← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 30

Sashe 27

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sun isa sunje sun tarar da Zahra a can gidan ita ma an kaita bayan sunci Abinci sun huta, daki daya aka ware ma Amare wannan umarnin kilishi ne, "Sittynerh buri ya cika an Auri Yaya Mubarak, 😜harda wata ta fara ciwon so, "Naji din naga wata ma hakane ta gama jan ajin Ana so Ana kaiwa kasuwa, ita dai Raleeyat dariya ta musu Nidai bana cewa komai nasan ina cewa yanzu za, a gwasaleni, dariya gaba daya suka kwashe dashi ai ke yanzu Auntyn mu ce, slmar da akayi shi ya katsemusu hiran da sukeyi, Aunty Adama ne ta shigo ita da wasu mata su biyu shuwa, Arab ne matan "yauwa ga Amaren nan yanzu yau zaku fara aiki ko sai gobe, "ai Hajiya tun yau ya kamata a fara sbda bamu da isashen lokaci, "ok to shikenan yan zu ko akwai abun da kuke bukata? "Eh to in ma muna bukata zamuyi mgna sannan akwai hadin kajin nan da yake kitchen din Hajia Kilishi a dauko mana da wani jarka da tsimi a fridge dinta, "ok to bari a kawo muku, dayan zama tayi ta fara kwaba dilkan da zata musu Anfani dashi ita kuma dayan ta shige toilet din dakin don hada musu ruwan dazasuyi tsarki dashi da wanka yaji turaruka Kala Kala, a ranar sai da suka kai sha biyun dare Ana abu daya a shafa wancan a goga wancan a turara wancan su ci wannan su sha wannan,

Washe gari nayi aka Dora a inda aka tsaya, Ana cikin musu turaren tsuguno ne sai ga Hajia Kilishi ta shigo ita da Hajia Yaya, "kai Masha Allah Aikin ku na kyau sosai ina sun da an kaisu ne inji Sakon kyautar mota Daga mazajen su, su Momy dasu Aunty Adama suka sa dariya sai Hajian mu, "ato ai gskya na fada, suko gaba daya kunya ma ta Basu, "yauwa mai gyara a gyaramun jikokina da kyau komai yaji zam zam fa, "to Hajia baki da matsala to shikenan fita sukayi dukan su aka bar Amare da masu gyaran jiki suna cigaba da Aikin su,
Kasan cewar gaba daya Hajia Kilishi ta Anshe wayar Amaren, haka angwaye sukayi ta zarya ta hanasu ganin Amarensu,

"Yauwa Aminullahi munyi magana da mahaifinka yace mun Business ka karanta to shine da nake so zan bude kanfani ne anan kaduna nake so ka dunga kulamin dashi, tunda kaga Shi Amar Aikin soja yakeyi duk ya kosa ya ajiye Aikin nan, sbda haka Yanzu ya kake gani? Already dama an riga an gina kamfanin kawai ma, aikata za, a dauka, shine nakeso in danka Amanar kamfanin a hannunka, "Insha Allah Daddy ba matsala Allah ya tayani riko, Ameen ya Allah Kai kuma Mubarak tunda yanxu hankakinka ya dawo jikinka sai kayi kokari kai da matarka ku farfado da Asibitinka, "insha Allah Daddy, "yauwa Aminullahi ga wannan takardun gidane dana baka halas a Malali quarters dake kaduna Allah ya baku zaman lpy, Kai kuma Mubarak kaine Babba ga Makullin naku gidan nan kai da dan uwanka kowa da part dinshi, in ya zo sai su dunga sauka shida Matarshi, Allah yayi muku Albrka gaba dayan ku ya baku Zuri'a na gari, sunkuyar da kai sukayi hadi da cewa Ameen ku tashi ku tafi, "uhmm Daddy nace ba wai yaushe za, a bamu matan mune,? "To Nidai ban sani ba kuje ku tanbayi mutumiyarku kilishi, dariya dukansu su kayi harda Daddy, "Amar ne yace wlh Daddy tsohuwan nan fa ta cika kofsi ta bamu matan mu kawai ta wani hana mu Sai anja mana rai, "gidan ku Amar kai rasa kunya ko dariya su Mubarak suka Kama yi mai.

*************************
"Dan uwa lpy? "Ka bari kawai wlh dan uwa kwana biyu inata mafarki da Umma ne tana kirana da in taimaketa, gashi Abba ya hanamu mu nemeta, kawai sai ya fashe da kuka, rungumeshi Umar yayi yana lallashin shi, Insha Allah za, a ganta kayi hkr dan uwa taso muje, mikewar dazasuyi suka ga Baffa Jibrin shima kukan yakeyi "Jafar kaje na baka izini ka nemo mahaifiyarku, Amma ka sani cewa ni na saki Habiba bazan iya Kara zaman aure da ita ba, yana gama fadin haka ya juya da sauri ya tafi,

Bayan sati daya da bikin Su Ummimi Billy ta koma makaranta dama bata karishe secondary dinta ba, ta kuma shiga islamiyan bayan layin su,
Duk da in tafi an dunga nunata kenan Ana gulmanta wasu har gabanta ma suke zuwa su yaba mata mgna suyi gaba, duk ta rame ba wani sauran gayun nan da iyayin da take dashi, gashi dangin Umman duk sun yardasu, Kakan Sune ma da take lekowa tace anga Habiba to yanzu ta dena zuwa, su iklymsi kuwa dama sunyi auren su sun Auri masu rufin Asiri suna zaune lpy a gidajen su,

*************************

Yau kwanan su Zahra Ashirin da shida da Aure in ka gansu bazaka ganesu ba sbda tsananin gyara da suke sha, duk inda suka zauna kanshi ne ke tashi, Kilishi tace sai randa suka cika kwana talatin zata mika ma kowa matarsa sunyi zarya har sun gaji ya hanasu ganin su,

Su momy suka fitar da ankon Dinner dana Mother day da zasuyi da Hajia Kilishi da Amar ma sunce A barshi, su Momy suka dage sai anyi anfito da Anko Kala biyu da Material da lace duk wanda suka Amsa sunan su, Ankon ka shine pass dinka na shiga gurin Dinner, to inasu sister Adama da Sister Nafeesat da Maman Ahmad da takwara da Fatan kunji da duk yan gidan gado fans sai ku tanaji anko Don musamu mu isa gurin Dinner kar a hanamu shiga.

Don jibi za, ayi Dinner washe gari kuma mothers Day hade da walima, sai a mika Amare dakinsu.

**************

Kuyi hkr da wannan wlh kaninane ba lhy muna Asibiti dashi tun jiya har yanzu bai farfado ba Allah ya baka lpy ya tashi kafadunka Ameen ya Allah.

Share

Vote

Comment

Please ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(DINNER 💞💞)

WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

🌹🌹EPISODE SIXTY EIGHT&NINE🌹🌹

"Wayyo Allah na Ummu ki dagota mu tafi asibiti karta mutu su likitocin Basu jin tsoron Allah ne, da gudu ta fito kofar gidan su ba kowa a layi can ta hango wani makocin su ya gunguro mashin din shi, da gudu ta karisa kusa dashi don Allah mudi ka taimakemu Rabin raina zata mutu ciwonta ya tashi, da sauri ya saki mashin dinshi ya bita tarar wa yayi Ummu na ta tofa mata Addu'a ita ko ba abunda takeyi sai kukan wayyo kafanta ku ciremun kafan in huta Ummu please zan mutu Ummu, kamata sukayi suka fito da ita kofar gida don tafiya da ita Asibiti da sauri Sumayya tayi hanyar bakin titi don taro abun hawa, rikita rikita kenan wai shin mai ke damun yar uwar Sumayya to meye ma asalinsu to ina zasu samu kudin kaita asibiti shin Mudi zai taimaka musu ne,? Wadan nan Amsoshi naku duk yana cikin Sabon Novel Dina mai suna 💞💞WAZAN AURA💞💞karki sake ko ka sake a baka lbr yana nan tafe nan bada jimawa ba, kudai kucigaba da bin yar mutan zazzau.
Chapter 27 · 0% Book details