← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 41

Sashe 20

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK

IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 31 to 32

Yana sake kallonta bata iya bashi amsaba sebayan tagama kwara aman tace " kayi mamaki lokacin dakaga wasu kaya jikin ka ba wa'inda ka kwanta dasuba amma mamaki kawai kayi bakace a a bawasu bane ko bakace bakai bane " amma ni kacemin bakai bane bakuma zai yiyuba lokacin daka cire imani karabani da abinda yafi komi daraja agun kowace mace Ina kaba haquri Ina kuka amma baka saurareni ba seda kacimma burinka akaina har kayi sanadin samuwar gudan jinin ka cikin jikina amma kajuya baya kanuna bakasan hakanba haba Prince tunda nasanka nasan waye Kai Allah yasani ban ta'ba suffantaka ayadda kake tunani ba nasan lalurace bawai rashin hankali ba kamar yadda kake tunanin na d'auka ko kusa kalli wuyana Prince ji yadda kajimin ciwo har yanzu yagagara warkewa dubi yatsan hannuna kusan kwana 4 kenan yana a kumbure se azabar ciwo ka kalli fuskata da kyau har yanzu akwai shacin marin ka ajiki amma ko sau 1 bakata'ba duba irin illar dakayimin ba ko katambayeni kullum iqirarin ka shine bakason mace bakason duk wata ma'amala da ita to tayaya zan iya sanar dakai abinda yafaru bayan kasakamin tsoran ka cikin zuciya ta kaf cikin gidan ka akwai CCTV camera amma ko sau 1 bakata'ba duba abinda yake faruwaba cikin gidan kenan babu amfanin saka CCTV d'in Kai ne kayi sanadin rabuwata da iyayena amma ko tausayina bakaji maiye haka Prince idan baka duba kasan wanda yasamin guba ba to wallahi zannemi gubar dakaina nasha gara namutu da wannan baqincikin yau idan na tsallake gobe fa ? dan nayi imanin idan baka Kama Wanda yasaba gobema za'a sake sakawa kayi tunanin Prince nikam nazomaka da dukkan alkairi " taqarashe fad'ara hakan cikin tsananin kuka Mai qona zuciya

Sosai jikin Maher yayi sanyi dajin kalaman Iftahal Kuma sunyi masifar ratsa zuciyar shi sosai ya fuskanceta yace " naji Kuma zan bincika amma idan har ta tabbata wannan cikin nawane to bana buqatar shi zansa acire shi dan bazan iya da hayaniyar yaroba dan kinsan banason hayaniya idan ma kinsashi cikin ranki to gara ki gaggauta cire shi sannan tabbas nasan akwai CCTV camera amma banason dubata sabida natsani kallon halin da nike kasancewa idan ciwona yatashi amma yau yazama dole naduba zanje gida nadawo yanzu "

Daga haka yafita cikin sauri yana fita doctor Sera tashiga sannu tashigayima Iftahal sannan tasaka aka gyara gurin rumtse idon ta Iftahal tayi afili tace " bazan iya zubda ciki ba dan bansan abinda Allah yake shirin baniba banaso nazama maiyin butulci gurin Allah sede kayi duk abinda zakayi Prince amma bazan iya zubda wannan cikin ba

Maher Yana Isa gida yanufi saman shi wani room yashiga yana shiga ya kunna Computers d'in ciki cikin bedroom d'in shi yafara duba abubuwan dasuka faru tun daga ranar da Iftahal tashigo gidan yana zuwa dede gurin da tafara shiga bedroom d'in shi lokacin da ciwon shi yatashi har kwanciyar dasukayi saman bed yanayimata abu tamkar yaro da shaqarar dayayi mata dafe kan shi yayi amma baiga ya kusancetaba dawoda binciken yayi qasa cikin bedroom d'in ta nanfa yaga duk abin da yafaru tashi yayi cikin zafin rai yature Computer gefanshi tafad'i tafashe cikin tsananin zafin rai yace " wannan ne ni tabbas jikin nawane Amma akwai banbancin ruhi babu yadda za'ayi na amshi wannan cikin "

Har zai fita sekuma yakoma cigaba dadubawa yayi yaga zuwanta cikin bedroom d'in shi nad'azu sannan yaga yadda suka kasance dashi wanda yake iqirarin bashi bane sosai zuciyar Maher takeyin muguwar tafasa bayan shigarta bedroom d'in yaduba idon shi yagane mishi doctor yana saka qwayar cikin ruwa hakan yasashi komawa yaduba camera cikin bedroom d'in shi amma babu komi camera ma bata ayki tashi yayi yashiga watsi dakayan cikin room d'in duk yagama yanke hannu da glass sakkowa qasa yayi yanufi bedroom d'in da doctor yake zama amma Babu kowa duban shi yakai kan Camera dakin amma seyaganta afashe komawa saman yayi aguje cikin zafin rai yabud'e wordrop yawatso kayan ciki azafafe yashiga cire kayan yatsanza wasu yafita tun kafin lenta takaishi qasa yashiga Kiran securitys yana sakkowa sukayi saurin isowa gabanshi cikin zafin rai da fusata yace

" Yau she doctor yafita ? " amsa sukabashi da kafin shigowar ka babu jimawa " cikin d'aga murya yace " inaso kukawomin shi nanda 1 hour Yana gama fad'ar hakan yace " atadamin mota " duban juna suka cikin sauri d'aya yace " ranka shi dad'e ay tare kuka fita da Shanwul d'in " wata irin tsawa Maher yadaka musu dafad'in " dole se Shanwul ne kawai zaiyi driving d'ina ? " Jin haka yasa wani soja saurin nufar mota yabud'e shiga Maher yayi yace " Asibitin su Sera idan kawuce 15 minutes bamu isaba to bakin aykinka jin haka yasa shi taka mota aguje wayar shi yaciro yadanna Kira ana d'agawa yace " Uncle inaso adakatar da tashin kowane jirgi a yau sannan abaza jami'ai duk inda Doctor darman yake akawomin shi " daga haka yakashe Kiran

A asibiti kuwa bayan fitar Maher Shanwul yashigo ciki amma abin mamaki seganin doctor darman yayi yashiga hanyar room d'in da Iftahal take yanufa Kai tsaye yashiga ji Shanwul yayi zuciyar shi bata kwanta ba hakan yasashi bin bayanshi yana shiga Iftahal tayi saurin bud'e ido ganin doctor darman yasata zaro ido murmushi yasakar mata yace

" Ay har yanzu baki tsiraba Kinga wannan allurar yanzu zata kaiki kiyama ke mai miji ko ? to kinguji allurar a gida zaki sameta cikin Asibitin kamo hannun ta yayi daqarfin tsiya zeyi mata allurar Shanwul yashigo tureshi yayi daqarfin tsiya yafad'i tare da allurar saurin tashi doctor yayi yashaqo wuyan Shanwul sosai yashaqure shi ganin hakan yasa Iftahal fasha ihu Wanda seda ko Ina na cikin Asibitin yad'auka Kuma dede lokacin motar Maher tatsaya jin hakan yasa doctor sakin Shanwul yafito aguje cikin sauri aka bishi Maher Yana fitowa daga mota yaga doctor darman yafito aguje cikin zafin nama yabishi tareda sauran ma aykatan asibitin cikin sa'a Maher yashaqo wuyan shi wani irin duka yashiga yimai tako Ina jama'ar suna isowa doctor yazame rigar saman shi datsiya yasakar ma Maher yasake rugawa amma kafin yayi nishi sukaji qarar harbin bindiga kafin wani lokaci doctor yabaje matatce aqasa duba sukakai kan motar data wuce tagaban shi nanko idansu yagane musu Wanda yayi kisan riqe da bindiga cikin mota amma kafin su yunqura tuni motar ta'bace saman titi sabida irin mugun gudun datayi

Dede lakacin jami'ai suka iso amma Koda suka d'aga doctor tuni yamutu sabida tsakiyar kanshi bullet d'in yashiga seda yafasa qwaqwalwar kanshi wani irin ihu Maher yasaki yashiga fad'in " wallahi idan baku nemo Wanda yayi wannan kisanba duk Sena kashe ku Sena kasheku " ganin hakan yasa aka riqeshi cikin zafin rai yawatsar dasu yajuya afusace kai tsaye yashiga cikin Asibitin room d'in da Iftahal take yashiga ganin doctor Sera yayi kan Shanwul daketa faman tari sabida muguwar shaqarar dayasha duban Iftahal yayi ganin hawaye yayi saman fuskar ta sha'be sha'be qoqarin seta muryarshi yayi yace

" Fatan Babu abinda yayi miki ? " d'aga mushi Kai tayi dan bazata iya yin magana ba sabida har yanzu zuciyar ta bugawa takeyi taga mutuwa kusa badan Shanwul ba dayanzu tazama labari kallon doctor Sera yayi yace yanzu zamubar wannan asibitin sabida bashida tsari babu tsaro tunda har za'abar Mai lefi yashigo yayi yunqurin kisa Kuma idan baku gyaraba senayi duk yadda zanyi naga anrufe wannan asibitin zamu tafi yanzu Kya dinga zuwa gida kina dubata amma kisani wallahi idan matata tamutu ko wani abu yasameta sanadin ki to wallahi wallahi kema sekin mutu "

Jikin doctor Sera yad'auki rawa cikin rawar murya tace " kayi haquri kanemi wani doctor ni bazan iya cigaba da dubata ba nima banida lafiya zani gida yanzu " tsawa Maher yadaka mata yace " ke Kika fara dubata kuma kece zaki qarasa idan Kuma Kika qi zan tuhumeki akan barin Mai lefi shiga cikin Asibitin "

Daga haka yaduqa yatada Shanwul tsaye yace " sannu nagode ma Allah da Babu abinda yasameka daya kashemin Kai danayi babban rashi jeka waje gani nan fitowa duban shi Shanwul yayi cikin zuciyar shi yace " ashe Prince yadamu da rayuwata fita yayi yanajin farinciki matsananci cikin zuciyar shi itama doctor Sera fita tayi bayan fitar su yadubi Iftahal sosai yace
Chapter 20 · 0% Book details