← Book details Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 159

Sashe 74

Huriyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“To na tsorata da lamarinka fa, wacan ma ana daf da daura aure komai ya lalace kuma tun daga lokacin baka sake gabatar mana da kowa ba”

“Bata min rai ta yi da yawa, taya ana daf da daura aurena zaki yi chat da wani saurayi har ya daukeki ku fita, ni fa ina da mugun kishi da zai iya sakawa na kashe mutum, bana iya daukar irin wadannan abubuwan, idan ina son mace ko kallonta bana son ayi”

Ya aje ayar maganar tare da daukar lemun da Namra ta aje masa ta sha. Momy ta yi murmushi.

“Toh Allah ya bada ta gari, yasa kamin ka bar garin nan ka samu wanda kake so, kuma ya rage maka wannan fushi idan ba haka ba zaka yi wahalar zaman aure”

“Amin”

Ya amsa yana dauke fuskarsa da murmushi tare da shan lemun a hankali. Namra ma ta yi murmushi tana taba wayar hannunta kamin ya dago ta kalleshi.

“Yauwa Captain wai a ina ka san Salim?”

Ya juyo ya kalleta.

“Salim Sarauta, abokina ne sosai tun a jami'a muke tare, ke ina kika san shi?”

Ya daga kafada tana dan zare ido kadan kamar wanda ta rasa abun cewa.

“A hanya muka hadu, ya nuna yana so na daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, shiyasa na kai shi gidan ma har ka ganshi, amman ban san me ka fada masa ba na ga yanayinsa ya canja kuma har yau be sake kirana ba”

Captain yayi murmushi kasaita murmushin dake kara masa kyauta da haiba

“Ban fada masa komai ba, maybe dai ita ta bata masa rai, na je karbar abu ne na gansu tare, amman karki sake kai shi gurinta, haka yake duk garin da yaje sai yayi budurwa, musamman idan ya ga mai kyau ce just like your sister....”

“Hum himm”

Ya dan kalli Momy kamin ta sake kallonsa dan amsa masa tambayarta.

“Ina yarinyar take ta dawo?”

Momy zata yi magana Namra ta yi karaf ta tari numfashinta ta ce.

“Eh tana dakinta”

Ya maida dubansa gurin Momy fukarsa shimfide da murmushi yayi mata godiya.

“Thank You Momy, ko wace mace ta fi daraja da martaba a gidan iyayenta ko mijinta, kuma a matsayinki na uwa daman haka ya kamata ki yi”

Ya dubansa gurin tsadaden agogon hannunsa sannan ya mike tsaye.

“Ya kamata na tafi kar na bata lokaci”

Momy dake mamaki yadda Namra ta yi masa karya ta ce.

“Nan da nan, baka wani dadewa”

“Yanayin aikin ne a haka, wai Musib har yanzu ba su dawo ba?”

“Suna da daf da dawowa, muna waya da su ai”

“Good”

Ya nufi kofar fita falon, Momyda Namra suka mike tsaye domin yi masa rakiya. Yana bude kofar da zimmar fita Hurriya ta dake rike da kofar tana murdawa da zimmar shigowa, dayan hannunta kuma yana rike da luggage ta sake naushin kirjinsa da kanta daidai saitin zuciyarsa, a karo na biyu by mistake. A take daga hannun sama saitin fuskarta. Kamin hannun ya kai fuskarta ta yi saurin lumshe idanuwanta dake cike da yalwatacce gashin ido ga kuma na gira da ya kara masa kyau a sama, ta dauke numfashinta tana jiran jin tafin hannunsa a fuskarta.

“Yarinyar bata da hankali komai a haukace take yinsa”

Kalaman Momy da kuma jin shiru babu mari babu alamarsa a fuskarta ya saka ta bude ido a hankali pink lips dinta suna motsawa kamar zata ce wani abu. Hannu ta gani a tsaye saitin fuskarta ba tare da ya kai hannun a fuskarta ya mareta, kuma be sauke hannun ba, haka zalika be dauke idonsa daga kallonta ba, kamar yadda fuskarsa take daure saboda abun da ta yi masa. Da sauri ta duke kasa ta ratsa gefenta ta shige falon har Luggage dinsa na dukan kafarsa, abun da ya kara bata masa rai. A lokacin ne ta tuna cewar shi ne mutumen da ya taba marinta.

“Yi hakuri”

Ya ta fada tana kara matsawa baya da sauri domin jin take kamar zai iya rikota yayi mata hukunci ne, gashi babu Hamad mai rama mata. Ya sauke hannu ya juyo sai dai ba ita ya kalla ba, Namra ya kalla.

“Why do you lie?”

Ta dan yi baya kadan ta rasa yadda zata wanke kanta, Momy ta kalleta sannan ta kalli Captain ta already ya fice har yana kokarin rufe kofar. Sannan ta juyo ta watsawa Hurriya harara

“Kin dawo ko? To shiga ciki ki zauna, gida kam na ubanki ne amman ikonsa nawa ne domin bangarena ne”

Hurriya ta sauke kanta ta juya tare da taja kayanta ta haye sama. After ta shige Momy ta kalli Namra ta ce.

“Me yasa kika yi haka? Namra ki daina yin abun da zai saka Captain ya tsaneki fa”

Ta dan cize baki cikin yanayin damuwa ta ce.

“Ban dauka zata shigo yanzu”

“Ki kiyaye next, domin ni ban ki kum fahimci junanku ba har ya kai ku ga aure, ko ranar da ya bar gidan nan sai da muka yi magana da Ammy, akan ke da shi, amman saboda lura da hankalinku baya kan juna ya saka ba ma son matsawa, kuma ko da babu irin wannan be kamata kina haka ba be careful...”

“I will...”

Ta amsa tare da kallon kofar kamar mai tunani, tare da saka hannunta tana taba wuyanta. Momy kuma ta nufi upstairs cikin matukar bacin rai.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
𝐊𝐇𝐀𝐃𝐄𝐄𝐉𝐀 𝐂𝐀𝐍𝐃𝐘

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

𝐏𝐚𝐠𝐞 2⃣3⃣

Tana tsaka da cire tufafinta a luggage Momy ta turo kofar dakin ta tsaya daga wajr tana kallonta.

“Mun ga sakon da Hajiya da ta aiko mana akanki, kuma mun gode ke ma kuma zaki ga irin nawa sakon, mahaifinki yayi gaskiya gidansa ni da ke duk muna karkashin ikonsa, amman nan bangarena ne ina da nawa rules and regulations, dole kuma ki kiyaye domin ba bangaren Iyami ba ne”

Hurriya ta sauke kanta ba tare da ta cewa Momy komai ba, ganin haka ya saka Momy ta bar kofar a bude ta nufi nata dakin. Ajiyar zuciya Hurriya ta sauke ta dafa goshinta.

“Allah ka kara min hakura zama a gidan nan, kowa da kallar tsanar da yake min”

Ta sake aje numfashi mai karfi sannan ta cigaba da cire tufafin ta jera a closet ta aje luggage din gefe ta cire hijab dinta ta saka talkaminta ta fito daga dakin. Ko da ta sauko babu kowa a falon kai tsaye ta nufi kofa ta bude ta fita. By this time ta san cewa mahaifinta baya a gidan sai idan wani abu ya dawo da shi ko kuma ya hana shi fita, dan haka Hajiya Kaltume uwargida, nan ma sai da ya ki bacin ranta da take ganin za a cusa mata, ta bawa zuciyarta hakuri ta danne duk wani abu da zata ji tun gabanin su fada mata, sannan ta tura kofar ta shiga. Sukan na su falon a cike yake suna ta murnar dawowar Salma, sai dai ganin Hurriya ya saka sun tsaya cak suna kallonta kamar irin wanda aka jefo daga sama daga gabansu.

“Hurriya”

Hajiya Kaltume ta fada da mamakinta karara a fuskarta.

“Na'am Hajiya ina wuni, Yaya Khairy Yayana, ina wuni yaya Salma sannu da zuwa”

Salma ta amsa tana kokarin boye munafurcinta a cikinta.

“Lfy kalau”

Yasir kuma ya ce.

“Lafiya Kalau kanwata, na jidadin da kika dawo, Hajiya kin yi abun da ya dace”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi, wani abun da ya bawa kowa dake falon mamaki ciki har da Hajiya Kaltume da ita kanta Hurriya shi ne tashin da Khairy ta yi ta koma kusa da ita ta rumgumeta tana far'a.

“Alhamdulillah, Allah ya kawar da bacin rana na jidadin da kika dawo, I'm so happy”

Hurriya ta kalleta har tana rasa abun furtawa, mamaki ya lake mata a zuciya.

“Ina taje ne ake ta murnar dawowarta?”

“Abubuwa da yawa suka faru Salma sai kin zauna zaki sha labari”

Khairy ta amsa bayan ta saki Hurriya.

“Ni ma fa ina da labarin da zan baku, kuma dukansu sai mamaki ya kama ku”

“Mamaki zai wuce ki ce kin samu wanda kike so zaku yi aure soon bla bla bla ni ma aurar da ni Hajiya take kokarin yi fa, ga Fadeel kin san shi ai dan Hajiya Fatee”

A yanzu ma Khairy ce ke amsawa Salma tana dorawa da zancen auren dake ci mata rai. Da mamaki Salma ta kalli Hajiya ta ce.

“Da gaske Hajiya? Fadeel ba yana da mata ba?”

Hajiya ta daga mata kai.
Chapter 74 · 0% Book details