← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 159

Sashe 65

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta fada bayan ya fice. Hurriya dai bata ce komai ba, ta cire hannunta daga taliyar tana kallon wani gafen na dabam, zuciyarta na raya mata yayanta ma yayi fushi da ita a yanzu.

WASHE GARI....

_Barka da safiya Namra, fatar kin tashi lafiya ya su Mama da Daddy, And my beautiful Young Lady, hope kowa yana kalau, a mika min gaisuwa gurin gimbiyar please_

Ta aje wayar a hankali bayan ta gama karanta sakon ta manhajar whatsapp dinta, sai ta nufi windows dinta ta bude curtains din tana kallon kasan bene zuciyarta na gabato mata da wani abu na rashin dadi da bata san dalilinsa ba.
Me yasa zata ji haka, shi ne abun da ya fara zuwa mata a rai, daman ai be ce yana sonta ba balle har tace ya koma gurin kanwarta ne. But at first alamunsa sun nuna ni yake so. Wata zuciyar ta fada mata. Ta kai hannunta tana taba karamar sarkar dake wuyanta.
Yana yawan tambayar Hurriya, amman ban yi zaton ita yake so ba, ko kuma dai ya juya kanta ne saboda ya ga ta fini kyau. Sai kuma ta juyo tana kallon dakin kamar wani bakonta sai sake sake take a ranta, wai it's normal ya so Hurriya domin be furta mata so kai tsaye ba, but why take jin babu dadi so disappointed? It's because of ta fara sabawa da shi kwana biyu, the way he approached her gashi da saka nishadi da iya kula da aika ko kuma saboda tana tsamanin ita zai ce yana so.

Ta bar jikin windows din ta nufi gurin da ta aje ledar da ya kawo ma Hurriya ta bude ledar ta ciro waya tana dubawa irin wyar Momy ce sak daga kala har model. Ta sake saka hannu cikin ledar ta ciro Perfume set masu kamshi sosai. Sai da ta shaka turare sannan ya maida komai yadda yake, ta nufi wayarta ta dauka. Ta rubuta masa.
_Bata karbi komai ba, na yi try bata karba ba, tace na aje maka_

After ta yi sending sakon sai kuma ta ga kamar be dace ta yi haka ba, but me zata yi? Ta karba da sunan Hurriya ta karba, yayi ta jiran kiran Hurriya ya ga shiru, ai kara ta fada masa gaskiya, ta jefar da wayar a kan gado tsakanin faduwar wayar da shigowar kiran Salim ba za a iya fadar wanda ya riga wani ba. Hannu ta kai ta dauka ta danna picking

“Are you free mu yi magana?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa masa.

“Eh ina jinka”

“Me yasa bata karba ba?”

Ta daga kafadunta kamar ance nata yana tsaye gabanta yana kallonta.

“Ban sani ba, maybe she's not interested, kuma bata shirya ma hakan ba, domin wani be taba nuna yana som Hurriya ba, so ina tunanin ba abu ne mai sauki ta karbi abun ba, saboda tana da banbanci da mu, tana ganin abubuwan differently”

“Amman da kika fada mata ya kika ga reaction dinta?”

“Not good... Not Bad...”

“How do you think zan iya shawo kanta”

Ta taka zuwa gaba tana shafa goshinta.

“Ina ganin kamar ba a takurawa mutum akan soyayya she's 19yrs idan tana ra'ayinka zata sani”

“Or Maybe i can talk to her by myself? Ya kika gani na fahimtar da ita abun da ke zuciyata kuma na nuna mata ba da wasa na zo nan ba, ko kuma kina ganin sai mun fara daukar permission gurin iyaye? Maybe ita ma zata fi yarda da ni”

Ta yi shiru kamar mai tunani.

“Karka yi saurin tafiya gurin iyaye, ka fara magana da ita ka ji ta bakinta, domin Appanmu baya daukar komai da wasa”

“Okay zan yi haka, zan shigo yau da dare ko na zo yanzu”

Ya lumshe ido ta bude jin yadda yake rawar jiki.

“Da dare zai fi sirri, domin bata nan jiya ta koma gurin kakarmu da zama, zan kwatanta maka gurin”

“Zan fi jin natsuwa idan muka tafi tare, and Kakarta ma zata fi daukar abun da muhimmanci, idan kina ganin babu matsala zan fara zuwa na dauke ki sai mu tafi tare”

Samun kanta ta yi ta saka bijirewa rokonsa, duk kuwa da zuciyarta ta raya mata haka, domin tana son ta cire kanta ne daga duk wani abu da ya shafe shi a yanzu saboda ya nuna ba ita yake ra'ayi ba.

“Shikenan Allah ya kaimu”

“Ameen thank you”

Ta sauke wayar tana kallon kiransa har sai da ya yanke sannan ta dauke fuskarta tare da ajiyar zuciya. Bata kara raina kanta ba sai bayan Sallah Isha'i a lokacin da ya kira wayarta ya sanar mata yana waje yana jiranta, sanin ba dan ita ya zo ba, ya saka bata cilastawa kanta shafa ko da hoda ba, balle kuma ta canja tufafi ko saka turare. Tun bayan wanda ta saka sa rana bata sake saka wani ba, mayafi kawai ta dauka ta yafa a saman gowns din atamfar dake jikin sannan ta saka shoes din da suka yi shige da atamfar. Sannan ta fito dakinta ta nufi dakin Momy, kamar jiya yau ma waya ta same ta tana yi. Daga bakin kofar dakin ta tsaya rike da kofar

“Momy zan leka waje ina da bako?”

Wani kasaitaccen murmushi ya bayyana a fuskarsa Momy, ba tare da ya yanke kiran ba ta ce.

“Haka nake so, na jiya ne ko wani dabam?”

“Shi ne na jiya”

“Yayi kyau, amman ki sake fuskar mana, ki yi far'a ba fuskar damuwa ba”

Ta amsawa Momy da kai, Momy ta kara mata da cewar.

“Make sure kuma wanda ya cancanta ne, kin san dai waye iyayenki”

Nan da kai ta amsa mata, sannan ta juya ta fice idonta na cika da hawaye a karo na biyu. A jiya ta kwadaita ma Momy cewar gurinta aka zo, saboda zatonta ne, yanzu kuma Momy ta sake zaton hakan a karon kanta. Har ta fito falon rike da wayarta a hannu bata daina fadawa kanta ajinta ya wuce ta tsaya irin wannan tunanin da damuwar akan namijin da ba shi ne autan maza ba, kuma ba ita ce a gabansa ba. A kokarinsa na karramata ya fito daga motarsa ya zagaya ya bude mata front seat, tana kusantar gurin da motar take buri na kusantota. Bude mata motar kawai da yayi kamin ta karaso wani abu ne da ba a taba yi mata ba, and to her wani abu ne dake bayyana halinsa na kula da mace yadda ya kamata.

“Barka da dare”

Kamar wanda ta fado daga wata duniyar haka ta farko daga duniyar tunaninta ta dan kalleshi and a lokacin ne ta fahimci ta karaso kusa da shi.

“Barka dai”

Ta amsa a takaice fuska ba yabo ba fallasa sannan ta shiga motar ta zauna, shi kuma ya rufe murfin motar gently, sannan ya zagaya ga shiga bangarensa, ya kalleta bayan ya rufe bangarensa yana tunanin ko zata masa wani karin bayani ko shawar before su tafi.

“Za mu oya tafiya?”

‘Da gaske umarni na yake jira? Wai duk wannan na miye ne? Meye haka? Why why?’

Ta tambayi kanta, a zahiri kuma sai ta amsa masa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba.

“Yea...”

Yayi baya da motar tare da juya kanta sannan suka fice daga gidan.

HURRIYA POV.

Hurriya na kwance jikin Hajiya Binta tana game da keypad dinta, Hajiya ta ce.

“Wato da wani gurin kika fada shi ke nan babu wanda zai biyo bayanki ya binciki lafiyarki, shi sun rufe masa ido su kuma babu wanda Allah yake ranta kowace daga ita sai Yayanta take hange”

“Haka kwanan baya suka laka min sata, Momy ta ce na sace mata sarka da kudi, kuma ban dauka ba, amman Hajiya ma cewa ta yi wai zan iya yi saboda na canja hali, Appa ne kawai ya wanke ni, da Allah kadai ya san dukan da zan sha a gurin Yayana tun da shi ne mai hukunta mutane, kuma da kowa sai ya rika kallo a matsayin barauniya”

Hajiya Binta ta daki kirjinta.

“Sata Hurriya? Sata dai sata? Ke Nafisa ta zarga da sata?”

Hurriya ta tashi zaune tare da amsa mata da kai.

“Har da cewa ta yi ba zata bari da Allah ba, amman ni dai har yanzu ban ji ance an gane barawo ba”

“lallai rashin uwa a gida kukumi ne, saboda suna ganin baki da kowa shi ne suke kwaso sharar sai ya sauke kanki, ai baki gadi sata ba Hurriya uwa da uba, yanzu da uwarki bata da rai haka mutanen nan zasu rika ki? Ke ta ce kin satar mata?”

“Sakar zinari da kudi mai yawa, har da sarkar Yaya Namra kuma ban shiga dakin kowa ba... ”

Ta fadawa Hajiya yadda komai ya faru, idon Hajiya Binta ya cika da kwalla.

“Ashe haka kike ta rayuwa cikin matsuwa a gidan nan? Duk fadin gidan nan da ma'aikatan cikinsa a rasa waye za a zarga sai ke?”

“Ai Appa ya wanke ni yace ni ba barauniya ba ce”

“Me yasa baki fada min ba? Amman ko yanzu bata bace ba”

Hurriya ta kalleta da sauri.

“Hajiya ai ya wuce”

“Be wuce ba, uwarki bata min komai ba sai alheri, Allah ya mata albarka ya bata lafiya, ta kula da ni kamar ni na haifeta, ba zan taba bari yayanta su wulakanta ba, ba zancen sata kadai ba ko wannan korar da aka yi miki ba zan kyale ba, domin idan aka kyalesu nan gaba za su aikata wanda ya fi wannan ma, gobe zan yafa mayafina na tafi duk sai na ci musu mutunci”

Hurriya ta fasa kuka da yafi kama da shagwaba.

“Hajiya Wallahi zaki ja min ne kawai ace na zo na yi minahicci”

“Uwarki bata min komai ba sai alheri, matukar ina raye ita ko yayanta ba za su wulakanta ba”

“Aa Hajiya ni dai dan Allah kar ki yi”

“Ba gidan zaki koma ba balle su ganki su wulakantaki, nan zaki zauna kuma yadda wannan abun ya tsaya min a rai idan ba amayar da shi ba ba ni da kwanciyar hankali”

Duk yadda Hurriya ta so lallaba Hajiya Binta ta hakura da maganar, bata saureta ba.

“Ni da na sani ba zan fada miki ba Hajiya”
Chapter 65 · 0% Book details