← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 41

Sashe 2

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" ayko shine babban marar adalci tunda gashi yasaka rayuwata cikin masifa daga yin FURUCI!!!! cikin 'kawayena shikenan yazamarmin masifa to wallahi bari kaji zan...... " afusace wani security yazo gurin cikin zafin rai yad'aga hannu zai mareta had'ida fad'in " kinatsu ba'ayimana hayaniya anan cikin harshen turanci " cikin sauri Shanwul yace " sorry Matar oga ce fa " saurin sauke hannunshi yayi yana gaidata cikin matu'kar tsoro tabi bayan Shanwul

har zuwa hawa na 5 sannan suka shiga cikin wani had'add'an parlour nuna mata wajan zama yayi sannan yace

" nan shine parlour ki zaki iya shiga kowane bedroom amma banda wancan sabida kayan motsa jikin prince ne aciki yana motsa jiki duk safiya dakuma yamma daga hawa na 6 yake sakkowa nan yana shan black tea akan wancan dining d'in kullum safiya yana sakkowa ya kalli News a wannan parlour kullum dare idan kina bu'katar wani abu nizaki sanar mawa karki manta bayason hayaniya k.... "

jin takun sakkowar Prince yasa Shanwul yin shiru saurin du'kawa yayi yana kwasar gaisuwa cikin rikicewa yake nunama Iftahal tadu'ka amma tayi 'banza Sigarin dake hannun shi yazu'ka yabusar da haya'kin seda yakusa shanyeta sannan cikin tsadaddiyar muryar shi yace

" Wanna fa daga ina ? "
Cikin sauri da rawar jiki Shanwul yace " Allah yataimakeka wadda kace akaima sadakin 2.1 million kuma d'aura maka aure da ita ayanzu itace " hannu yanuna ma Shanwul alamar yafita bayan fitar Shanwul Maher yasake zu'kar Sigarin shi sannan yadu'ko dede fuskar Iftahal yahura mata haya'kin Sigarin yace

" Welcome "

daga haka yami'ke yanufi d'akin motsa jikin shi bin bayanshi tayi da kallo tanasakin tari sabida haya'kin daya busha mata gawani irin bugun zuciya datakeji sabida ganin suffar Maher cikin zuciyarta tace

" anya wannan mutun ne tuda nike banta'ba ganin kyakkyawa kamar shiba ko acikin finafinan India gaskiya babu kamar shi " sekuma tace nashiga 3 yanzu yaya zanyi wai dagaske nazama matar aure ? "

Daga Al'kalamin....🖊

NPEEDY A AJI
🌹Mamyn Zarah 🌹

Comments and shine please

yawan comment yawan typing

*Allah kaji'kan Zarha*

love u all fans 😘🌹
🗡 *!!!FURUCI!!!*🗡
💔💔
💔
*(((((Murd'add'iyar Soyayya))))* 💓❣💘

Story and written
By
NPEEDY A AJI 🌸mamyn Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
and
Lovely
Daughter
*Zarah*

>>>>>>>>> 👌🏻>>>>>>>
We are together all fans 🤝🏻👌🏻

KAFA'DI ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 nayi Rayuwa dake
2 sanadin accident
3 Sakayyar cuta
4 Fufaffiyar zuciya
5 Hayatul mahayat
6 Mugun Sartse

Loading....🖊

🗡💔FURUCI!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

🅿 3 to 4

' kwafa tayi tace " lalle kam wallahi baze yiyuba haka kawai zakafito ne gashi ko wayana tanacan tayaya zankira 'kawayen nawa ? " tun tana zaune har tagaji dazaman Maher bai fitoba kwanciya tayi saman lafiyayyar cushion d'in harta cire rai dazai fito setaji takun shi cikin sauri tami'ke dake zuciyarta tayi tasha gabanshi tace

" Maher kake kowa ? kasani nifa bazan zauna cikin gidannan ba hauka akeyi aure batare da yardata ko sanin iyayena ba to wallahi bazai yiwuba kasan wannan dan haka yanzu zanbar gidan nan basai anjima ba k....."

Hannu yasa yatureta gefe batare dayace komiba yayi taku d'aya zuwa 2 yatsaya ahankali yace " ciiizoii zoka koya mata yadda akai natsuwa cikin gidan *Saraki* " wannan shine sunan da iyayen shi suke kiranshi dashi aguje wani 'katon kare yafito daga room din motsa jikin shi yayi kan *Iftahal* cikin matu'kar razana tajuya aguje ayko yabita shiko *Maher* hayewa sama yayi abinshi fuskarnan tashi atamke babu alamun fari'a sosai karan yakebin *Iftahal* tun tana ihu harta gaji tayi shiru abin mamaki datayi shiru se Karan yajuya datayi ihu seyataso mata dole tanatsu kamar wata marainiya sewasu irin hawaye dasuka shiga gangarowa daga cikin idanunta tashi tayi ahankali takoma kan cushion ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya

Egypt

Babbar masarauta ce maicike da bayi Sarki Zaid sarkine mai cikakken iko ga tausayi da kyautatawa talakawan shi yanada mata 2 Hajiya Karimat itace uwar gida mace mai tausayi da son jama'a gasanin yakamata tanada yara 4 duka mata *Faheemat Sumer kurrat Bahijjat* sunada matu'kar had'in Kai babu maijin kansu *Faheemat da Sumer* sunyi aure saura *kurrat da Bahijjat* ganin yadda Sarki yake matu'kar son haihuwar namiji yasa Hajiya Karimat sashi 'karin aure ko Allah zai bashi segashi kuwa Yana auran Hajiya Batol tahaifi Maher ayko gabad'ayan su suka dauki son duniya suka d'aura mishi daga Sarki Zaid Hajiya Karimat dayaranta dakuma mahaifiyar Sarki Zaid wato Mama lokacin da akahaifi Maher babbar Yar Sarki Zaid tanada kusan shekara 15 sun girmi Maher sosai sede Bahijjat itace tabashi 4 yrs babu abinda zai nema yarasa tun yana 'karami yayyen shi suna matu'kar son shi haka Marmy wato Hajiya Karimat tamkar itace tahaifeshi tunda Hajiya Batol tahaifi Maher batasake haihuwa ba

Amma lokacin dayagama secondary School seyasamu wani mugun ciwo wanda idan yatashi bayasanin inda kanshi yake Kuma duk wanda yake kusa dashi idan yakamashi seyaga baya motsi dawowa yakeyi tamkar mahaukaci kullum ciwon 'kara gaba yakeyi ko yaya yayi farinciki seciwon yatashi hakan yakesa mahaifiyarta shi kuka da damuwa sosai amma natane yafito fili Sarki Zaid 'bakin cikin nashi yafi haka ganin wannan halin da iyayen shi suke ciki yasa yaza' bi yin karatu a USA sabida yayi nesa dasu amma duk da haka duk 'karshen wata Sarki Zaid yanazuwa da doctor dan duba lafiyar shi

Kafin zuwan wannan lokacin an keshi 'kasashe daban daban dan gano matsalar shi amma ina wasu suce yasamu matsalar 'kwa'kwalwane wasu suce matsalar zuciya ce hakade amma babu wani sauyi se wannan doctor da'ake d'akkowa daga India duk 'karshen wata to shine idan yamishi allura ciwon yake yin kamar 2 weeks bai tashiba Cikin damuwa Hajiya batol wato Ammi tashiga shashen Sarki Zaid bakinta d'auke da sallama amsawa yayi sannan tazauna duban shi tayi cikin raunin murya tace

" Abbeen *Saraki* dan Allah inason zuwa USA idan zaka ganin *Saraki* dan Allah zuciyata takasa jurewa inason ganin shi ka taimakamin kafin zuciyata takumbura sabida damuwar rashin ganin shi "

Jinjina Kai *Sarki Zaid* yayi yace
" Haba Ammin *Saraki* kinsanfa *Saraki* bayason yin farinciki sabida ciwon shi Kuma nasan inde yaganki seyaji dad'i sosai kinga kuwa hakan zaitadamai ciwo ina matu'kar son ya kammala karatun shi kinga koda yaushe baya yakeyi tun 2 yrs dasuka wuce yakamata yagama amma wannan ciwon nashi yahana kiyi ha'kuri Ammin *Saraki* kinji hakama *Marmyn* shi take matsamin akan zataje amma sede nabata ha'kuri "

Dafe 'kirji ta Ammi tayi tanajan numfashi da 'kyar ganin haka yasa Sarki Zaid rud'ewa sosai kamata yayi takwanta saman cushion kiran doctor yayi yadubata sannan yadubi Sarki Zaid yace

" Yace gaskiya tanada damuwa sosai wadda take barazanar ta'ba zuciyarta ga shi jininta yahau sosai Allah ya'karamaka nasara yakamata anema mata abinda takeso jinjina kai Sarki Zaid yayi ya sallami doctor sannan yazauna kusada ita yakamo hannunta yasaka cikin nashi yace

" Shi kenan Ammin *Saraki* zamuje tare nanda 6 days sekiyi shirye shiryen dayakamata "

Murmushi Ammi tayi tataso ahankali tarungumo Abbee tanasakin ajiyar zuciya shima ajiyar zuciyar yasauke cikin sauri Marmy tashigo cikin part d'in Abbee ganin Ammin rungume da Abbeen yasata sakin ajiyar zuciya zama tayi tace

" Masha Allah kinji yadda hankalina yatashi kuwa ? danaji ance ankira doctor dama nalura kinada damuwa amma sekidinga cewa babu komi "

Murmushi Ammi tayi Nan Zarki Zaid yasanar da Marmyn akan zasuje ganin *Saraki* da ita sosai tayi farinciki sannan itama taro'ki alfarmar aje da ita zuwa gaba babu yadda Sarki Zaid ya iya dole ya amince dahakan dan kartaga anyi mata badede ba kafin wani lokaci Ammi tafarayin shirye shiryen zuwa ganin gudan jininta 'kwaya d'aya tilo murmushi Bahijjat tayi tace

" Ammi gaskiya *Saraki* zaiyi farincikin ganin ki Ammi nimafa inason ganin 'kanina " shiru Ammi tayi tana nazarin abubuwa sannan tace
" Bahijjat nikam tsoran yin farincikin nashi nikeyi amma gashi ina matu'kar son ganin shi Bahijjat kode nafasa zuwane " ta'karashe fad'ar hakan cikin muryar kuka tacigaba dacewa " ya Allah kayayema wannan bawa naka wannan muguwar lalurar shima yasan dad'in farinciki a cikin rayuwar shi Allah sarki *Saraki* koyaya yakejin zuciyar shi tayaya zaka rayu babu farinciki ga mugun ciwo maisawa amanta komi waiyyo Allah ya Allah kanunamin ranar da *Saraki* zai warke yakoma cikakken mutun "

Saurin barin parlour tayi cikin kuka cikin matu'kar tausayawa Bahijjat tabita da kallo itama hawayen ne suka gangaro daga cikin idanunta d'aga wayarta tayi takira layin *Maher* har takusa 'katsewa sannan yad'aga baiyi magana ba duk da yasan Aunty shi Bahijjat ce ajiyar zuciya tasauke tace

" Ina fatan *Sarakin* mu Yana cikin 'koshin lafiya amm dama sanar dakai zanyi cewa Abbeen tareda Ammin zasuzo nanda kwana 6 in sha Allah to kabayar da abu namusamman akawo min " kashe wayar yayi batare dayace komiba itako Bahijjat tayi hakan ne sabida koda zai farinciki yayi yanzu kafin zuwan Ammi dan kar taga tashin ciwanshi gara yatashi kafin taje sabida hawan jinin dake gareta yanzu

USA

Kasa d'aura agogon hannun shi *Maher* yayi sabida kanshi dayaji yafara saramai gawani irin bugu da zuciyar shi takeyimai sabida d'an wani sanyi dayaji akan zuwan Ammi komawa yayi yazauna bakin bed yamarasa mai keyimai dad'i 'karuwa ciwon kan yafarayi had'ida bugun zuciyar wanda yasa *Maher* kasa zaman dole yami'ke yafara kaiwa da komowa cikin bedroom d'in a parlour kuwa Shanwul ne yashigo shida wani Security hannun su d'auke da banyan bag guda 3 cikin bedroom suka Kai suka aje sannan wancan yafita shikuma Shanwul ya'karaso gurin *Iftahal* mi'ka mata wayarta yayi had'ida abincin dayasiyo mata sannan yace

" Ranki yadad'e ga kayanan Yalla'bai yace akawo miki tareda 'kawarki Salma mukaje taza'ba miki sannan yace idan zakishiga Skul kisanar dani naso nakaiki nasaka miki no ta cikin wayar ki Kuma duk abinda kike 'bukata kisanar dani akwai kayan abinci kalakala cikin kitchen namiji ne yakeyima Yalla'bai abinci Amma yanzu yace yatafi akawo mace zuwa gobe zatazo kullum masu ayki sau 3 suke gyaran wannan part d'in dana sama yakamata kishiga ciki kinga dare yafara nasan Yalla'bai yakusa sakkowa kallon News "
Chapter 2 · 0% Book details