← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 41

Sashe 5

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu siraran hawaye suka gangaro saman kyakkyawar fuskarta dede lokacin wata dattijuwar mata tashigo cikin 'karamin parlour bakinta d'auke da Sallama saurin share hawayen nata Iftahal tayi tafito parlour cikin girmamawa dattijuwar matar tagaidata murmushin 'karfin hali Iftahal tayi tace " haba Mama dagirmanki ay nice yakamata nagaidaki bakeba mama dan Allah kibari " murmushi Mama tayi tace nagode sosai dakika bani girmana sunana Iya Rabi ina d'aya daga cikin masuyima duka ma aykatan gidannan abinci Ni Yar Nigeria ce kamar ki kasancewa ta Yar Nigeria yasa Shanwul za'boni dan yimiki hidima wajan abinci se masu gyaran bedroom d'in ki sud'in Yan nan 'kasar ne se mai tayaki hira itakuma daga 'kasar 'yalla'bai take wato misra konace Egypt ko yanzu breakfast d'in ki angama yana kan dinning nashiryashi dawuri sabida Shanwul yacemin zakishiga Skul 08:00 "

Murmushin ya'ke Iftahal tayi tace " to Mama nagode amma bazan samu shiga Skul d'in ba kicema Shanwul yatafi hidimar shi kawai breakfast Kuma idan nafito naci sukuma masu gyaran bedroom su gyara parlour kawai zan gyara nan nagode " daga haka Iftahal tajuya takoma cikin bedroom fita itama mama tayi tana fita taci karo da Maher yafito daga room d'in motsa jikin shi gaidashi tayi bai amsaba dama batayi tunanin amsawar tashiba cikin shakka tace

" Allah ya'karamaka lafiya Saraki kai d'aya ne tak magajin sarautar Egyy ina neman afuwa nakasa saka sarauniyar mu fitowa yin breakfast ayanzu duk da tanada shiga Skul 08:00 agafarceni Saraki Mai nasara senaga kamar gimbiyar tamu batacikin yanayi Mai dad'i sabida tace bazata samu shiga Skul d'in ba agafarcemu ranka shidad'e " hannu Maher yad'aga mata sannan yace

" Kuje kawai " daga haka yajuya yanufi bedroom d'in Iftahal

Comments and share please

........📖🖊 NPEEDY A AJI MARMNY ZARAH 🥰👍🏻
🗡 *!!!FURUCI!!!* 🗡
💔💔💔
💔
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* 💓❣💘

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agunku ko kyauta zaku iyabani 200 batare da kasuwanci ba sannan bawai nakomayin book d'in kud'i bakenan a a har gobe zan dingayin na kyuta sabida Ina matu'kar sonku kamar yadda kuke sona zan dingayin nakud'ine sabida siyan data kai carji sabida bakoda yaushe akesamun wutaba gashi lokaci d'aya waya zatabu'kaci gyara idan babu kud'in gyaran to Yaya kenan

Nasan wasu zasufahimceni amma wasu ina sabida kowa da irin halinshi sabida haka inasake baku ha'kuri afuwan Dan Allah 👏🏻 zanyi Free page har zuwa 9 to 10 nagode NPEEDY A AJI takuce har abada

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER zansaka muku Number account din a last free page

IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA 🥰🤝🏻

_Free page_

🅿 7 to 8

Yana shiga Iftahal tayi saurin mi'kewa tayo gunshi tun kafin ya'karasa gareta dur'kusawa tayi agaban shi tasaki kuka tace

" Kayima Allah karabani dawannan auran 'kaddarar naka dan Allah fushin iyaye akan d'ansu masifane kasan haka dan Allah kacece ni " ajiyar zuciya Maher yasauke sannan yace " idan kinason cikar burinki to kisaki jikin ki kiyi karatu yadda yakamata yin hakan zesa nayimiki aminda kike so shima Abban zaiyi farinciki dahakan kiyi sauri kifita kiyi breakfast time yana tafiya " daga haka Maher yajuya yafita kuka Iftahal tasake saki amma babu yadda zatayi dole tayi yadda yace idan har tanason yayi mata abinda takeso cikin sanyin jiki tafito parlour gun dining tanufa wayarta tagani saman dining d'in dakud'i ruwan tea kawai tasha tami'ke wayar kawai tad'auka da bag d'in ta tanufi hanyar fita cikin sanyin jiki tana fita Shanwul yashiga gaidata amma bata amsaba bud'e mata mota yayi tashiga yarufe ahankali yake tu'kin har suka isa cikin harabar Skul d'in bin motar kowa yayi da kallo dan Kam kowa yazata Prince Maher ne cikin sauri Shanwul yafito bayan yayi parking yabud'e mata motar tafito cikin girmamawa yace

" Ranki yadad'e kamar yaushe zanzo d'aukar ki " kamar bazatayi magana be sekuma tace zan kiraka " daga haka tayi cikin Skul d'in dagudu su Salma suka nufota rungumai ta sukayi cikin zolaya Salma tace Iftahal cikin kwana d'aya har kinzama babbar yarinya wannan irin mota haka dubi shigarki gaskiya wannan furucin naki alkairi ne agareki " turo Salma tayi cikin raunin murya tace " haba Salma kibar wannan zolayar FURUCI!!! na babu abinda yajamin se tsananin tashin hankali da ba'kin ciki Salma ayanzu haka iyayena sunyi fushi dani tayaya zanga dede " kasa 'karasa zancan tayi sabida kuka " kama hannunta sukayi suka nemi guri suka zauna cikin damuwa Salma tace

" Nafahimci halin dakike ciki Iftahal amma ni shawarar dazan baki itace " addu'a itace zaki ri'ke sabida babu wanda yasan abinda Allah yake nufi akan wannan lamarin kid'auka auran Nan naki wani ikon ubangiji ne Iftahal kiduba babu wanda yayi tunanin wannan lamarin gashi har Allah yasa yabarki zuwa Skul Kinga kenan babu niyyar cutar dake cikin ranshi ni aganina kiyima mijinki biyayya har zuwa lokacin da iyayenki zasu huce in sha Allah zasu yafemiki yanzu dansunyi fushi ne shiyasa Iftahal dan Allah kicire damuwa yadda karatunki zai tafi dede "

Wannan shawarar sukadinga bata har time d'in shiga lecture yayi Koda suka fito daga lecture Iftahal binsu Salma tayi hostel kwanciyar ta tayi ganin su Salma yasata d'an jin sassauci dakuma irin shawarwarin dasuke bata har tasamu yin bacci se yamma sosai Iftahal tatashi damunta su Salma suka d'in gayi akan tatafi gida kar tasake saka kanta cikin wata matsalar sosai ranta ya'baci tatashi d'aukar wayarta tayi ayko taga miss call d'in Shanwul har guda 8 kafin takirashi wani kiran nashi yasake shigowa seda takusa katsewa sannan tad'aga cikin sauri Shanwul yace

" Ranki yadad'e dan Allah kitaimake ni kizo mukoma gida idan kika 'ki to wallahi zan fuskanci matsala wajan Prince dan Allah ina wajan danayi parking d'azu " kashe wayar tayi taja tsaki sannan tami'ke har wajan mota su Salma suka rakota sannan suka koma cikin hanzari Shanwul yabud'e motar tashiga sannan yarufe yakoma yabud'e mazaunin shi yatada mota sukabar cikin Skul d'in cikin shakka Shanwul yace " Ranki yadad'e am kamar jiya ciwon Prince yatashi ko ? " tamke fuska Iftahal tayi tace " to tunda kasan haka meye kuma natambayata " murmushi Shanwul yayi yakuma cewa " sabida naji bai dad'e yanayin ihun ba hakan yasani yin farinciki sosai sabida aduk lokacin danaji ciwon Prince yatashi inayin kuka sosai sabida tsananin tausayin shi inaji kamar naje wajan shi koda zai kasheni ne senaji jiya bai dad'e ba yadena ihun hakan yasa naji araina ked'in alkairi ce agareshi " jin hakan yasa Iftahal duban Shanwul sosai tace

" To amma maiyasa ba'a saka malamai sunayimai addu'a se kwai akeyimai maganin asibiti ? " cikin raunanniyar murya Shanwul yace " hmmm Ranki yadad'e wannan hanyar akafara 'ko'karin bi amma abin mamaki duk malamin da'aka kira to kafin zuwan shi sede muji labarin mutuwar shi tun ba'a gane hakanba har aka gane idan Kuma aka d'auke shi zuwa wajan maganin to ana isa sekiji ance ikon Allah yanzun nan akawuce da malam zuwa asibiti ciwo na gaggawa ma'ana yanzu ciwon yasameshi hmmm wani abun mugun tashin hankali shine kakan shi wato Mahaifiya maimartaba Zaid dayayi yun'kurin yimai magani kasancewar shi malami aykuwa sede muka wayi gari yasamu ciwon 'barin jiki har yanzu shikam yananan bai mutuba amma baisan yaya duniyar take ciki ba yazama tamkar gawa to amma akwai wani tsoho cikin 'kasa Mai tsarki yake wato Saudiyya munje nida Sarauniya Batol wato Mahaifiyar Prince sabida duk bayan 6 months setaje dan yima Prince da Kaka addu'a shine tsohon yace Min amma ni kad'e lokacin Sarauniya Batol tana cikin masallaci nikuma ina waje shine kawai naganshi yashiga yimin bayani sosai nacika da mamaki sabida ni bance dashi komiba kuma banko ta'ba ganin shi ba bayani yayi min kamar haka

Dole se Prince yayi aure matar dazai aura itace mafarin warakar shi sannan yace abubuwa guda 3 suke damunshi 1 akwai jinnu wanda akayimai ture dasu sune suke barazanar kasheshi Kuma suke sakamishi matsanancin ciwon Kai sekuma 'yan 'kungiyar asiri wato mafiya sune suke raba 'kwa'kwalwar shi gida 2 sekiga yakoma tamkar yaro 'karami duk abinda zaiyi alokacin to bazai iya tunashiba bayan yadawo dede Kuma sune suke shashi yun'kurin kisa sabidasusha jini na 3 anyimai sihiri akan rashin samun natsuwar rayuwa sabida ba'aso yayi farinciki ko kad'an shiyasa ko Yaya yaji farinciki tofa ansamu matsala akoda yaushe zuciyar shi cikin tsananin bugu take sannan wannan sihirin yanasaka mazantakar shi mi'kewa ta'ki kwanciya har na tsawon kwanaki 2 aduk lokacin daciwon yatashi Kuma yanasa jikin shi d'aukar zafi sosai shiyasa baya shiga Skul har se bayan kwanaki 2

Tsohon yacigaba dacewa duk matar daya aura ita kad'e ce zatagagari kisa agun su amma zatasha matu'kar wahala sannan zamanta akusa dashi zaisa yadinga samun sassauci sabida addu'ar ta zatayi matu'kar tasiri agare shi sannan yace wannan doctor akwai wani munafurci atare dashi wato doctor dayake dubashi daga India wanda zasuzo tare da maimartaba Zaid da Sarauniya Batol nanda kwanaki 5 a 'karshe yace karna sanar dakowa wannan maganar se matar da Prince ya aura idan kuma nasanar dawani to zasu kasheni sabida zasusan nasan sirrin su yace itama matar tashi karta sanar dakowa idan lokaci yayi kowa zaisani
Chapter 5 · 0% Book details