← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 30

Sashe 24

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Aisha mu kun barmu a duhu fa, Hajia yaya take wannan maganar, Guggo tsohuwa ne tace, "Haba ya'ta ku daina kukan nan kuyi mana bayani mana, "don Allah Hajia ina son inga Mijin yar uwata, da kuma Wanda ta rikemun yar uwata, Hajia Yaya ta aika aka kira su Baffa Habibu harda su Daddy nan da nan falo ya cika da mutane, Daddy Babba tunda ya shigo ya kura ma Mama Ido "Momy Boy wannan ba Nusaibatu bane, "kwarai kuwa nima tunda na shigo nake kallonta gaba daya kowa yanata mamaki, Yaya Ameen ne yayi karfin halin "cewa don Allah Mama ku fadamana abunda ke faruwa, kun barmu a duhu, "Momy ne ta mike tana kuka tabbas yau naga yar uwata domin wannan da kuke kallo ba sunanta Aishatu ba sunanta Nusaibatu yar uwata ce Mu din yan biyu aka haifemu bayan tsawon shekaru da mahaifiyar mu ta dauka bata taba haihuwa ba, kwatsam sai ta samu cikin mu, a lokacin duk muna Maiduguri da zama Amma Mahaifin mu Dan Asalin Yola ne zama ne ya kaishi Maiduguri, da Mahaifina da kilishi Uwansu daya Ubansu daya, muna yawan Zuwa Yola sosai, kwatsam watarana ranar da ya kasance ranar bakin ciki a garemu randa Mahaifiyata da yar uwa ta sun fita anguwa ranar bamufi shekara biyu a duniya ba, kun san halin da kasar mu take ciki, game da yawan ta, addanci, akace yan Boko Haram sun sa Boom a super market din da su Momy na suka je, kuma sun kwashe wasu sun gudu dasu, da kyar aka ga gawar Mahaifiyata, yar uwata kuwa haka muka dunga nemanta har gidajen radio da television, kasan cewar lokacin da aka haifemu irin mu daya, kuma Mahaifiyar mu tayi mana shaida lokacin da Razor haka ranar mahaifin mu ya dunga mata fada, akan mene zata jima na ciwo, tace mai yayi hkr tayi mana hakane sbda batasan ya rayuwa zata kasance ba, kowa farkon sunanshi ta samai, ni a hannun hagu ita kuma yar uwata a hannun dama ina Zuwa gidan nan na dora ido akanta Naji kawai inajin wani abu game da ita haka na dunga kokarin ganin naga shaidan da zai tabbatar mun da haka, shiyasa na tare a dakinta, sbda naga tsananin kaman da mukeyi da ita a lokacin da ta fita yin alwala na bita lokacin da taxo wanke hannayenta naga shaidan nan, nan na tabbatar da cewa ita din yar uwata ce Amma sai da na kira Kilishi ta turamun da pic namu da muke yara, kasan cewar bayan rasuwar Mahaifiyan mu Mahaifin mu bai Kara Aure ba, sai Kilishi ta daukeni ta cigaba da rukona, har na girma akayimin Aure nida Daddy ku, hadin zumunci ne, sai gashi mun cire rai zamu Kara ganin yar uwan mu Sai gashi ta sanadiyar yarinyar ta mun ganta Ashe Alhaji yarinyar mu muka rike bamu sani ba, Alhmdulillah, gaba daya dakin ya dau kabbara, Guggo tsohuwa ce ta mike, tace Tabbas Aishatu yar Uwarki ne, sbda Shekaru masu yawa, Alhaji Mallam yaje wani tafiya Maiduguri gurin wani taro na Malamai da, akayi, kwatsam sai gashi ya dawo da yarinyar yar kyakyawa da ita taci kuka har ta gaji, bayan dawowan shi ya Tara taro kowa a gidan ya shaidamusu cewa zuwanshi Maiduguri, ansa Boom bayan ya fito zai tafi kowa nata gudu yana neman gurin buya bayan sun sha da kyar suka koma inda suka ajiye Motar su, suka shiga suka kamo hanya kwatsam sai da sukayi nisa, sai sukaji kukan yarinya a bayan seat din Motar su tana kiran Momy, gaba daya sun tsorata, da suka duba sai suka ga yarinyar nan tayi biji biji jikinta duk jini duk ta kuje, wato ta firgita ne lkcn da akasa Boom din shine taje ta shige Motar su, tunaninta inaga Motar da Mahaifiyanta tazo da itane sbda tsaban rudewa datayi, bayan ya gama mana bayani yace mun Ke Karima tun da keda Jibo baku taba Haihuwa ba ga Amanar yarinyar nan har lokacin da Allah zai gaddara mana ganin Iyayenta don inaji a jikina komai dadewa Zata sadu da iyayenta ko danginta, tabbas yau Maganar Alhaji Mallam ya tabbata Aishatu yau gaki ga yan uwanki, Bayan nayi ta rainon Aishatu tun bata yarda dani har ya kasan ce ta saba dani, duk da haka tafi sabawa da jibo don gatan duniya ya nuna mata, har ta girma Alhaji Mallam ya Aurar da ita ga Habibu danshi da yafi so, a rayuwar shi, sbda yace bazai Aura ma kowa ita ba kar wataran a Mata gori, haka dai Habibu ya karbi Auren Badan yana so ba sbda yana da wata budurwa dasukayi alkawarin aure Amma bayan ta gama karatu, da yake su iyayene jajirtattu akan yaransu hakanan ya Auri Aishatu, Akan cewa bayan shekaru zai Auri Budurwan shi dayake so, haka ko akayi, Yanzu Habibu Matanshi Biyu Amaryan ma tana da yara hudu, to kundai ji inda muka samo Aishatu, ba Wanda baiyi kuka ba a falon, ni kaina sai da na taya su Momy kuka, bayan duk an gama je jeton Al'amarin sai Daddy ya daga waya ya kira Kilishi ya sanar da ita Abunda ke faruwa aiko a Daren tace a nema mata jirgin da zai kaita Kaduna daganan sai, ZARIA yau komai Dare sai taxo ta ga yarinyar ta, haka aka kira UK aka fada ma Daddy UK wato Mahaifin su Momy kenan aiko har da kuka sai da Daddy UK yayi Yace shima gobe insha Allah yana Nigeria, da kyar aka lallabi Kilishi ta bari sai gobe tazo, sbda ba, asamu jirgin da zaizo kaduna ba, haka taro ya watse gaba daya Momy dakin Mama ta tare, haka su Zahra aiko Mamy ma tace ita can zata koma, Dangin miji, Su Yaya Amar ne kawai suka tare a dakin Hajia Yaya, sunce su suna Auren da ita, haka suka dunga shan hira da ita, dayake ita akwai son jikoki,

Washe gari Asuba ta gari Hajia Kilishi ta kamo Hanya, haka Daddy UK shida Matarshi da ya Aura A can, Hajiya Kilishi kuwa ita da Talban ta, karfe goma ya musu a Zaria nan da nan gida ya cika, lbr ya karade gidan fulani kowa yasha Mamaki, haka Kilishi ta dunga lallaba Mama kamar zata mai data ciki, Ummimi na Zuwa taje da gudu ta rungumeta, Dallah dagani da kika mana gudun Hijira, Toni ba ta kanki nakeyi ba yanzu ta kan ya'ta nakeyi, Aka kwashe da dariya turo baki tayi Momy tace kinji zo Baby na ni ban dena yayinki ba, "yauwa Momy na, can suka ga An fara shigowa da kayayyaki na alfarma Kama daga abun ci da Abun sha, da akwatinan kaya Kala Kala, wata Balarabiyan matane ta shigo rike da wata yarinya irin su daya da Ummimi, tana Zuwa ta tsaya tana kallon duka yan dakin aiko da sauri ta karasa kusa da Mama ta rungumeta tana fadin MashaAllah, Alhmdulillah yau kukan mijina ya kare, Mun gode Allah, kowa ka kallah a gurin farin ciki fal ranshi, bayan an natsa Daddy UK ko yaki sakin Mama tunda ya rungumeta a jikinshi, daka ganshi kasan ya tsufa sosai sai dai jin dadi ya boye tsufan nashi, ita sai jin kunya takeyi, tana yin motsi kowa zai taso yace mata lpy, Aiko Aunty mu taga karyar Arziki da gata da takeyi ma Mama gori, kunya duk ya isheta, ta rasa yanda zatayi don Daddy UK Akwati guda aka bata na tsaraba da ita da yaranta,

Bayan kwana biyu komai ya lafa aka kira taro Hajia Yaya da Hajia Kilishi, Bayan an zauna ne, suka gabatar da abunda yake ransu Maganar sa ranar Ummimi, da Mubarak, nan aka sa ranar sati biyu, Yaya Ameen ne ya mike yace nima fa na samu mata kawai aje kano a tanbayo mun Auren nan a hada duka ayi rana daya, "iyye mare kunya Kilishi ne tace haka waye matar to, ai da gudu RALEEYAT ta tashi ta gudu don taga Alama YAYA Ameen ba kunya gareshi ba, dariya gaba daya akayi, "Yaya Umar ne yace "ai gunda layi ya dunga matsawa ko a bamu guri muma, "iyyeh gidan ku Umari nace, ta wurgoshi da pillow data kishin gida dashi, kaucewa yayi yana dariya Hajia Kilishi ai gskya na fada ko Jafar? "Eh mana Aboki to munji kai Habibu da Habibu da Jibrin da Yahaya da Ahmadu kundai ji yaron ku yana son kuje ku nema mai Aure, "Eh Hajia ai yau Zamu tafi, toni Anata Maganar Aure banji kunyi na yarana bane, inata kawaici naga kun share, "suwa kenan,? "Su Zahra da Amar mana, "ok ai duk tare za, ayi da nasu Mubarak din Hankalinki ya kwanta yanzu koh? "Sosai ma nan taro ya watse,

"Madam ya kamata a dunga kulani mana don Allah bakya ganin su Zahra ne da Yaya Ameen yanda suke shan luv Amma ni sunan an Amince mun din ne amma anki bani daman in nuna irin Soyayyan da ke raina, "Naji zan baka dama, Amma da a sharadi har sai kace ka yafe ma Billy sannan ka nuna ma yayanta mahimmancinta a garesu, ka dunga kaisu gurinta su saba da ita kafin ku koma, "haba baby wannan sharadin yayi tsanani da yawa, gskya bazan iya ba, to shikenan juyawa tayi ta tafi ta barshi a gurin a tsaye, da sauri Billy ta juya ta labe tana share hawaye lallai Ummimi ta cika yar halas duk irin muguntar dasukayi mata Amma ita kokari take ta nema mata yafiya take yi, Abunda ta kasa ita, wayyo rayuwa, niko nace Billy kadan ma kika gani,

Haka akaje aka nemama Yaya Ameen Auren Raleeyat inda duk aka sa rana daya dana su Ummimi, nan su Momy suka fara shirin komawa sbda Biki, Kilishi ta dage sai da Mama zasu tafi ita da Daddy UK, su daddy suka haba su barta mana bayan bikin su Ummimi sai taje duk dangi su ganta, da kyar suka yarda,
Haka suka shirya suka dunguma sai Yola Yaya Mubarak duk da haka Basu daidaita da Ummimi ba,

To nima nace bari inbi ayari inje Yo, la daga nan na in biya gidan su sis Adama, 😂😂

KUCIGABA da bin yar mutan Zazzau ✍️✍️✍️

Share

Vote

Comment ✍️✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________
Chapter 24 · 0% Book details