← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 30

Sashe 20

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(OUR COUNTRY)

WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

🌹🌹EPISODE FIFTY TWO&THREE🌹🌹

Wannan page din sadaukarwa ne ga duk wata mai suna (ZAINAB) Ina matukar son sunana I love my Name😂🙈

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

"Yahaya wannan ba Ummimi bane,? Wai ina ma take ya akayi taje kasar India karatu, to wai ma ya, akayi duk muka manta da ita a Family din mu, da sauri suka fita don zuwa sashin Hajiya yayah, kadan ya rage suyi gware da Habibu lpy Na ganku haka? "Ai kai zamu tanbaya lpy, "kunga Abunda na gani kuwa Ummimi ya'ta na gani a TV fa ya akayi ta tafi meyasa muka manta da ita Wai, "nima tanbayar da nakeyi ma kaina kenan fa, mu karisa gurin Hajia Yaya suna shiga dakin Hajiya yayah suka tarar da ita tana zagaye dakinta, "lpy Hajia? Da sauri ta waigo, "Yauwa Jibrin dama ina shirin nemanku ne da fatan kunga abunda na gani a TV? Lokaci yayi da kowa zai san Abunda yake faruwa a gidan nan, Jikata mafi soyuwa a gidan nan aka ma Asiri ta shiga duniya, aka mantar da kowa a gidan nan game da ita, sai ni Kadai, da komai ake shiryawa a gidan nan akan idonane da kunnina, tunda Ummimi ta bar gida har yau ina bibiye da rayuwar datake ciki, na tabbatar ta fada hannu na gari, naki daukan matakin komai ne sbda na Bari Allah yayi ikonshi akan makiya, sannan su san cewa zakarar da Allah ya nufa da chara ko Ana mazuru Ana shaho sai yayi, Burin Ummimi ya cika zata dawo gidan nan kwanan nan a Matsayin cikakkiyar likita, A lokacin Mahassada zasuyi kuka da idanunsu kuma su tona Asirin su kowa ya sansu, Abunda nakeso da ku yanzu kar wanda ya tada Maganar Ummimi a cikin ku, a cigaba da tafiya a haka, har Allah ya nuna mana ranar da Ummimi zata dawo gidan nan, "Insha Allah Hajia haka za, ayi mun gde juyawar dazasuyi kawai ganin Mama sukayi a bakin kofa ta durkushe tana kuka a gurin da sauri Hajia Yaya ta karaso gurinta, ta dagota ta rungumeta, tana rarrashinta, Guggo tsohuwa a tsaye a bakin kofa ita ma ta hawaye, "Ashe Nusaibatu Halin da muke ciki kenan Allah mun gode maka, kiyi hakuri Aishatu haka Allah ya tsaramuki naki rayuwar kin taso cikin Ahalin da ba naki ba har kin hayayyafa, har yanzu bamu samu wani lbr da zai bayyana Ahalinki ba, sai gashi tarihi ya maimaita kansa akan diyarki, Amma Alhmdulillah ita gashi zata dawo garemu cikin farin ciki, kukane yaci karfin Mama ta kara rungume Guggo tsohuwa "ni banda kowa da ya wucemun ku, kune Ahalina bandaku ban san kowa ba, kice Uwata Allah ya ji kan Babana Jibo ya nunamin gata na duniya, shiyasa kullum nake mai Addu'a Allah yaji kanshi, duka suka Ansa day Ameen gaba dayan su,

*************************
YOLA

"Kut Innalilahi wa Inna ilaihir raji'un wannan ai Ummimi ce kuma wa'innan mutanen ai yan gidan su Mubarak ne, meyake shirin faruwa damu ne dama bata mutu ba mun shiga uku, wayyo Allah na, da gudu tayi hanyar Bedroom dinta zata dauko phone nata, jitayi tayi karo da mutum, "kai Baby yaushe ka dawo, wani kallon tsana da yayi mata sai da hanjin cikinta ya kada...

*************
Tofa kodai kodai kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU ✍️✍️✍️✍️

Share
Vote
Comment
Please 🙏🙏🙏
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
( MY DECISION)

WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

🌹🌹EPISODE FIFTY SIX&SEVEN🌹🌹

Wannan page din na sadaukar dashi ga duk wani Masoyin Novel dina GIDAN GADO, Allah ya bar kauna.

Cakume Billy Zahra tayi "wlh Yayana ya mutu kema Sai kin mutu, "dallah malama sakeni!! Kilishi ta ce a debo mata ruwa a cup, bayan an debo ta zauna tayi Addu, oi a cikin ruwan, ta mikama Momy datake ta Kuka, tace Amsa ki yayyafa mishi ku dago shi ku bashi ya sha ku tabbatar ya wuce mai cikin bakin shi, sbda tabbas jikin yaron nan akwai sihiri, kuma yarinyar can ita ce makarin sihirin shi, na sha gani a barcina, Billy komawa tayi gefe ta rabe ba, abun da take Sai aikin kuka, tasan Zamanta da Mubarak ya kare shikenan gashi bata san yanda zatayi ta samu Umma ba,
Bayan An yayyafa mai ruwa ne, ya dunga jera Atishawa can kuma ya fara Wani bakin Amai, hade da wasu mulmula mulmulan Abu a cikin Aman, duk Hankalin su Momy gaba daya ya tashi, Kilishi tace musu kar ku damu sihirin dake jikinshi ne yake fita, ya kusa Awa daya yana Aikin Abu daya, ya wahala sosai daganan Sai wani barci mai nauyi ya daukeshi, su Daddy suka daukeshi aka gyaramai jikin shi, su kai shi daki, kowa ya kama gabanshi aka bar Billy a gurin ba wanda ya Kara bi ta kanta, ina shiga daki na fada gado na fara kuka sbda ganin Billy da Uncle Mubarak yau ya Kara tunamin komai na rayuwata, ina Mamana da Hajia Yaya wani hali suke ciki, dole zanzo in bar family nan don bazan taba iya Auren wanda ya Auri yar uwata ba, bawai zan butulce musu bane ko inki musu biyayya bisa hukuncin da suka zartar a kaina ba, yaya family na zasu dauki maganar Mijin Billy nake Aure da wani ido zasu kalleni, kai Ina bazan iya ba, Zahra ne ta shigo dakin, ta dafa ni, "don Allah Bloody kiyi hkr komai ya faru da bawa mukaddarine ga Ubangiji kiyi hakuri mu rungumi kaddaran mu, nasan bakyason dan uwana, Amma karkiga laifin dan uwana ba yin kanshi bane, wlh dan uwana na sonki sosai,
Karfe hudu dai dai, a lokacin ne kuma Yaya Mubarak ya farfado, da sauri Amar ya tashi ya rikeshi, yayin da Billy itama ta taso da saurinta, "dallah malama karki tabamun dan uwa muguwa kawai, wlh Sai Allah ya ma dan uwana sakayyah, sannu kaji besty, binshi da kallo yayi, da kyar ya bude baki, yace mai Besty taje na saketa saki biyu in ta sami miji tayi Aure, ban san ganinta ta cutar dani a rayuwa ta rabani da komai nawa, ta rabani da wanda nafi so a rayuwata, "wayyo Allah na shiga uku Baby kayimun rai wlh bazan iya rayuwa ba kai ba, don Allah kayi hkr kar muyi haka da kai ka taimakeni "dallah!! Malama ki fita daganan yace ya sakeki ko dolene Auren kudi ya jefo mata dauki kiyi na mota, "to yarana fa? "Oh dama dasu kikazo iyeh bar nan gurin kafin in karyaki, da gudu ta fito, yayin da Ummimi ma ta juya da sauri ta shige kitchen ta Kara rushewa da kuka, wai yar uwanta ake ma kurar kare, tabbas tare zasu tafi, Indai ta tafi itama anjima zata kama hanyar Zaria,

Bayan fitowan Billy, can gidan su ta koma, Amma mai gadi kiri kiri ya hanata shiga, Sai dai Akwatin kayanta da ya miko mata, yace umarnine daga oga yace kar a barki ki shiga gidan, "hauka cemai tayi ta dunga buga gidan wlh Sai ka budemun gidan Ubanka ne, dazaka hanani shiga iyeh? Shidai mai gadi shigewa yayi ciki ya maida get ya rufe, ya barta anan da ta gaji taja akwatin ta tayi tasha tana tafe tana kuka, niko nace Billy Allah ya raka taki gona nima na dana inji su takwara bani ba😜, yau dai Billy Sai kwanan Zazzau, Umma yau zakiyi babban bakuwa ko ince baki don Ummimi ma tana hanya yau zaki girbi Abunda kika shuka.

*********************
"Maman Baby nifa yau gabana Sai faduwa yakeyi "to Maman jafar ni ina ruwana Allah yasa masifan da kike ta tarama kanki ne zaki girba, ehe ni da nake rakaki muke aikin nan tare Amma don kun samu duniya ne kika gujeni, ki ka maidani Banza, Au haka ma zakice lallai dan Adam butulu ne, duk hidiman danake miki baki gani, don kince in baki dubu Ashirin na hanaki shine kike cemun haka, "Ance din, danbe ne ya kaure tsakanin su, nan da nan Gida aka fara taruwa kasancewar gidan haka yake, da An fara fada zasu fara taruwa kuma ba mai rabawa, musamman fadan kawa da kawa, don kowa yayi mamaki, ga yar tone tone da suke tayi a tsakanin su.

***********************

Ummimi ne ta fito rike da akwatinta a hannu Sai data duba ba kowa a falon da harabar gidan sannan ta Ajiye musu letter a kan kujera ta tafi, niko nace Ummimi baki kyauta ba, bakiyi halarci ba, Ummimi ta dauki Hanyar zaria.

************************

Dambe yayi danbe har da jin ciwo har dare Ana Abu daya kwatsam Sai ga Billy ta shigo tana rusa kuka, gaba daya kallo ya koma kanta dama ga mutanen gida gaba daya a tsakar gida a na kallon danbe don Baffa Yahaya yace kar wanda ya rabasu a barsu su daku da kyau in sun gaji sa bari, Sai ga wani tashin hankali, da gudu ta yar da Akwatinta taje ta rungume Ummanta, da sauri Umma ta jata suka shige daki, kowa ya watse Ana ta gulmace gulmace, wasu suna Allah Kara dama Auren bana Allah bane shiyasa baiyi lasting ba tunda gashi Maman Baby ta fara tona Asiri.
Chapter 20 · 0% Book details