← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 41

Sashe 40

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka Abdul yasaki yace " haba Momy to wallahi sede muje tare ay kinada hanyar samun fiyeda 30 million ga mahaifin ki Nan gakuma Yayanki nan Sarki Zaid gakuma Saraki d'an yayanki kaf d'in su kowa Don ne amma kibarni naje gidan yari Ina wallahi sede mutafi tare " wani irin baqinciki Hjy Himla taji yataso yatokare zuciyar ruri wayarta tad'auka da qyar ta'iya daga wayar cikin tashin hankali akace mata

" Hjy akwai babbar matsala fa Ayna tana raye kuma gashi gobene shiga kotu fa idan bakiyi wani abuba tofa tabbas munshiga 3 Hjy na tabbatar idan har akashiga kotu da Ayna gobe Kuma shima Barrister Maher yashiga tofa tabbas mukam munshiga cikin wahala nashiga 3 hjy Himla kinjefani cikin masifa " cikin wata irin murya Hjy Himla tace " garake shiga 3 kikayi nikuwa da cikin shiga 9 nike ayanzu kuwa nashiga 1000 bama 100 tabbas yazama dole nabar qasar nan ayau basegobeba kema kiyi takanki " daga haka takashe wayar tashiga cikin bedroom aguje shima Abdul binta yayi agujan

Ahankali Alhaji Tukur yake bud'e idanunshi saukesu yayi kan Maher cikin razana yazaro ido murmushi Maher yayi yace " kayi mamaki ko ? kad'an daga cikin basirar Barrister Maher Ibban Islam kuzo yaganki " duban yaran yayi cikin matuqar mamaki yace tayaya haka tafaru ? " Murmushi Maher yayi yace

" Kafara bani wannan amsar tukun da 500,0000 da 10 millions wanne yafi ? Cikin rawar baki yace 10 millions " murmushi Maher yasakeyi sannan yace " to sune nabiya akamin ayki 2 nafarko aka dawomin dayarana na biyu aka qwamusomin Kai wa'inda kasa suka sacemin yara suka kaimaka sune nasaka suka koma sukasake d'akkomin yarana har cikin bedroom d'in dakuka kaisu sauran bayanan yadda akayi zakajisu a kotu gobe in Sha Allah yarana muje ko dama nace ma mom d'in ku in Sha Allah zandawo Mata daku nan kusa "

Dariya Ibban yayi yaje kusada Alhaji Tukur yace " kagani dama munce maka Allah zaibamu mafita tunda mundogara dashi kaima idan dashi kadogara zamu gani " Jan kunnan shi Islam tayi tace " Ina Ina Ibban wannan baiyi Kama da wanda yadogara ga Allah ba daya dogara dashi dabaze tutar dakowaba balle qananan yara kamar mu muje gida d'an uwana Ina kewar Irfan da Iman muje muji abincin mom d'in mu Mai dad'i ta sumbacemu kamar yadda tasaba kullum sau 3 yau gashi iya 1 mukasamu " riqe hannun ta Ibban yayi yace " zamusamu na 2 yanzu idan munje " murmushi Maher yayi yace " kagani Alhaji Tukur har abada cikin farinciki zamu kasance kagudu kafin zuwa gobe idan zaka iya "

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_
🗡 *!!!FURUCI!!!* 🗡
💔💔💔
💔
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* 💓❣💘

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 75 to 80

LAST PAGE

Maher yanayin parking cikin parking space d'in masarautar yaran suka bud'e mota sukayi ciki aguje suna qwala kiran Mom Irfan Iman kafin wani lokaci masarautar takaure da farincikin dawowar su Ibban duban shi Iftahal tayi cikin farinciki tarungume shi cikin wata irin murya tace " nagode ma Allah dayabani miji kamarka tabbas FURUCI!!!!!! na yazamarmin alkairi "
Farinciki akaitayi cikin masarautar bayan nan Barrister Maher yamiqa Alhaji Tukur wajan police kafin zuwa lokacin sauraran shari'ar yabada damar atuhumeshi sosai shidawaye suka aykata wa'innan lefukan da yaqi cewa komi amma dayaji wuya dole yafad'a jin cewa Hjy Himla tanacikin wannan lamarin yasa Maher girgiza sosai yaji tashin hankali marar misali domin kuwa harda hawaye yazubar sosai baqinciki yasa yakasa sanar da kowa hakan amma gana ganin shi kasan yanada damuwa sosai cikin zuciyar shi Iftahal tafaminci hakan amma tayi duk yadda zatayi yacemata babu komi

Hjy Himla da Abdul suna Shirin guduwa aka cafkesu sosai hjy Himla tashiga kururuwar kuka tana neman d'auki ko sauraranta basuyiba shima Abdul kukan yakeyi kamar ranshi zaifita

Kamar yadda alqali yace 13 February za'adawo dan sauraran wannan shari'ar togashi Allah yanufa anshigo da Alhaji Tukur da Hjy Abdul Ayna cikin tashin hankali Kaka mama Sarki Zaid Umma Ammin dasu Aunty kurrat kowa yamiqe cikin matuqar mamaki darajana kowa yadubi Maher saurin kawar dakanshi yayi sabida bayason su kashemai gyuwa wajan gabatar da shari'ar "

Bayan Alqali yazauna akafara gabatar da shari'ar kamar haka

Barrister Maher yamiqe yace " yamai girma mai Sari'a ayau inatafe da manyan hujjojin dazasu tabbatar da wa'inda sukayi wannan kisan idan kotu tabani dama zanyima Alhaji Tukur wasu tambayoyi " kotu tabaka dama juyawa yayi ya'isa gaban Alhaji Tukur duban shi yayi sosai cikin damuwa Alhaji Tukur yajuya yadubi Ammin sannan yadubi yaranshi yaduqar da kanshi cikin tsananin nadama ajiyar zuciya Barrister Maher yasauke yace

" Alhaji Tukur kasanar da kotu dalilin dayasa kuka kashe baby Kuma kai dasuwaye ? " Cikin raunin murya yace

" Nikam babu tsarin kashe baby cikin shirina ni matar ka da yaranka nikeson kashewa Kai Kuma nasaka rayuwar ka cikin tashin hankali kamar yadda nayi abaya dani da Hjy Himla dakuma wadda baikamata nafad'i sunanta ayanzu ba sabida tuni ita tatuba tunkafin zuwan wannan ranar ta tonon asiri agaremu dan haka babu buqatar sake sakota cikin lamarin mune muka sakaka cikin wannan muguwar lalurar Maher tasanadinka nakashe mutane dayawa nazama sanadin kwantawa ciwon kakanka nine nasaka aka kashe doctor darman Kuma nasaka aka kashe mahin wato wanda yakashe doctor darman bayan ankamashi anbashi wuya sosai amma Koda sunana yaqifadi har nakwanta ciwo bayan nawarke nasaka aka kasheshi duk dan dalilin abu 1 shine Mahaifiyar ka nasota so mai tsanani amma taqini taje ta auri mahaifin ka hakan yasa naqudiri niyyar sakata cikin masifa da tashin hankali nine nayi asirin dabata sake haihuwa ba tun daga kanka

Maher nine nasaka aka rabamin qwaqwalwar ka biyu tahanyar tsafi itakuma Hjy Himla ta turomaka manyan aljanu sannan nahad'a Kai da doctor darman yake canza allurar da akeyimaka sannan nine nasaka akamaka muguwar allurar datasaka kayima Iftahal wannan mugun fyad'en Kai Kuma nasaka ayimaka wannan allurar wadda zata kashe qwayoyin halittar haihuwar ka amma se matarka tasauya allurar bayan ta amshi ta hannun Doctor darman tabada ta bacci akayimaka

Bayan na warke muka had'a Shirin sake tarwatsa farincikin dakuke ciki nida Hjy Himla ananne shirin kashe baby yashigo sabida Hjy Himla tayi alqawarin kuntatama gimbiya Bahijjat shiyasa tafara takanta kafin mudawo kan ku munyi amfani da Ayna ne sabida qiyayyar damukaga tanayima gimbiya Bahijjat tabbas batasan suwaye muba waya kawai mukeyi nine wanda yanemo gubar Hjy Himla kuma itace tasaka wannan gubar cikin yoghurt d'in sannan akabama qawarta taje tasaka cikin motar Ayna itakuma Ayna taje tabama baby yoghurt d'in tasha kagin kagano komi yasa mukasaka a harbe mana Ayna dan kar asirinmu yatonu bayan nan mukasaka aka sacemin yaranka biyu wannan shine gaskiyar lamarin Ina roqon kotu datayimin sassauci natuba bazan sakeba

" Sosai kotu takaure da la'antar su Alhaji Tukur su Kaka kuwa kuka kawai sukeyi sabida mugun baqin ciki Ammin kuwa tafi kowa kuka Sabida jitakeyi duk tasanadinta ne komi yafaru duban Hjy Himla Barrister Maher yayi yace " Momy kinadaja akan abinda Alhaji Tukur yafad'i ? "

Cikin matsanancin kuka tace " a a babu gaskiya ne duk abindayafadi dan Allah Saraki kayafemin nacutar dakai nasan nima ayanzu kasheni za'ayi dan Allah ga Abdul nabaka amanar shi nasan Kai Mai maida alkairi ne akan sharri yaciyo bashin banking dan Allah kabiya mishi kagyaramin rayuwar shi Ni nakasayin haka kwad'ayin abun duniya yamakantar dani Maher katayani roqon su mama da Yaya Zaid da Mahaifiyar ka suyafemin dan Allah sannan tabbas nasan Zaffar da Bahijjat bazasu iya yafemin ba amma dukda haka dan Allah kace suyafemin "

Allah sarki zuciyar dake cike da imani tana saurin manta sarri rungumai ta Barrister Maher yayi yana kuka yace " nayafemiki Momy duniya da lahira suma zasu yafe Miki in Sha Allah Kuma nayi miki alqawarin biyan banking wannan kud'ad'an Koda duka dukiyata ne zanbayar Momy har abada ke uwace agareni har namutu bazan ta'ba kallon Abdul amatsayin maqiyiba har abada shid'in Yaya nane " kuka Abdul yasaki sosai yadubi Hjy Himla amma yakasayin magana tashi Kaka da mama sukayi suka fita dan Kam bazasu iya kalloba gyaran murya Alqali yayi yace

" Duba da kwararan hujjojin dakuma fad'in gaskiya damasu lefi sukayi wannan kotu Mai adalci zata yanke hukunci kamar haka " Alhaji Tukur kotu tayanke mishi hukuncin kisa tahanyar harbi da bindiga Hjy Himla kotu tayanke mata hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari tareda ayki mai wahala Ayna da 'kawar Hjy Himla kotu tayanke musu hukuncin d'aurin 20 yrs agidan yari kooooooootuuuuuuuu "

Ihu Alhaji Tukur yasaka hakama sauran sunaji suna gani akasakasu a mota Abdul yana kallo katafi da Momy shi durkushewa yayi yasaki kuka mai qona zuciya sosai su Kaka sukayi baqinciki to amma yaya zasuyi

Bayan kwanaki 2 Aunty kurrat tazo ganawa tayi da Maher shi daya tasanar dashi gaskiyar lamari takuma roqeshi yafiya yakuma yafe mata sannan yace tabar maganar iya ita dashi kawai

Sosai Maher yaqarajin tsananin son Iftahal shiryamusu zuwa Nigeria yayi hadda Abdul bayan yabiya mishi bashin banking sosai su Abba da Ummi sukayi farincikin zuwansu sabida tsananin farinciki sunma rasa Ina zasusakasu duban Iftahal Zayyat yayi yace " iyye Iftahal kece haka ah lalle yazama dole nacanzama matata cima dan kam nafiso tafiki " dariya kowa yasaki seda sukayi 5 months a Nigerian alokacin Abdul yasamu mata Yar dan uwan Ummi Kuma akabashi sannan suka koma Egypt
Chapter 40 · 0% Book details