← Book details Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 30

Sashe 15

Gidan Gado 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari su Yaya Ameen sunje sun sayi plaza an gama komai a cikin kwana bakwai, saboda akwai kudi, a hannun su, plaza yayi kyau sosai su Baffa Yahaya da Baffa Jibrin da Baffa Habibu, sunje sun ga guri yayi kyau sosai, anyi musu sauka a gurin kuma, anyi musu addu, oi za,a fara Aiki a gurin ranar laraba, Maman Jafar tayi bin kwakwaf din dazataji plazan waye Amma ta kasa sani, tunda ance na Yaya Ameen ne, nan da nan Bakin ciki ya wanzu a cikin zuciyan yan gidan Fulani masu mai murna nayi masu Hassada nayi,

Note:wai ace yan uwa yau dan uwanka ne Abun alheri zai sameshi maimakon ka tayashi murna, a,a sai bakin ciki, taya zamuga cigaba a rayuwa don Allah mu gyara halin mu yan uwa sai muga cigaba, a rayuwar mu, Allah yasa mufi karfin zuciyan mu,

Su Yaya Ameen da Yaya Jafar da Yaya Umar komai ya tafi musu yanda suke so, MAMI SPECIAL SEWING MACHINE AND DESIGNERS PLAZA, Yaya Jafar ya bada shawaran a sama plazan sunan Mami mutumiyarshi, duk saboda kar mutane su gane plazan waye,

*************************

Sallama yayi ta Ansa mai shi Kadai ya shigo gidan, yana isa kusa da ita ya zauna "Amarya bakya laifi, "dakata Mallam dama ka daukoni ne danginka su wulakantani iyeeh? Haba Baby na rungumeta yayi, kara fashewa da kuka tayi na kissa, nan da nan Ango ya rude, ya fara sakin layi nima dai na tattaro biro na da littafina, na gudo nace Allah yasa dai Wainnan Amarya da Angon nan ma su samu suyi dan sallah nafila da Addu'a, don naga Alama Angon a hannu yake, 🙈 nayi nan bani na fada ba🏃🏃

*************************

INDIA

Karatu yayi zafi don yanzu su Zarah basa wani samun zama, sosai, "Yauwa Sittynerh wai wace na ganku tare jiya a Department kaman na Santa wlh, ya sunanta? "Sunanta Raleeyat Ya'u kano, "kai wlh nikuwa na taba jin sunan fa Sittynerh kuma tun da dadewa, Amma na manta inda na Santa, nocking akayi musu, "Bloodynerh ana nocking fa, "bari naje na duba, to, Hanyar fita tayi taje bakin kofa, sai taji gabanta ya fadi, tana bude kofar suka hada ido da wanda take tsaye bakin kofar, kawai jiri taji ya debeta zata fadi da sauri Zahra ta tareta,

To kudai cigaba da bin YAR MUTAN ZAZZAU
Kowa Ummimi ta gani to nima dai ban saniba✍️✍️✍️
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: 💗💗💗💗💗💗
GIDAN GADO
💗💗💗💗💗💗
(CELEBRATION WEDDING AND TRAVELING TO ABROAD)

WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.

🌹🌹EPISODE FOURTY TWO &THREE🌹🌹

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

Aunty na na kaina wannan page naki ne na baki kyauta(Ummu Inteesar) ke da kawanki (Ummu Affan) kuna sani nishadi😍😍

Aunty mai sunan yan gayu😜(Saamlad) ina tayaki murna fara sabon novel dinki mai suna SO NE Allah yasa anfara a sa, a.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Whatpad
Zeeyterh Rahzeey yaree@

"Kanaji ko Mubarak? "Eh Addah Adama, "yauwa kayan nan ne sunyi yawa ya kamata a rage kaga nan gaba, in ka tashi auro Matar da Mamin ka take so ka aura kaga zai zo maka da sauki, sai a karo wasu kawai, koya ka gani? "Gskya ni Addah a barmun kayana haka nake so a kai ko mayafi bance a ragemun ba, ita Mamin in ta tashi yimin wancan auran ta hada mata laifen da kanta, "iyee!! Har ni zaka fada ma haka don kaga ina binka ta lalama wlh sai an rage kayan nan, yarinya kamar yar gold, kodaddiya ma da ita ni Banga abun so a jikin ta ba, duk kawani rude ka susuce a kan mace duk kabi ka lalace, ni Anya ma Mubarak yarinyar nan haka ta barka kuwa? "Kai Addah ni ban san mai Billy ta muku ba duk kun tsaneta, bakwa sonta ita ko tana matukar son ku, ban san ya zan muku ku fahimta ba kuma wlh tana da kirki ga tarbiya, "dallah rufemun baki Ana ga gabas kana ga yamma, tashi ka ban guri, tashi yayi yana mai jin Haushin Addah nashi, duk sunbi sun tsanar mai mata,

Yauwa Bloodynerh kin san har yanzu kinki bari ku hadu da yayana gashi za, ayi bikin shi bama nan, naso Daddy Babba ya barmu muyi biki sai mu tafi duk da ni wlh Haushin matar dazai aura nakeji ta cika iyayi wlh, gata ba wata mai kyau ba sai tsawon tsiya farine kawai ya ceceta, "kai Sittynerh wai ke inkika fara magana bakya gajiyane ayi mutum ya cika surutu, "to nayi din yau miskilancin ya Motsa ne, wlh Maclean tsada yakeyi kyayi warin baki, Amma da yaya Amar ne ai kin iya surutu dashi in ni nayi miki kice na cika surutu, ke da Yaya ban san wayafi miskilanci ba wlh, don Allah ki kalli pic din Yayana yau, "ke ni kyaleni bazan kallah ba, tashi tayi ta fita daga dakin, zuwanta falo kenan Yaya Mubarak ya haye sama dakin Mami bayan Adda Adama ta gama mai fada, Addan mu kece a nan? "Eh yar Albrka in yar uwar taki tana ciki, ok kitchen tana nufa ta bude fridge ta dauko ice cream tana tsauna a table din da yake kitchen din tana shan kayanta, "wlh Yaya zamuyi fada da Bloodynerh wai kwata kwata bazata zauna muyi hira ba sai tace na cika surutu haka akeyi, "to My kanwaty haka bloody naki takeyi miki, to ai ke matsalan ki daya in kika fara surutu kaman gidan Radio FM Yola, "uhm uhmm au ma haka zakace Yaya goyon bayanta zakayi dama ai nasan san kai kakeyi, buga Kafa ta fara yi, A,a waya tabamun takwara ta ne, "yauwa Hajia Kaka ba Yaya Amar bane, "kai kai ba ruwanshi Hajia kaka halinta ne fa aka fada, au hardake Baby, kun hadu da Yayanki kun samun takwara a gaba, zaka sani wlh sai in fasa baka auran, "yo ni Dama Hajia Kaka me zanyi da wannan Afiruwan takwaran naki ci ba kiba, ai sai a ga kaman ban iya kiwo bane, hhhhh "Wai haniyar me kuke tayi Yauwa Mamin mu tsayafa kiji yanda akayi, "to Baby ina jinki, fadi ma Mami duk yanda akayi tayi, Mami tace, "to in banda abunki Auta ai ke din ne kin cika zuba, gaba daya kwashewa da dariya akayi kuka ta saka ta Haye sama tana fadin"wlh sai na fadoku da yayana da Adda Adama da Adda juwaira nasan suma bayana zasu bi tunda abun hakane,

Uhmm Babyn Momy kizo mu tafi gida Affan nata kewanki, da Momy duk ta damu yanxu shigowana garin kenan fa ban ganki ba nayo nan, niko nace kai dai yaya Amar fadi gskya 😍
To muma ai Bamu gaji da ita ba Son, "to Momy dama ina son muje taga kayan dana siyo musu ne kin san tafiyan nasu ya matso, "wai yanxu da gske su Habibu Kasar waje zasu kai yaran nan ni aure naso ayi musu, Amma Allah ya bada sa,a "Ameen Hajia kinga zamani yanzu ya canza Ilimi shine mutum, Hakane Allah ya taimaka Ameeen,

"Mamy zan tafi, "to Baby ai dama nasan kema kin kusa ki gudu kibi Yayanki, wataran dai zan kwace ki duka inga yanda zasuyi ai, ita dai Baby bata kawo komai a ranta ba ta haye sama tayi ma su Addah Adama sallama, da Hajiya kaka, ta fito kenan su ka hadu da Abul khairi
Aunty Baby ina zaki na ganki da mayafi, "yaron Mamy zan tafi gidane, "zan biki nima inje gurin Affan, "wlh bazanje da kai ba kuyi ta sa Momy magana, kuka ya fara ya juya zuwa dakin Mamy, ita kuma taji kaman Alamun bude kofar Daddy, kuma tasan Yayan su Mubarak yana nan a dakin ita kuma a rayuwa ba wanda ta tsana irinshi sbda Halin shi da Sittyn ta take fada mata, da kuma abunda yayi ma Nusaibat,

"Oyoyo Aunty Baby ta dawo Momy kizo ga Baby ki ta dawo, da sauri Momy ta fito daga kitchen "oyo yo my Baby I Miss you too, Miss you too Momy na, "ai nayi niyar da Bali dawo ba yau zanje da kaina in dauko ki, "kai Momy to ba gashi na dawo ba to in muka tafi school fa, ya zakiyi, "ai wlh ni kaina Abunda nake ta tunani kenan "Uhmn Momy ko ganina bakiyi ba kina can gurin yarki, kin shareni, na shawo hanya ko gida banje ba nazo na dauko miki yarinyar ki, "Uhmm sorry son oyoyo, "uhmn ni banson oyo yon gwalo tayi mai ta boye bayan Momy "kai yaya Wlh Aunty Baby gwalo takeyi maka, ai da gudu ya bita ta haye sama, "Oh ni Hindu ka dawo kenan ko zaku fara, dariya tayi ta koma kitchen don karishe girkinta,

*************************

"Kin san meye Umma wlh na tsani uwar nan nashi da shegun kannin nan nashi su biyu yan mata shikenan yace Zahra da Baby kinga hotunan su kuwa kaman larabawa wlh, ke sun hadu, kawai Sai naji wani bakin ciki sun fini kyau, kin san Meye ke damu na Umma inda Baba ya samana ido ya hanaki fita, balle ki koma gurin Mallam, ni damuwa ta ma kudin da ake yawan satamun, Umma, kedai bari, Bilki ni damuwa ta ma daya kar Asirin nan yayi kasa ya rage baki kudin nan, gashi kwana biyu muna rashin kudi, gashi yaki zuwa, "eh wai sai kannin shi sun tafi makaranta zasu India karatu, shiyasa Hidima yayi mishi yawa, wan can karan ma fa wannan brother nashi ya aiko, ni wlh ma shi kanshi brother nashi bai birgeni sai da ya dunga mun tanbayoyi fa, kaman wani Ubana, "duk ki rabu da shegu zan kai sunan su gaba daya gurin Mallam, "yauwa my Ummata, ina son ma in fara zuwa gyaran jiki gobe a Ungwan Masa, ok Gidan Salaha Mai gyaran jiki "eh Umma,
Chapter 15 · 0% Book details