya kawai take ta kasa cewa komai, domin a gurinta abun is so funny ita bata tsorata kamar yadda Namra ta fara tsorata yanzu ba. Namra ta rage gudun motarta ta sauka gefen titi shi ma sai ya rage gudun ya sauka gefen titi ya faka gabansu.

“Ki daina dariya what if he want to kidnap us? Ko kuma wannan saurayin ne na dazu?”

Hurriya ta ji gabanta ya fadi a take ta daina dariyar, A daidai lokacin da aka bude motar wani matashin saurayi ya fito sanye da black T-shirt da wandon soja haka ma kafarsa na sanye da black shoes. Murmushin da suka gani a fuskarsa ne ya dan sanyaya musu zuciya domin alama da yanayin jikinsa be yi kama da masu aikata mummunan aiki ba. Ya iso gurinta ya duko yana kallon fuskokinsu ko wannensu da tsoro a idonsa.

“Nice race”

Namra ta dan yi murmushin karfin yana kallonsa, daga fuskarsa har hasken fatarsa be yi kama da dan nigeria ba rigar soja dake jikinsa da kuma wandon. Sai dai kafarta na kan burki jiran kawai take ta ga wani abu ba daidai ba ta taka burkin da karfi.

“Na zo na bi ku har gida sai kuma na yi gudun kar na tsorata ku”

“Yanzu ma a tsorace muke”

Yayi murmushi sosai ya shafa kansa.

“Na gani ai a idon wannan”

Ya nuna Hurriya.

“But i like it, tun da kuka fito Mall nake binku shiyasa na so na bi ku har gida in case of na yi mussing race sai na biyo na kwankwasa muku”

Namra ta yi murmushi, Hurriya kam har lokacin a tsorace take. Hannu ya saka Aljihu ya ciro karamin kati ya aje mata.

“Here is my cart duk lokacin da kika yi marmarin race just give me a call I'm Salim Sarauta aka Ethiopian nice to meet you All”

Still idonsa ya kan Hurriya da tsoro ya gama bayyana a fuskarta, ya juya ta nufi gurin motarsa ya shiga ya yi reverse ya hau titi, sai da ya kawo saiti mn gurin da Hurriya take sannan ya danna horn sau biyu. Namra ta danna ta masa sau daya murmushi yayi ya dauke kai yaja motarsa, Namra ta bi motar da kallo ta mirror ta kai hannu ta dauki katin tana dubawa kamin ta kai babban yatsanta ta shafa. It take her some minutes tana kallon katin sannan ta ja motar suka cigaba da tafiya, bata yarda baya binsu ba sai da suka isa ta faka motarta.

“Yaya Namra na fada miki account din a yanzu”

“Bari sai mun shiga ciki na huta”

“Toh”

Ta bude motar ta fita tare da ledar da suka yi siyayya, har ta isa bakin kofar falon ta tura ta shiga Namra na zaune a motar bata zare key ba sai kallon katin take, har yanzu zuciyarta bata gama yarda mutumen kwarai ne ko na banza ba, and ta kasa zaba mata tsakanin jefar da katin da kuma barinsa...

•••••
•••••
•••••

khairi ta tashi zaune da sauri tana kallon Hajiya Kaltume dake yakar hakora tana murmushi.

“Haba Hajiya ni dai gaskiya”

Sai kuma ta yi shiru.

“Ke dai gaskiya me? Kin san dai tarenmu da Hajiya Fatee ko wani dabam ta dauko ta ce ki aura ba zaki ce aa ba balle kuma danta, yaro kuma yana da nasa rufin asiri daidai gwargwado”

“Amman yana da mata fa Hajiya”

“Ina ruwanki da matarsa? Matar da uwarsa ma ba sonta take ba, kuma saboda ita ne ake son hada aurenku”

“Ni gaskiya ba zan auri mai mata ba da kurciyata haka nan, kuma yana da yara fa, Hajiya kin fa san sha'anin kishiya yadda yake”

“Ko rabuwa suka yi ba hannunki yaran zasu zauna ba, kuma muna fatar kamin ki shiga ma ita ta fita kin ga shi kenan an huta”

Ta bata fuska sosai kamar zata yi kuka.

“Gaskiya Hajiya ina da sauran time yanzu fa na gama makaranta kuma nake rayuwa”
Chapter 50 · 0% Book details