← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 30

Sashe 19

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu Zahra tazo ta rungume Ummimi wayyo Bloodynerh yau burin mu ya cika, Mun kammala karatun mu lapiya tare da nasarori masu yawa, ji sukayi an kara rungume su, Ta bayansu juyawa gaba daya sukayi, "kai Besty kin bamu tsoro fa😂 "to sarauniyar matsorata, dariya duka sukayi, Motar su suka nufa wanda Daddy ya siya musu don zirga zirga, "Sittynerh yaufa ke zaki tukamu wlh na gaji, "ai dama na sani wlh nima bazan tuka ba, kullum ni nake tukawa, "kudai wlh kullum sai kun raba hali, gashi in mutum ya shiga fadanku ku bashi kunya, "Eh din kinji Sittynerh kawo key din zan tuka, haba mana Sittynerh kiyi dariya mana ko sai nace Autan Mamy ne kawar Hajia Kilishi, 😂kwashewa da dariya duka sukayi, ni kin san mene ke damuna ma Bloodynerh muna komawa gidan wannan tsohuwan zata taso mu gaba, gunda ma kefa, naga tana daga miki Kafa, hhhhh"wlh na lura Sittynerh kina bala'in tsoron Kilishi ni kuma banji tsoronta har hira fa mukeyi in mukaje dake inkin fita kin barni dakinta, Uhmmm "ai ke din da banne Sittynerh kinada wani kwarjini da kikema mutane kamar yadda itama Kilishi ke dashi, kai har mun iso gida Ashe, suna shiga gida, Zahra ta kira Mamy ita kuma Ummimi ta kira Momy suka fara hira, suna Basu labarin Exam dinsu, haka suka sha hiransu, wai Mamy ina Yaya Mubarak ne? Tunda fa mukazo kasar nan bai taba zuwa ya dubamu ba, kuma har yanzu ko kalan Amaryan da yaranshi fa bamu sani ba, "Uhmmm Auta ke dai kawai ki Bari Yayan ku yana bukatar Addu'a don sai muyi wata bamu sashi a ido ba, "what!!? Mamy ko gaudaku bai zuwa kenan,? "Sai ya dauro mai zaizo yayi ta bamu hkr yace bazai kara ba, shi kanshi bai san meke damunshi ba, "tab Mamy Amma wannan ba aikin sihiri bane kuwa, ya kamata ku tashi mai tsaye da Addu'a hakane Raleeyat sihiri ne kuma muna zargin matanshi ta mai, duk da ance zato zunubi, "Tab wlh Mamy muka dawo zamuje har gidan sai ta gane kuranta kuma ta karya sihiri data ma dan uwan mu, shegiya la,a nanniyan Allah kawai, to waima Mamy yar gidan uban waye ita, hala daga gidan marasu tarbiya ta fito karamin gida, duk Ummimi take wannan maganar, niko nace a,a Ummimi karki zafafa kanwarkice fa, sallama sukayi da Mami kowa ranshi a bace, musamman Ummimi da tun daga lokacin data dawo hayyacinta, taji ta tsani matar Yaya Mubarak kuma kullum sai tunanin shi takeyi, ga kuma soyayyanta da Yaya Amar jira kawai yake su dawo a Daura musu Aure, ya Allah ka kawomun mafita, bazan taba iya Auran Mubarak ba, dayana sona bazai taba Aure ba zai ta nemana ne, ya kuma jirani, Amma gashi yayi Auren shi Harda yara biyu, kuma yana sonane don sister Nusaibat data rasu, "Sitty wai tunanin me kikeyi ne tun dazu inata magana kinyi shiru, firgigit tayi ba komai Sitty na kosa mu koma gidane, karki damu jibi fa su Momy zasu zo, ranar Monday zamu yi celebrate Tuesday kuma muna gida inshaallah, muna komawa zamu sanar dasu Momy komai, daganan sai Yaya ya kaimu Zaria muga family ku mu dawo don bazasu kwace mana ke ba, ehee,

*************************

NIGERIA

Momy ne ke ta shiri yayin da Affan ke tayata, "Momy I eager to see my Aunties fa, kai Affan ne ya zama saurayi haka, "aini Affan na fika kosawa inga Baby na kaman in jawo anjima in ganni a jirgi, "tab Momy aini duk nafi ku kosawa fa, Waigawa duka sukayi, "yaushe ka shigo gari Soja Mazan fama, murmushi yayi "wlh Momy yanzun nan, ok

"Abul khairi "yes Mamy wani dan gayun yaro ne ya fito yaci Ado Abunshi, sai da na kalla da kyau naga Ashe Abokin na Affan ne, ka dauko mun hand bag dina a daki, tom Mami

Gaba daya sun dunguma Harda yaran Mubarak kasancewar Kilishi taje har gida tama Bilki kaca kaca dataji Abunda ke faruwa kuma ta kwashe yaran ta dawo dasu gidan su Mami, sai Gasu a Airport kowa ka kalla kasan yana cikin farin ciki, nan da nan jirgin su ya daga sai india, niko nace su Mamy a dawo lpy nima ina nan zuwa da yan Indian gidan mu AREWA WRITERS ASSOCIATION, Meraahenat da lashyzmeyy😜.

************************

INDIA

"Ke lashmey ki sauri fa zamuje gyaran kaine fa, ok wanda aka kira da lashmey na kalla wata yar india ce datake musu aike aike a gidan nasu Yaya Amar ya daukan musu ita sbda Abubuwa sun musu yawa,

Su Momy sun iso lafiya, kawai dawowa sukayi sukaga Su Momy a gidan, ai da gudu sukaje suka rungume iyayen nasu, wayyo zaku karyamune baku ga inda kuka zama yan lukutaye bane, kai Mamy, "Uhmmm wato ni baku ganni ba ko su Momy kuka gani, ai da gudu sukaje gurinshi, Zahra ta rungume shi yayinda Ummimi tayi birki ta kasa karasowa, bude mata hannu yayi, sai ta kale mai kafada tana mai Murmushi, haka lashmey ta jera musu Abinci kowa ya hallara har su Daddy da sukaje Sallah sun dawo, an fara cin abinci kenan sai sukaji nocking izinin shiga aka Basu Ashe Raleeyat ne, da iyaeyenta itama da kanninta, biyu duka Maza, suna shiga Falon Alhaji Ahmad ya mike a,a Alhaji ya'u, "na, am Alhji Ahmad nan fa aka fara murnan ganin juna Ashe Abokai ne, gashi sanadiyan yaransu sun kara haduwa, nan hira ya barke tsakanin Family suna cikin farinciki,

Washe gari ranar celebrate din su Hall ne ya Amsa sunansa Hall inda kowa ka gani a gurin dan wanine, taro yayi taro inda aka fara gabatar da taron anyi presentation anyi debate kusan kowanne da Nusaibat inda ta samu manyan kyaututtuka ita da Zarah, Anan ma gwamnatin india ta daukeso aiki a babban Asibitin New Delhi in suna so saboda kwazon su, kyauta ko har sun rasa ina zasu sakashi, duk inda aka juya daukan su akeyi a pic ana watsama duniya, bayan angama komai Ummimi tayi kukan farin ciki bata taba tunanin zataje wani kasa karatu ba, Balle har ta samu irin wannan daukakan, ba, abun dazata cema su Momy sai dai Addu'a don bazata taba biyansu abunda suka mata ba,

Washe gari suka shirya sai Nigeria kasarmu ta gado kowa ya bar gida gida ya barsa, sun iso Nigeria karfe takwas na dare, Driver ban gidan Hajia Kilishi yazo ya daukesu sai gidan Hajia kilishi.

*************************
Tom kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU kuji yanda zata kaya..✍️✍️✍️✍️

Share
Vote
Comment
Please ✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
*GIDAN GADO*
💗💗💗💗💗💗
*(OUR COUNTRY)*

*WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.*

*🌹🌹EPISODE FIFTY TWO&THREE🌹🌹*

*Wannan page din sadaukarwa ne ga duk wata mai suna (ZAINAB) Ina matukar son sunana I love my Name😂🙈*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.*_

"Yahaya wannan ba Ummimi bane,? Wai ina ma take ya akayi taje kasar India karatu, to wai ma ya, akayi duk muka manta da ita a Family din mu, da sauri suka fita don zuwa sashin Hajiya yayah, kadan ya rage suyi gware da Habibu lpy Na ganku haka? "Ai kai zamu tanbaya lpy, "kunga Abunda na gani kuwa Ummimi ya'ta na gani a TV fa ya akayi ta tafi meyasa muka manta da ita Wai, "nima tanbayar da nakeyi ma kaina kenan fa, mu karisa gurin Hajia Yaya suna shiga dakin Hajiya yayah suka tarar da ita tana zagaye dakinta, "lpy Hajia? Da sauri ta waigo, "Yauwa Jibrin dama ina shirin nemanku ne da fatan kunga abunda na gani a TV? Lokaci yayi da kowa zai san Abunda yake faruwa a gidan nan, Jikata mafi soyuwa a gidan nan aka ma Asiri ta shiga duniya, aka mantar da kowa a gidan nan game da ita, sai ni Kadai, da komai ake shiryawa a gidan nan akan idonane da kunnina, tunda Ummimi ta bar gida har yau ina bibiye da rayuwar datake ciki, na tabbatar ta fada hannu na gari, naki daukan matakin komai ne sbda na Bari Allah yayi ikonshi akan makiya, sannan su san cewa zakarar da Allah ya nufa da chara ko Ana mazuru Ana shaho sai yayi, Burin Ummimi ya cika zata dawo gidan nan kwanan nan a Matsayin cikakkiyar likita, A lokacin Mahassada zasuyi kuka da idanunsu kuma su tona Asirin su kowa ya sansu, Abunda nakeso da ku yanzu kar wanda ya tada Maganar Ummimi a cikin ku, a cigaba da tafiya a haka, har Allah ya nuna mana ranar da Ummimi zata dawo gidan nan, "Insha Allah Hajia haka za, ayi mun gde juyawar dazasuyi kawai ganin Mama sukayi a bakin kofa ta durkushe tana kuka a gurin da sauri Hajia Yaya ta karaso gurinta, ta dagota ta rungumeta, tana rarrashinta, Guggo tsohuwa a tsaye a bakin kofa ita ma ta hawaye, "Ashe Nusaibatu Halin da muke ciki kenan Allah mun gode maka, kiyi hakuri Aishatu haka Allah ya tsaramuki naki rayuwar kin taso cikin Ahalin da ba naki ba har kin hayayyafa, har yanzu bamu samu wani lbr da zai bayyana Ahalinki ba, sai gashi tarihi ya maimaita kansa akan diyarki, Amma Alhmdulillah ita gashi zata dawo garemu cikin farin ciki, kukane yaci karfin Mama ta kara rungume Guggo tsohuwa "ni banda kowa da ya wucemun ku, kune Ahalina bandaku ban san kowa ba, kice Uwata Allah ya ji kan Babana Jibo ya nunamin gata na duniya, shiyasa kullum nake mai Addu'a Allah yaji kanshi, duka suka Ansa day Ameen gaba dayan su,

*************************
YOLA

"Kut Innalilahi wa Inna ilaihir raji'un wannan ai Ummimi ce kuma wa'innan mutanen ai yan gidan su Mubarak ne, meyake shirin faruwa damu ne dama bata mutu ba mun shiga uku, wayyo Allah na, da gudu tayi hanyar Bedroom dinta zata dauko phone nata, jitayi tayi karo da mutum, "kai Baby yaushe ka dawo, wani kallon tsana da yayi mata sai da hanjin cikinta ya kada...

*************
Tofa kodai kodai kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU ✍️✍️✍️✍️

Share
Vote
Comment
Please 🙏🙏🙏
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗

WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

________________________________
Chapter 19 · 0% Book details