← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 30

Sashe 8

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai mallam tashi da Sauri Baffah ya mike lafiya bayin Allah Mai na muku?!! Me kuke bukata? Bai gama rufe baki ba yaji sauka bindiga a kafarsa, karan da Baffah ya saki ne ta tashi Shatu da Hajjo daga barcin da sukeyi, a firgice su Mike,!!
Kuka Shatu ta fashe dashi "tana fadin shikenan sun kashemun Baffa na, toshe bakinta Hajjo tayi "kiyi shiru kar su jimu"
Tattara gaba daya dabbobin sukayi, su kai gaba dasu yayin da suka kara Harbin Baffah a karo na biyu,
Nan ya zube a gurin ba rai ba Alamanshi, bayan tafiyan sune su Shatu suka fito daga bukkan da gudu suka nufi Baffah "don Allah Baffah Karka mutu ka barni kai kadai ka ragemun a duniya" Shatu keta fadin haka tana gigiza Baffa, da kyar ya dago ya kamo hannun Shatu dana Hajjo ya hada da kyar ya bude baki "Yace ma Hajjo duk randa kika warke, kika tuna Asalinki ka yar uwanki nan ki taimaketa kamar yadda muka taimakeki bata da kowa yanzu a duniya Sai ke, ku kiyaye mutuncinku duk runtsi karku rabu da juna Allah ya tsaremun ku ya albarkaci rayuwarku,,,,!!! Maganar da bai karisu ba ke Baffah ya rasu😭😭.

Haske sun da akayi da toch light ne yasasu mikewa da Sauri dama akwai wata jaka rataye a wuyan Shatu, aikam suka rike hannu juna su ranta a na kare, aikuwa barayin nan suka rufa musu baya,,!!

"Wai Hajiya Yaya meke damunki kwana biyu duk kin rame ko duk mutuwar Alhaji Mallam din ne yake kara dukan ki"? Ke dai bari ni na rasa meke damuna Aishatu, to Allah ya yaye mana damuwa, "bari inje in Dora girki Abban su Umar ya kusa dawo wa, " to yar albrka.

"Maman jafar wai ya maganar rabon gadon Alhaji Mallam ne? "Ke dai bari ni gidan nan nakeso a raba kowa yaja katan ganshi in dai na ganin makiyan nan namu, 😀😀😀 dariya sukayi, suka tafa, "yauwa wai ya maganar komawa gurin bokan nan ne? Ki bari gobe zamu Sai a turaro shi yaron yazo kawai ayi ayi a wuce gurin wlh kuwa mu kwashi arziki,,,,!!! Dariya suka karayi "kinji inje in Dora sanwa kin san Billy bazata taba yin aikin nan ba, "wlh yaran yanzu san jiki ya musu yawa aje gidan miji ba,a iya komai ba, "Ai da sauki ma ya dauko mata yar aiki,
Tofa readers kunji tun ba,ayi auren ba ake maganar yar aiki😀
Allah ya shiryi masu hali irin nasu Ameen🙏🙏

Ku cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU don sanbado muku lbr✍️✍️✍️✍️
[6/8, 14:26] 💞FAST CLASS💕: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗

(SHATU&HAJJO UMMIMI)

WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

🌹🌹EPISODE THIRTY&THIRTY ONE🌹🌹

Kanawa yaran zazzagawa ina muku brka da sallah sai kun kawomun naman sallah don kusamu albrka na😜😜😜

Gudu sukayi na ceton rai inda Shatu ta fadi, "Don Allah yar uwa ki tashi gasunan zuwa fa, "Hajjo ki Gudu ni karfina ya gama karewa, ki Gudu ki ceto ranki ki barni su kasheni in bi Baffa, ki Gudu nace gasunan fa, "ni bazan Gudu ba sai dai su kashemu tare, "don Allah ki gudu,!! Badan Ummimi taso ba ta tashi tana hawaye tanajan Shatu, Shatu ta fisge hannunta ta turata, haka Ummimi taci gaba da gudu, barin gurin nata yayi dai dai da isowan su,
"Oga ita kadai fa ta rage kuma da,alama nunan rana ce fa za,a shana, hhhh "kai jj baka da kyaufa amma wannan yar shilan meza,a ci a jikinta, "kai Oga irinsu fa sunfi dadi fa, "kai damisa aikata inda muka aika ubanta Kaji, ita ma dayar a shiga dajin a nemo min ita, "a,a Oga kar a kashe yarinyar nan zatayi mana Amfani fa, "dob Allah ku kashe in bi mahaifina yafimun ku taimaka mun ta karasa maganar tana fashewa da kuka!!!,
"Kuma JJ ya kawo shawara tsula dauketa ka kaimun gida akwai Amfaninta, haka tanaji tana gani kato ya sabata a wuya,
Wasu suka bi bayan Ummimi.

Iya gudu tasha don kwana tayi ta gudun ceton rai, Ankira sallah Asuba yayi daidai da zuwanta bakin titi, ta zube a gurin, dai dai wani Mota ya kwasu a guje har ya wuce ya dawo baya, wani matashin saurayine ya fito a Motan bazai wuce shekara Ashirin da takwas fa daga ganin shi kasan hutu ya zauna a tare dashi, black beauty ne ga wani zagayayyen saje da ya tsagaye dogon fuskan shi yana da manyan idanuwa, da dogon hanci wanda yai dai dai da karamin bakinshi, yana da fadin kirji kana ganin shi kaga irin sadaukan mazan nan masu motsa jiki,
Da sauri ya kariso gurin sai da gaban shi ya fadi ganin ta da yayi, tattaren hannun riganshi yayi ya dauketa sai yaji kaman ya daga takarda saboda tsaban Rashin nauyinta,
Mota ya kaita ya shimfideta gidan baya ya rufe Motar ya zaga ya shiga, ya figi Motan da gudunshi,

"Yaro kasan yau Abokinka zai dawo daga jos, ya kamata ku fitar da matan Aure kai dashi gaba daya kunki Aure, Asibitin naka ma ka dena zuwa, can Makarantar ma da kake dan zuwa can zaria shima ka bari, gaba daya baka da walwala na rasa meke damunka,? Iye ka fadamun mana, "wlh Momy ni kaina ban san meke damuna ba, kawai dai jikina yana bani na rasa wani Abu mai muhimmaci a rayuwata kuma na kasa tunawa,"
"To Allah ya yayemaka damuwan yarona kayi ta Addu,a Amma nidai na kosa kuyi aure, "inshaallah Momy zamuyi, Allah yasa inga lokacin "Ameeen Momy"

Horn ya keyi a wani Kofan gate na Asibiti ba tsayawa me gadine ya zo da gudu ya bude mai gate, "Barka da zuwa maigida Ashe kazo garin ne Eh kawai yace mai figi Motan shi, tun kafin ya iso yake kiran shi bai dauka ina ya ajiye wayan ne.

Ko gyara parking baiyi ba ya fito da sauri yana kiran Nurse, Nurse!! Nurse!! Da gudu suka kariso da gadon daukan marasa lafiya, don sun san halin Oga Ammar ba hakuri, gungurata sukayi suka shiga da ita emergency, ya rufama musu baya, ba kuma wanda ya isa ya hanashi shiga yanxu ka jama kanka kora,

"Al'ameen hankalina yana tashi kwana nan na rasa meke damuna, "ki bari kawai Ummah wlh duk haka muke, ni ina tunanin rikice rikecen gidan nan da rasuwan Alhaji Mallam duk shi ke damun mu, hayaniyar dasu kajine yasa su fitowa da sauri Ashe fada akeyi da Baban su billy da matar kaninshi, "kai Umma Allah ya hore mana mu tashi a gidan na,
Rigimar Gidan Gado ya ishemu, suka juya suka shige sashin su,

Yau kwanan Ummimi biyu a Asibiti Ammar ke mata komai amma har yanxu bata farfado ba,,,,,,,,!!!

YAR MUTAN ZAZZAU NE FATAN Alheri masoyana✍️✍️✍️
[6/8, 14:26] 💞FAST CLASS💕: 💗💗💗💗💗💗
*GIDAN GADO*
💗💗💗💗💗💗
*(NEW LIFE NEW FACE)*

*WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

*🌹🌹EPISODE THIRTY TWO&THIRTY THREE🌹🌹*

*INAMA DUKKAN AL'UMAR MUSULMI BRKA DA SALLAH ALLAH YA AMSHI IBADUN MU🙏🙏🙏*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Farfadowanta kenan ta fara waige-waige to inane nan me takeyi Anan wayyo Allah Shatu na shikenan sun kasheki sun kashe Baffa tunanin da ya fara zuwa mata kenan a rai, kawai ta fashe da kuka😭,

****************************

"Momy ya kamata muje kiga yarinyar nan dana tsinto fa," Ammar ne ke fadin haka, Waigawa nayi nakai kallona gurin wata hamshakiyan mace datake zaune a kayataccen falon nasu, "My Son to yaushe zamuje,? "Ko yanxu ki taso muje ok Affan dauko mun mayafi na" "to Momy Nima zanje "Ok oya dauko muje,
"Momy ina jiranku a mota in kun shirya" "to my sweet yarona, yauwa Momy mu tafi ga mayafin to Autan Momy, sun fito suka tarar Ammar har ya tada Motan shi, su kawai yake jira suna shiga suka kama hanya sai Asibitin,

****************************

"Kunajina koh? "Eh Mallam niko nace boka dai ba Mallam ba, "in har kuka bari yarinyar nan taga wanda ta sani Asirin dake jikinta zai karye, 😲😲 "to yanzu fa Mallam ya maganar shi wannan yaro? "Muna nan muna aiki akan shi yaron nada riko da ibada ne sai munyi da gske kafin a jawo ra,ayinshi Amma muna iya bakin kokarin mu abun bazai wuce wata biyu ba, mai wuyan a shawo kanshi, Aljani dan agundi na iya kokarin sa, ku tashi ku bamu guri gafalallun bayi Asararru, wanda baku ba samu Rahma,!!!! "to mun gode Mallam sai anjima,"

***********"****************

"Aslm Alaikum"da sauri ta waigo tana kallon mutanen dasuka shigo, "Lah kaga yaya ta tashi, "aikuwa ta tashi Momy ne tayi wannan maganar, da sauri suka karasa cikin dakin, "sannu aunty Affan yace mata yana kokarin hawa gadon, "kai Auta baka ga bata da lafiya bane zaka dameta,"cewan Ammar, "sannu yarinya ya jikin,? "Alhmdulillah Hajiya naji sauki, don Allah inane nan ku suwaye,? "Ayyah yarinya ki bari ki kara warkewa tukun na, sai mu fada miki koh nan kina Asibiti ne baki da lafiya,
My son je ka kira doctor kace ta farfado, "to Momy, "Zan bika yaya, "kai Auta rigima muje to.

**********************

"Ya Allah ka ciremun wannan yarinyar a raina karamar yarinya ta hana zuciyata sukuni, Alhalin ita tama mance dani, kiran Sallah magrib ne yaji Ana kira, Amma wani Barci ne mai dadi ya daukeshi, Mubarak ka tashi lokacin sallah, Karka yi barci su samu sa,a a kanka readers ku tayani tashin Uncle Mubarak😂😂.
Chapter 8 · 0% Book details