← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 41

Sashe 35

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Nashiga 3 Ammin wallahi mutuwa zanyi kizo tun kafin kirasani " daga haka tasaki wayar tafad'i jin haka yasa Ammin miqewa cikin tashin hankali tafita zuwa part d'in Sarki Zaid tsayin lokaci Akeey yana parlour Yana kuka kamar ranshi zaifita sannan yamiqe yafita cikin sanyin jiki Kiran driver yayi yace yatada mota bayan driver yatada mota Akeey Zaffar yashiga yazauna amma yakasayin magana dubanshi driver yayi cikin tausayawa yace " se ha'kuri Yalla'bai Allah yajiqan baby ina zamu ? " police Station " kawai Akeey Zaffar yace cikin dashasshiyar murya "

Babu jimawa dafitar Akeey Zaffar su Momy suka shigo cikin tashin hankali suna shiga Suma su Ammin da Umma suka shigo hadda shi kanshi maimartaba kafin wani lokaci duk sunji abinda yakefaruwa sosai hankalin kowa yayi matuqar tashi sannan kowa yayima Aunty Bahijjat kyakkyawan zato amma abin mamaki banda Momy wato Mahaifiyar Akeey Zaffar cikin tashin hankali tadubi Aunty Bahijjat tace

" Damani zuciya ta takasa yarda da irin kulawar dakike bama baby shidama mugu bashida Kama wato kinyi hakanne tsawon shekaru sabida wannan mugun nufin naki sabida idan kika aykata kowa yace bazaki iyaba sabida anga kinabata kulawa matuqar to Allah yafiki wato kinga tunda kikazo ke babu alamar haihuwar sede kici kiyi kashi to in Sha Allah se Allah yatoni asirin ki azzaluma Kuma kisan" dakatar da ita maimartaba yayi dafad'in " haba Hajiya wa'innan kalaman basudace dakeba dukda bakashedan d'an yau to amma akwai d'aure kai da tantama cikin wannan lamarin sannan kisani har yanzu zargine ba tabbaciba sabida haka mubari hukuma suyi aykinsu idan akagane cewa Bahijjat itace ta aykata wannan ayka ayka to tabbas ni Sarki Zaid Ina bayan gaskiya Kuma zanyi jagora wajan yanke mata hukunci idan Kuma yazama batada hannu acikin lamarin tofa bazan iya maida mata kimarkiba cikin idanunta " daga haka yadubi Ammin da Umma yace " zanje police station d'in naji Yaya ake ciki " kafin maimartaba yafita Momy tasake cewa " ay wannan lamarin yafi qarfin police Kotu kawai zamu ananne za'ayi cikakken bincike idana qwararan lawyer Wanda zai tabbatar dacewa Bahijjat itace takashe baby Wai ga abu afili akeyin wata kwana "

Cikin 'bacin rai Ammin zatayi magana maimartaba yadakatar da ita yace " Kar kice komi kude kukula dahalin da Bahijjat take ciki nakuma san 'yata akwai imani dakuma yarda da qaddara kowace irice yau ga ranar karatun Saraki tazo ashe gara danabar shi yakaranci abinda yakeso kisanar dashi komi yanzu Kuma cike komi yakeyi yabaro yataho agobe shida iyalin shi dama nagaji dazaman shi a USA "
Daga haka maimartaba yafita jikin sanyin jiki

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_ 👌🏻🥰
🗡 *!!!FURUCI!!!* 🗡
💔💔💔
💔
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* 💓❣💘

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK

IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 63 to 64

Police station d'in Sarki Zaid yasaka aka kaishi sosai su Ammin suke lallashin Bahijjat ayanzu Kam kukanma takasayin shi sede shassheka kawai dasauke ajiyar zuciya kiranwayar Saraki Ammin tayi dede lokacin Saraki yanasaman shi shida Iftahal wayar kuwa tana parlour yaran suma suna parlour kowa da'irin kalar wasan dayakeyi aguje Irfan yaruga wajan d'aukar wayar shima Ibban haka d'auka Irfan yayi yajuya yanufi saman aguje bin bayanshi Ibban yayi ganin hakan yasa Suma su Islam suka bisu adede wannan lokacin Iftahal tana kwance kanta yana kan cinyar Maher yana shafa kanta cikin soyayya da kulawa shigowar yaran yasa Maher saurin duban su kafin yayi magana Irfan yace " wayar ka dad ana Kira " sake shigowa Kiran yayi dan Kiran nafarko yariga yakatse cikin sauri Maher yad'aga wayar sabida ganin Kiran Ammin jin abinda take fad'a cikin tashin hankali yasa Maher miqewa cikin mugun furgici datashin hankali salati yashiga saki hakan yasa Iftahal duban shi cikin damuwa suko yara tuni sunbar bedroom d'in tambayar shi Iftahal tashigayi tsayin lokaci sannan ya'iya cire wayar daga kunnan shi yadubeta cikin tsananin tashin hankali yace

" Sonahh akwai babbar matsala gobe zamutafi Egypt muduka kishirya komi " cikin tashin hankali tace " haba my blood kasanar dani abinda yakefaruwa mana inacikin tashin hankali dan Allah " ajiyar zuciya Maher yasauke Mai nauyi cikin raunin murya yace " Aunty Bahijjat ake tuhuma da lefin kisan Kai " zaro ido Iftahal tayi cikin matuqar rud'ewa cigaba dasanar da'ita komi yayi sosai Iftahal taji tashin hankali cikin mutuwar jiki Maher yafita zuwa yimusu Shirin tafiyar cikin sanyin jiki Iftahal tashiga had'a musu kaya

Egypt

Duk wani bincike da doctor yakamata yayi duk yayi lokacin da Akeey Zaffar ya'isa zuwa police station d'in doctor baizoba sebayan zuwan Sarki Zaid sannan doctor yadawo tare da jagorancin wasu police 2 agaban Sarki Zaid da Akeey Zaffar da Kabir dakuma sauran wasu police bayan doctor yazauna yafara jawabi kamar haka

_Tabbas Baby gubace taci amma kuma gubar wata irin gubace mai d'aukar lokaci kafin tayi illah zata iya d'aukar kamar kimanin 2 hours zuwa 3 hours sannan tayi illa idan kuma tatashi lokaci d'aya take kashe mutun wannan shine gaskiyar lamarin " jinjina Kai Kabir yayi yadubi Akeey Zaffar yace " kamar wane time ne ake kaima baby abinci Skul ? " Cikin dakushewar murya yace " wajan kamar 2 pm " jinjina Kai Kabir yayi sannan yasake cewa to kamar qarfe nawa take dawowa ? " 5 sabida hadda Islam take tsayawa sutashi 2 boko sushiga Islam 2:30 30 minutes shine lokacin dazasusamu bayan yin sallah suci abinci sannan sushiga " jinjina Kai Kabir yayi yad'anyi shiru sannan yace " awannin da doctor yafad'a sunyi dede da lokacin da Bahijjat takaima baby abinci Skul har zuwa lokacin da baby tadawo kunga 3 hours kenan kunga kenan har yanzu Bahijjat tanacikin zargi amma zamuyi bincike sosai cikin Skul d'in dan tabbatar da gaskiya idan baby taci wani abu adede wannan lokacin kafin taci abincin da Bahijjat takai Mata ko bayan taci tozamu gani zaku iya tafiya zuwa zuwa gobai zakuji daga garemu kafin wannan lokacin gawar baby zatacigaba dazama a hospital sabida qila wani binciken zai iya tasowa_ "

Miqewa Akeey Zaffar yayi cikin 'bacin rai yace " bazai ta'ba yiwuwa ba kubani gawar 'yata ayimata sutura haba wannan wane irin abune ? " dafashi Sarki Zaid yayi cikin tausayawa yace " kayi haquri Zaffar kamar hukuma suyi aykin su karungumi wannan qaddarar " daga haka yadubi ACP Kabir yace " Allah yasa muji alkairi " kafin sufita mahaifin Zaffar da qanin shi suka shigo cikin police station d'in cikin tashin hankali bayani ACP Kabir yayi musu dole Suma sukabar police station d'in zuwa gidan Zaffar a wannan daran ko runtse ido Bahijjat takasa balle tayi wani bacci idanun nata sunyi jawur dun kumbura sabida kuka Ammin ce taketa tausarta itako Momy tuni har tasanar ma lawyer nata yakuma taho bayan yaji bayanan nata sannan yanufi police station dan zantawa da Acp Kabir

Washegari

Su ACP Kabir sunje Skul d'in su baby dan tabbatar da gaskiyar abinda baby taci a jiya sun kuma samu duk wani bayane dasukeso daga nan suka nufo gidan Akeey Zaffar suna shiga ACP Kabir yayi sallama bakin babban parlour gidan wanda d'inbin jama'a suke cike daga 'yan uwan Akeey Zaffar zuwa na Aunty Bahijjat su Saraki kuwa suna hanya basu isoba duban kowa ACP Kabir yayi sannan yace

" Mun aywatar da cikakken bincike kuma munsamu tabbacin cewa baby babu wani abunda taci sede abincin da Bahijjat takai Mata kuma an tabbatar mana cewa baby batacin komi idan taje Skul har se ankawo Mata abinci daga gida dan haka Bahijjat mun kamaki da zargin lefin kisan kai zamutafi da ke mutsareki kisanar damu gaskiyar tayaya kika zuba guba cikin abincin baby Kuma maiye dalilin ki nayin haka zaki iya d'aukar lawyer wanda zai kareki a kotu sabida zamu miqaki kotu dan itace zata yanke miki hukunci dede da abinda Kika aykata "

ACP Kabir yana qarasa fad'ar hakan Aunty Bahijjat tasumai cikin sauri akayi kanta amatu'kar furgice Akeey Zaffar yayi kanta yanafad'in bari akaita asibiti " wata irin tsawa Momy tadaka mishi " karka sake kata'bata Kai wane irin Sha Sha Sha ne yarinya takashe maka 'yarka qwaya d'aya tilo sannan dan tafad'i kake wani rud'ewa to babu inda zaka k........ "

" Yakoma Zama dole akaita asibiti dan duba lafiyar ta karki manta zargi ne har yanzu babu tabbaci to kibar kotu tayi nata aykin " cewar Maher daya shigo yanzu daga haka yajuya yadubi ACP Kabir " kafin Maher yayi magana ACP Kabir yace

" Barka dawar haka Barrister Maher yau she kashigo qasar ? " fuska tamke Maher yace " yanzu babu jimawa kun kai wannan kes d'in gaban kotu ne ? "

Girgiza kai ACP Kabir yayi sannan yace " zuwa anjima zamu miqashi sabida mun riga duk mungama namu bincikenan semu saurari kotu kuma amma duk wasu alamu suna tabbatar da cewa Bahijjat mai lefice "

Rumtse ido Maher yayi cikin jin zafin zuciya yace " babu tabbaci har yanzu zargine nine lawyer mai kareta a kotu inaso abani belin ta har zuwa lokacin shiga kotu sabida cikin jikinta idan tashiga cikin tashin hankali sosai komi zai'iya faruwa zamu kaita asibiti yanzu idan tafarka zaku iya cigaba dayimata tambayoyin dakuke buqata " daga haka Maher yajuya shida kanshi yad'auki Aunty Bahijjat Iftahal dake bayanshi kuka kawai takeyi Ammin da Umma ma haka

Comments please
Chapter 35 · 0% Book details