← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiyata!! hajiyata!! Kinga Yaya umar koh!! Wannan wani irin kirane ummimi kike mun iye? Hajiya ke fitowa daga kicin din dake cikin falon su,da gudu ummi ta karasa bayan hajiya ta boye yayin da Yaya umar ya shigo da wani bulala a hannunshi,Yana huci to zalumu me Kuma yau ta maka? Haba hajiya wlh duk ke kike Kara lalata yarinyar nan, jafar fa taje take ma rashin mutunci don ya rabata fada da bilkiki,Ace ita Bata da hkr sau nawa Zan gayamata ta dena kulasu ko sun tsokaneta iye yarinya ta zama jarababbiya da kowa fada wlh mudai ba haka mamah take ba,haba umar ya Isa haka ka wani tasamu a gaba kana ta wani Mana masifa,nine nan nace duk Wanda yayi mata ta rama ehe in batayi ba ai Allah ya tanbayeta sunana fa taci,kasan Nima ba,a tabani na kyale, ita bilkikin sa,anta ne sun raina mun ya' don sunganta haka to wlh su kiyayen mun yarinya zanje har sasan iyayen nasu ehe,in musu kashedi akan ummimi Zan iya batawa da kowa,hajiya kiyi hkr,rabu Dani guggon Yara,shi Kuma ya kwaso tsawo kaman falwaya zaka dakan mun ya mare kishin Yar uwanshi,shi Mai ya hana jafarun ya biyota ya bigetan iyeh Kaine mara kunya😏,ummimi fito ya tabaki mu gani fito wa ummimi tayi Tana Mai gwalo🤪,kutt hajiya gwalo 🤪 take mun tayi din🙄tun ba yau ba Naga alama baka kaunar ummimi to ka fita idona in rufe,Hasbunallahu wani'imall wakeell hajiya taya zakice ban son kanwata,uhmmm fice Mana a falo,ai ko baku ce ba dama Zan fita,ke Kuma wlh mama zataji,kwalla Kara ummimi tayi wayyo hajiyata ya rankwasheni,wai Inna fito sai ya karya ni,au haka kace Ina muciyan nan barni da ja'iri😂😂😂da gudu ta bishi ya gudu Yana dariya,😃😃😃, wooh hajiyata kinayi ina jin dadi,inji ummimi,dawo tayi tana haki dan banza kawai ummimi na ta kunshe dariyar dayake cinta,yaki dannuwa ta kwashe da dariya hajiyata kin iya gudu kuwa,dakuwa ta mata ke Kuma ki dinga Zama suna rainaki wlh sai kin sani iyayenki kawai nace ki raga ma a gidan nan kinji ai, naji hajiyata Allah ya barmun ke,
Aslm a,a Alhji mallam barka da shigowa, uhmmm ummimi ne ta tashi tana turo baki zata shige daki,haba Amaryan tawa zo Mana har yanxu fushin ake da maigidan,uhmmm ni wlh na fasa auren ka,Kuma mun bata, shikenan muma wlh mun huta bamu ba kishiya inji guggon Yara da take fitowa kicin da ruwa a jug don kawo ma Alhji mallam,au ma haka kikace,to kinji fa amarya kinaso a fan mu a ranane? Zo kiji wani albishir Mai dadi,dawowa tayi tazo ta zauna kusa da kafan mallam Alhji gani to gayamun,yauwa amaryan nawa,kin San meye ki yi murmushi kinfi kyau,in bakiyi murmushi ba bazan fada Miki albishir din ba,😊ta fara Ina jinka angona yauwa amaryan ko kefa,dama mun gama magana da iyayenki da kannina akan maganar makarantan ki sun amince Amma Zaki zauna ne a gidan guggon ki zuwaira, Alhmdulillah tsalle ta tashi tanayi ta je ta rungume guggon Yara 💃💃ngde Alhji mallam dina,ki gode ma takwaranki, yauwa Ina ummimi na,am,gobe kawun ki kabiru da sama'ila zasu soba don yin magana da mijin guggon naki inya amince, Inshallah ma zai amince inji guggon Yara,ai Yana da kirki sosai,hakane kam,
Sai magana na gaba ummimi na yarda dake nasan tarbiyan da kakanki ta baki,kinsan Kuma daga gidan dakika fito,ki tsaremana martaban gidan mu,in har kika aikata abunda bai dace ba gidan mu da zur'armu za,a zaga,ki sani kece yarinyar mace ta farko da kika fara karya kadarin gidan Fulani tun iyaye da kakanni,Ina fatan ki gina tarihi Mai kyau, ummimi kina da masoya da makiya a duniyar nan har ma a cikin Yan uwanki, ummimi ke yarinya ce Mai shiga rai tun kina karamanki,shiyasa duk cikin jikoki na ba Wanda nakeso kamarki, umimin kirike addinin ki duk da nasan bakya Wasa da ibadat, kirike addu'oi Allah ya Miki albrka ya baku miji na gari Ameen kakana ngd inshallah bazan baku kunya ba,sai na ba makiya da mahssada kunya, yauwa amaryata Mai hankalin manyan mutane,tashi kije ki kiramun takwaran naki,yau sarautan ya motsane baza,a fitomun sannu da dawowa ba,😊 ai na wakilcetane,hakane fa,tashi tayi ta shiga dakin Kaka Tana xuwa ta rungumeta hajiyata burina ya kusa cika nayin karatu mai zurfi,da gske ummimi na wlh kuwa hajiya mallam Alhji sun amince zanje makaranta ngd sosai masoyita ban San abunda Zan sakamiki dashi ba Ina sonko sosai Allah ya karamiki lpy da nisan kwana, Ameen Yar lelen hajiya,

Mama dama maganar makarantan ummimi ne yanxu muka dawo karbo mata admission,sannan su baba kabiru sunyi magana dashi mijin zuwairan ya amince,yanzu registration ya rage da dunka uniform sai Dan siyayyah daza,a mata,to Allah yasa albarka,ya shiryamun ku gaba dayanku da dukkan musulmai Ameen maman mu,Bari inje kasuwa in samu in karasa dinkunan da nake dashi,to a dawo lpy Dan albrka,

Cikin lokaci kankani magana ya zagaye gida cewa ummimi zata makarantan kwana, Alhaji mallam ya amince,masu zagin Alhaji mallam suna anyi rashin adalci nayi,wasu Kuma suna ga hakan wani cigaba aka samu suma nan gaba yaransu zasuyi, hakan ya kasan ce sashin su bilki Yaya tijjani ya shigo yake gaya ma mahaifiyansu uhmmm ayi dai mu gani,in rashin adalci abunyi ne, wlh bilki itama sai tayi makarantan kwana nan,Niko nace hassada ga Mai rabo taki,,

Ina yinka Dan tsoho Hussaini 8tk irin sosai dinnan ka shekara one five😂😂😂😂

Zeeeyterh ce✍️✍️✍️✍️✍️
[6/8, 14:26] 💞FAST CLASS💕: 💗💗💗💗💗💗
*GIDAN GADO*
💗💗💗💗💗💗
*(EXAM TENSION)*

*WRITTING BY ZEEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.*

بسم الله الر حمن الرحیم
الهم انی اسعلک علم نفع و رذق طیب و عمل متقبل🙏🙏

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*🌹🌹EPISODE SISTEEN&SEVENTEEN🌹🌹*

kuyi hkr jina shiru kwana 2 da kukayi sister na ce bata da lpy muna asibiti,sai yau akayi dis_charge namu in sha Allah yan zaku dinga jina sosai ngd,🙏🙏

Guggo dama maganar komawa hostel ne dana ce miki ina so in koma don inji dadin karatu a can,to ummimi yaushe ne yaushe ne kike son komawan? dama gobe friday nakeso na koma tunda kinga monday za,a fara exam,ok barin Abban iro ya shigo zan fada mai, to ngd mami.
zan shiga makota barka ki karasa girkin can,sai kin dawo.

yankan albasa takeyi tana bin karatun kur,ani datasa a wayanta kawai jin mutum tayi ya rungumota ta baya, ihu tayi iya karfinta tana kiran mami,ke matse mata baki yayi, ke nice fa baby zaro ido tayi hadi tureshi cikin masifa da takaici ta fara fadin haba yaya iro kasan ba kyau hakan, please karka karamun irin haka haba ummi zan dan gaisa da ajiya nane kullum sai sun tsokalemun ido yana fadan haka yana kara matso ta, tana kara matsawa nifa yar uwarka ce yaya iro karka batamun rayuwa ni yarinyace karama please yaya iro haka rungumota yana kokarin daukanta zuwa dakin shi,tana dukanshi da yakushin ship, amma bai sauketa ba ya fito falo dauke da ita, dai dai lokacin mami tayi sallama cikin falo,,!!daskarewa mami tayi a tsaye me idanunta suke gane mata iron ta ke shirin lalata mata yar dan uwa a cikin gidanta,sauketa yayi da gudu ummimi taje ta rungume mami tana kuka kaman ranta zai fita,zuwa yayi zai wuce ta gabanta wani lafiyayyun mari mami ta sauke mishi, cikin fushi take nuna shi nayi danasanin haihuwanka iro kanwarka,!! akuyan cin naka har ya kai haka iroohh bar gidan kafin inkusa kashe wlh!!!
Kiyi shiru ummimi na don Allah wannan mgnar ya zama sirri a tsakin mu ni dake please umimi karki fadama hajiya yaya na miki alkwarin hakan bazai kara faruwa ba kinji yata? eh naji guggo insha Allah.
washe gari ummimi ta gama hada duk abunda zata bukata ta fito sai ga mami ma ta fito da mayafi a hannu, muje ko, to mami suna isa school raleeyat na zuwa taryan su, gaida mami tayi, mami ta ansa tana kallon raleeyat tayaba da hankalin yarinyar hakan yasa ta kara amincewa da zaman ummimi tare da ita, har hostel din sai da taje ta ga inda yar ta ta zata zauna sannan ta kara musu nasiha su kula da kansu, suyi abunda ya kawo su, insha Allah mami sai na dawo haka mami ta tafi tana kewar yarta,
fita sukayi domin su debo ruwa, uncle mubarak da uncle Aliyu suka gani sun shigo school din a motan uncle mubarak din shi yake driving din,har su sun wuce sai yayi revers ya dawo ke ku kawomun ruwa a gida banda ruwa,,!!!raleeyat ne jikin ta na rawa ta ansa da to,ita ko ummimi banza tayi dashi ke i am talking to you kinyi shiru,sir na amsa ai tana murguda mai baki ta juya,kawai samun kanshi yayi da murmushi😊 kawai uncle Aliyu sakin baki yayi yana kallon shi imaging abunda zai sa mubarak dariya, anya yarinyar nan uhmmm tafiya sukayi sukuma su ummimi sukayi gaba diban ruwansu,sai da suka yi guri sahu biyar gidan uncle mubarak,sannan su ka wanke mai toilet suka gyara mai gida sannan suka debo nasu,ranar ba karamin gajiya sukayi ba,gashi duk aikin nan dasuke mai yana zaune a falo yaki fita,haka suka koma hostel a galabaice ranar ko iya zuwa karban abinci basuyi coonflex suka shabbier,
besty besty ki tashi muyi karatu,uhmmm kai besty ki bari sai asuba,no kin san dai gobe karbe takwas muke da exam, kuma kin san baki iya calculation din physic dinnan ba kuma zai iya fito mana a exam,haka ta tashi suka dunga karatu har saida ta tabbatar sun gane sosai sannan suka kwanta,asuba nayi sun dauki bucket zuwa masallaci daga nan su debo ruwa,sun ajiye buckets din ruwansu a bakin fanpo suka shige masallaci,bayan idar da sallah sukayi azkar suka danyi karatun kur,ani, bayan gari yayi haske suka zo fanpo don su debi ruwa su Afra suka tarar a gurin suna diba sai suka koma gefe suna jiran su gama, bayan sun gama suka dauki ruwan su zuwa hostel duk da su afra sun takalesu amma basu kulasu ba,sbda raleeyat tayi iya kokarinta na ganin kawanta bata kulasu ba,
Chapter 3 · 0% Book details