← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 41

Sashe 31

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK

IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 55 to 56

Sakata yayi a mota Kai tsaye yanufi asibiti da ita suna isa aka amsheta cikin sauri duba abinda yake damunta akashigayi tsayin lokaci sannan doctor yafito yace mishi yasameshi a office babu musu yabishi Zama Zayyat yayi cikin damuwa duban shi doctor yayi yace

" Kamar kune nabaku shawara wasu lokaci dayawuce amma abin mamaki abin baiko canzaba Ina ganin ma kamar bakubi shawarar tawaba to gashi yau abin yayi zafi sosai har yakaita ga suma idan kasan bakasontane to karabu da ita ta auri wanda zai iya biya mata buqatun ta " ajiyar zuciya Zayyat yasauke yace " bahakabane doctor itace takasa fahimta amma dan Allah kayi mata irin wannan bayanin ni a 'bangarena babu matsala " jinjina kai doctor yayi yace nafahimta adaran wannan ranar a Asibitin suka kwana ahankali Aunty Shukura take bud'e idanunta tasaukesu kan Zayyat rumtse idon ta tayi cikin raunin murya tace

" Dan Allah mijina kataimakeni bazan iya jure wannan azabar ciwon marar ba qaruwa yakeyi ankai inda bazan iyaba dan Allah kabani haqqina " sosai Zayyat yake dubanta cikin mamaki kafin yayi magana Abba da Ummi suka turo qofar cikin sauri Ummi tanufi bed d'in Zama tayi takamo hannun ta tashiga yimata sannu dede lokacin yaya Ibrahim da matar shi suka shigo akashiga yimata sannu tashi tayi zaune tace " nikam naji sauqi sosai muje gida tashi Zayyat yayi yaje yasanar da doctor akabasu sallama duka suka nufi gidan haddasu Abba cikin mota Aunty Shukura tadubi Zayyat tace " dan Allah karka sanar dasu Abba abinda yake faruwaba nayima alqawarin gyara komi dan Allah "

Jinjina kai yayi suna Isa gida Ummi tafito takama Shukura suka nufi ciki bayan tazaunar da ita tadubeta tace " sannu kekuma naki laulayin dahaka zezo ? " Saurin dubanta Aunty Shukura tayi sekuma ta kauda kanta cikin zuciyar ta tace " nida babu abinda yata'ba shiga tsakanina dashi tayaya zanyi ciki amma in Sha Allah yana gaf dazuwa " afili kuwa cewa tayi " a a Ummi nikam banida komi " sosai Ummi tasake dubanta tace " kode har yanzu baki canza halin nakiba ? to ay shikenan ko Iftahal datake qanwa agareki kuma nasan kinfita kwanciyar hankali sabida ke babu wani qulli a tsakanin mu amma itafa fushi sosai Abbanku yayi da ita nikuwa umarni nabi to Yaya zanyi amma kullum Iftahal tana cikin raina kuma akullum cikin yimata addu'a nike Allah yatsaremin ita daga dukkan sharri ayanzu haka nasamu labari wajan qawarta Salma cewa tana nan daciki kuma sosai take samun kulawa mai kyau wajan mijinta Kuma tabada natsuwa wajan karatunta tayi haquri ta amshi tata qaddarar amma ke kinqi amsar taki qaddarar Shukura maiye haka "

Kuka sosai Aunty Shukura tashigayi tace " Allah Ummi tun ranar da Abba yayi min fad'a naroqi yafiyar Zayyat kuma nashiga sauke duk wani haqqi nashi kuyi haquri in Sha Allah komi yawuce " tashi Ummi tayi tashiga sakamata albarka sannan tayi mata sallama tafita komawa gida su Ummi sukayi a cikin mota Ummi tadubi Abba tace " tun jiya naso sanar dakai cewa Iftahal cikine da ita tana buqatar addu'a daga gareka sannan yakamata kashirya niyyar sauke wannan alqawarin daka d'aukar Mata alokacin datayima albishir akan son auran Zayyat nasan bakadaga cikin masu karya alqawari "

Duban ta Abba yayi yace " Allah yarabasu lafiya sannan batun alqawari ay akan Zayyat nayi ba akan Iftahal ba dan haka bai shafetaba " ajiyar zuciya Ummi tasauke tace " ayko ita yashafa Alhaji bari natuna maka cewafa kayi kayi alqawarin duk ranar dakika samu ciki kika haihu to tabbas idan har Ina raye nine wanda zanfara tauna dabino nabama yaron kafin kowa " cikin murmushi Iftahal tace maka to Abba idan Kuma ba a gari d'aya mukeba lokacin ? " kamo hannun ta kayi ka sumbata sannan kace " Koda ba a qasa 1 mukeba zanzo duk inda kuke dan cika wannan alqawarin kaga kuwa babu sunan Zayyat cikin wannan alqawarin dakayima Iftahal "

Shiru Abba yayi nawani lokaci sannan yace hakane kuma zancika wannan alqawarin daga yau nabaki damar yin waya da ita sabida idan tahaihu naji dawuri amma karkiyi tunanin nasauke fushina akantane a a yananan " murmushi Ummi tayi tace " nagode sosai da wannan damar daka bani cikin zuciyar ta kuwa cewa tayi " in Sha Allah sanadin abinda Iftahal zata Haifa zaisa kasauke wannan fushin naka "

A 'bangaran Shukura kuwa tashi tayi tashiga bedroom d'in ta tayi wanka tashirya dukda jikin nata babu qarfi fitowa tayi daniyyar shiga Kitchen dede lokacin Zayyat yashigo hannun shi riqe da ledoji ajewa yayi saman cushion yanufi wajan Shukura yawota yayi jikin shi yarungumai ta sosai yace " ga abinci nan nasiyo mana kizo muci seki Sha magani sannan yau zan tambayi abinda ban ta'ba tambayaba shine ina buqatar yau kibani haqqina na aure " murmushi Aunty Shukura tayi tace " bakada matsala akan wannan kasani ni takace kaga kenan komi nawa nakane nima ina roqon wata alfarma dan Allah daga yau karka sakecin abincin waje " murmushi Zayyat yayi yace " angama Aunty na " tamke fuska tayi tace " gaskiya kabari bana buqatar wannan sunan daga gareka kabari su Usman suce " murmushi yayi yaja hannun ta zuwa wajan cin abincin

a wannan ranar seda Zayyat yasa Shukura goge mishi wannan kalmar ta yaro sosai ya gurjeta kamar babu gobai seda yakira mata doctor dan kam yayi Mata illah sosai tun daga wannan ranar Aunty Shukura tasan cewa Namiji baya kad'an sosai takenuna ma Zayyat soyayya

Egypt

Cikin rud'ewa aka kwashi Alhaji Tukur se asibiti bayan wasu lokaci doctor yafito yace " gaskiya Alhaji yasamu razana sosai hakan yazama sanadin shigar shi cikin wani mawuyacin hali wanda ayanzu zai d'auki tsayin lokaci batare dayasan maike faruwa cikin duniyar ba Kuma Koda zaku fitar dashi qasashe sama da 100 bazaisa yatashi anan kusaba " kuka yaranshi suka saki itako matar shi cewa tayi gaskiya ne ku kuka yagani amma baniba idanhar alhaki ne yafarabin Alhaji tokam baimaga komiba zanyi jinyarshi nawasu lokuta shima sabida darajar aure amma idan naga abin bana qare bane tofa zan tattara inawa inawa nayi gaba "

A cikin masarautar Sarki Zaid kuwa adede lokacin da Alhaji Tukur yafad'i adede lokacin Abba yatashi wato Kaka cikin mamaki yami'ke tsaye yashiga zagaya cikin bedroom d'in kukan farinciki yasaki yadubi gabas yayima Allah sujuda yadad'e yanayin addu'o'i sannan yamiqe yafito parlour cikin mamaki Mama da Hjy Himla da Umma suka shiga kallon shi tamkar a mafarki tashi mama tayi taje ta rungumo shi sannan ta tabbatar da gaskene kukan farinciki tasaki Suma su Umma tashi sukayi suna sakin nasu kukan farincikin cikin sauri Umma tafita part d'in Sarki Zaid tanufa tasanar dashi takoma part d'in Ammin maimartaba aguje yarugo wajan ganin mahaifin nashi hakama Maher da Ammin dakuma Iftahal amma ita takasayin gudu sabida cikin jikinta dogarawa ma kafin wani lokaci tunin part d'in yaciga da jama'a

Tsayin lokaci ana taya jaje sannan Kaka yashiga karanto addu'a had'ida sake miqama Allah godiya sannan yashiga tambayar ankai su Bahijjat dakunansu aka tabbatar mishi dacewa ankaisu babu jimawa duban Maher yayi yazo zonan Saraki na Ina matar taka kuzo naji diminku nasamuku taku albarkar " kama hannun Iftahal Maher yayi suka isa gaban Kaka rungumai su yayi yashiga saka musu albarka cikin farinciki bayan nan yadubi Hjy Himla yace

" Ke ina wannan Sha Sha Shan d'an naki yanatsu kuwa ? koda yake babu alama sabida tunda nakwanta banganshi yashiga gaidaniba ko sau 1 hakan ya tabbatar min dacewa har yanzu bashida hankali " tamke fuska hjy Himla tayi duban Kaka Maher yayi yace " tabbas kuwa Kaka nima nasheda wannan rashin hankalin nashi d'azu nakamashi yanaqoqarin yima Aunty Bahijjat fyad'e shine nayimai duka nasa aka rufeshi kafin ayimai hukun da anan gaba bazai sakeba agaban Mahaifiyar tashi akayi " zaro ido Hjy Himla tayi tace

" Kajimin munafukin yaro to ni bansan komi ba tun d'azu nike neman Abdul ashe kaine kasa aka rufemin yaro to wallahi kayi gaggawar sawa abud'e shi dan wallahi nasan Abdul bazai aykata hakan ba " sosai Maher yayi mamakin FURUCIN hjy Himla kafin yayi magana kaka yadakamata tsawa dafad'in

" Yimin shiru Himla tabbas Abdul zai iya aykata hakan dan nasan halin shi balle yanajin haushin an hanashi auran Bahijjat Kuma nasan Saraki ba zeyimai qazafiba ribar mai zaici idan yayi ma Abdul qazafin fyad'e kinsan kuwa hukuncin wanda yayi yunqurin fayd'e ? to abune mai qirma hakan yasa zansa ayimai hukunci irin wanda agobe ko ance yasake baze yiba dan haka nabada umarnin gobe dasafe afito da Abdul gaban kowa afad'i irin lefin dayayi sannan a kwaramai ruwan sanyi atubemai riga azaneshi da wannan zabgegiyar bulalar bulala 505 "

Jin haka yasa Hjy Himla miqewa cikin 'bacin rai tace " gaskiya Abba idan akayimin haka toni wallahi ba'amin adalciba dama ni kam nalura antsaneni dagani har d'ana cikin masarautar nan dan haka idan har akayima Addul wannan wulaqancin to zan tattara nida d'ana mubar mugu masarautar gaba d'aya tun....... " Kafin taqarasa Sarki Zaid yatashi yasauke mata marika guda 2 cikin fusata yace
Chapter 31 · 0% Book details