← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 159

Sashe 78

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Namra ta dan kalli gafe tana tunawa da maganarsu da Salim a jiya, and if she guess it right Salim ne bakon kenan, domin Captain ya fada mata alakarsa da shi.

“Uhmmmm wahalalle”

“Wa...?”

A tsawace Momy ta tambaya tana mata wani kallo sakaka. And that's was the moment da ta yi realize bata fayyace ko waye ba.

“Wani tunanin nake yi dabam ba Momy ba Captain ba, na isa? Haba ko hauka nake ai ba zan fara ce masa haka ba”

“Good”

Sai a lokacin Momy ta numfasa kamin ta bi miyar da Inna Shatu ke zubawa a karamin kula.

“Wa kike zubawa miya Shatu? Ko kun fara satar nin har da abinci kuma?”

“Subhanallahi, Wallahi ban taba ba, Hurriya ce idan zan zuba abinci na zuba mata  nata dabam”

“Saboda me?”

“Toh Hajiya yanzu kuma ni na ce wani abu? Sai dai ki tambaye ta”

“Karki sake raba abincin mu da ita, salon da saka mana wani abu a abinci ko kuma saboda ita ta fi wani neda za a ware mata abinci, ban da ma rainin wayo idan Hurriya ta fada miki abu sai ki yi? Waya dauke ku aiki? Babu sisin mahaifinta a cikin biyan masu aikin gidana, juye miyar nan tun wuri”

“Toh Hajiya”

Ta juye miyar ta aje kular ta fice. Anan ne Namra take bata labarin abun da ya faru tsakaninta da Hurriya.

HURRIYA POV.

Yadda ta yi spending Night and Morning dinta a dakinta haka ta zauna a dakinta har la'asar, saboda tana gudun ta sake fitowa ta sake yin arba da wani abun bakinciki, kukan kan ta sha shi kamar shi ne last hope dinta. Ta rumgume yunwa, bakiniki kuma yayi mata rumfa a zuciya, bata ji zata iya fita ba har sai da yunwa ta yi ta kawo mata farmaki ta hana ta shakat ta hana ta zaman lafiya balle kwanciyar gado lafiya.

Sai da ta hada da karfin hali sannan ta iya Sallah la'asar saboda jikin nata babu kwari ko kadan, tana sallamewa ta dauko kur'ane ta karanta suratul Kahafi ta yi addu'a ta maida kur'anen a muhallinsa sannan ta dawo gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, fuskarta har ta yi rama saboda azumin dole da ya kamata tun jiya har yau da yamma.

Siraran hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta dauko hoto ta shafa a fuskarsa saboda boye abokin rayuwarta wato kuka, sannan ta ta shafa man lebe kadan, ta tashi ta dauko dankwalinta ta daura daidai yadda zai tsaya akanta ta karya karin dankwalin da kyau irin daurin Zarah Buhari, ta sako gashin kanta data daure ya sauko a gadon bayanta hakan kuma ba karamin karawa daurin nata kyau yayi ba, ta gyara gilashinta, ba dan komai ta yi haka ba sai dan karawa kanta courage, and tana jin she deserves to live a happy life kamar sauran sa'aninta balle kuma a yau da yake rana ta musamman wato jumma'ah even though zuciyarta na cike da damuwa da kunci, kuma kwalliyarta zata boye kukan da ta yi. Bata saka talkamin da suka saba sakawa idan za su saka kasa ba a haka ta nufi kofar dakinta ta bude idonta cike da tsoron arba da Momy ko Namra, ba dan tana jin yunwa sosai ba ba zata sauko ba sai dai bata da wani zabi da ya wuce ta bawa cikinta da jikinta abun da suke bukata.

Ta dan rika skirt dinta ta dage shi kadan saboda ta samu sauka stairs din cikin jindadi, hakan kuwa sai ya bawa kyawawan kafafuwanta kuma farare fes damar bayyana. Tana hango falon da mutane gabanta ya buga da karfi, maza ne biyu da bata ga fuskokinsu ba, sai Momy da Namra dake falon, ganin babu sarki sai Allah ya saka ta cigaba da takawar without making any sound domin babu talkamin a kafarta, hakan kuma sai ya taimaka mata babu wanda ya lura da saukowarta har sai da ya rage sauran taku biyar ta sauka.

Kusan a tare Captain da Salim suka dago suka kalli stairs din dake hagu da inda suke zaune, sai dai sun samu tsabanin aje idonuwansu a mabanbanta muhalli a jikin Hurriya, Salim ya tafi kai tsaye gurin fuskarta, yayinda Captain ya fara sauko idonsa a kan zarazaran yastun kafarta sirara masu matukar kyau zuwa leg dinta slowly ya bi kasanta da kallo zuwa gurin da Salim ya dade da yada zango wato fuskarta, Subhanallahi ba zai ce be taba ganin mata masu kyau ba a duniya but Hurriya is different tana da wani sirritacce kyau mai jam hankali maza zuwa gareta, wato kwarjini yana fisgar zuciyar wanda duk yayi arba da Innocent face dinta, tun daga kan daurin dankwalinta har bakar atamfar dake da ratsin blue, zuwa gashin kanta da ya bayyana, da yadda gilashin idonta ya daidaita a fuskarta, kaf babu abun da bata yi masa kyau ba.

(Mace mai sirhirtaccen kyau ba ana nufin sai mai kyau ba, aa wasu ma ba su suka kyau ba amman Allah yayi musu kwarjinin da maza suke sonsu, balle kuma ayi sa'a kwarjin ya hadu da dan'uwansa kyau, ko kuma kudi, ko farinjini, sai namiji yayi kamar zai haukace akanki yayi ta nan da nan da ke, abu ne mai wahala ko a taron mutane ka ga an wulakanta mace mai kwarjini, ba kuma dole sai mai kudi ba, wani ko talaka ne zaku ganshi da kwarjini, wani kuma an hada masa duka, kudi, kyau, farinjini, kwarjini)

Salim ya mike tsaye yana kallonta.

“Sauko mana Hurriya”

Momy da Namra suka dago su ma dan bawa idanuwansu abincin. A take zuciyar Hurriya ta raya mata saboda ita ya zo, ko kuma saboda Yayarta Namra amman yanzu da ya ganta yake kokarin bata shirinsa, ga kuma mutumen dake kuss da shi mutumen nan ne da ta bugewa kirji a jiya har ya so ya mareta, daman kuma ya taba dandana mata zafin hannunsa dan haka bata manta ba, ga kuma Momy da Namra da bata san iya hukuncin da zata karba a gurinsu ba idan wani abun ya faru. Juyawa ta yi da sauri ta koma tana hada taku biyu uku na stairs din duk wani rashin karfi da yunwa sai suka kau a lokacin, a tafiyar da za a iya kiranta da gudu ta haye sama ta shige dakinta ta rufe ta saka key.

***    ***    ***

“Salim zauna mana”

Kamar mai jiran umarnin Captain sai ya koma ya zauna ya maida idonsa a kasa.

“Yarinyar nan fa bata shirya magana da kai ko saurarenka ba, jiya babu yadda ban lallabata ma amman sam bata ba ma saurareni ba balle har ta fahimci me nake fada”

Namra ta fada tana kallon yana yanayinsa ya can sauya duk kuwa da irin kokarin da yake na ganin ya boye damuwarsa.

Captain ya kallesa ya fara magana calmly.

“Ita soyayya ba a mata dole, idan bata ra'ayinka karka ce sai ka cusa kanka da karfi a gurinta, kuma ni ban ga wani dalili na son a biyo mace ama lallabata ta so mutum ba, ni dai har ga Allah ban ga yarinyar da zan iya yi ma wannan ba, kuma ba zan taba ganin ta ba har abada, yanzu ma saboda ka fada min da gaske kake yi kuma kana sonta sosai shiyasa har na yarda muka zo tare, amman dan ina da alaka da ita ko ba zan iya saka wani abun ba ko na hanata”

“Allah ma ya tsareka da hada alaka da wacan yarinyar”

Daga Salim har Captain kallon Momy suka yi sai dai babu wanda ya ce komai. Momy ce ta fara mikewa tsaye.

“Bari mu baku guri ku ci abinci”

Namra ta bi bayanta suka haura sama, haka Salim ya bi abincin da aka jera musu ga kuma plate din plantain da Captain ya saka hannu ya dauki daya.

“Ni zan tafi Captain, bana jin zan iya cin komai kuma sai da na ci abinci sannan na fito, ya kamata na tafi”

Ya mike tsaye tare da kallon ledodin dake gefen kujerar da suka zauna.

“Ka shigar mata da wannan”

Captain ya dan motsa baki irin na wanda ya rasa abin cewa, ya bi Captain da kallo kamin ta mike tsaye ya bi bayansa.

HURRIYA POV.

Kofar windows dakinta ta tsaya tana kallon kasa, har lokacin gabanta be daina faduwa ba arba da ta yi da Salim da kuma mutumen da har yanzu bata san sunansa ba.
Each seconds sai ta juya ta kalli kofar dakinta tana jiran ta ji ko za a kwankwaso mata ace ta fito, gashi idan Momy ce ba ta isa ta ki fitowarba, hankalinta be kwanta ba sai da ta hango fitowar Salim, ta yi baya baya kadan daga windows din gudun kar ya ganta, sai kuma ta ga mutumen da yake tare da shi a dazun ma ya fito. Da sauri ta bar jikin window din ta cire dankwalin kanta ta jefar a gado ta bude kofar ta sauka kasa ita a nufinta ta samu abun da zata sakawa cikinta kamin ta su dawo ko kuma a cilasta mata fitowa a dakin da take da niyar shiga ta rufe kanta. Ganin babu kowa falon ya saka ta taka a hankali ta leka Kitchen nan ma babu kowa, ta dawo dinning har ta fara bude warmers sai kuma wata zuciyar ta raya mata cewar za a iya ganewa ita ta ci abincin ganin ba a taba shi ba, a take ta rufe ta dauki plate daya ta nufi abincin da aka jerawa baki ta zuba white rice ce da ta ji green beans da carrots sai pepper soup din hanta da aka yanka kanana kuma aka saka kaza sai kamshi take, ga plantain da aka soya. Komai sai da ta zuna, Jin kamar motsi a sama wato stairs ya saka ta dauke plate din tana kallon stairs din ta watsa da gudu kitchen ta rufo kofar.
Chapter 78 · 0% Book details