← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 41

Sashe 34

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Abba nasauka daga jirgi akazo tarbarsu anashigowa cikin harabar gidan Abba yadubi Ummi yace " ikon Allah kenan lalle yau duk wata tantamata ansharemin ita wajan mamakin kud'in sadakin da Maher yabiya akan Iftahal wannan irin gida haka " murmushi Ummi tayi kafin tayi magana aka bud'e musu murfin mota suka fito har cikin part d'in su Iftahal akakaisu kwance Iftahal take amma cikin sauri tami'ke danufin Isa wajan su Ummi juwar dataji tad'ibaita yasata dole takoma tazauna cikin sauri Ummi taqaraso ta rungumai Iftahal hakama Abba kukan farinciki Iftahal tasaki tsayin lokaci suna ahaka sannan suka zauna kafin wani lokaci akacikasu da nau'in abinci kalakala babu jimawa Sarki Zaid da Umma dasu Aunty Faheemat suka iso suna shiga Akeey Zaffar da Aunty Bahijjat da baby su Suma suka iso kafin wani lokaci gida yacika da d'inbin jama'a kamar yadda Abba yayi alqawari Kuma yacika shine wanda yatauna dabino yabama kowane jariri sosai su Maimartaba sukayi murnar ganin Abba cike dafarin ciki agun 'yarshi bayan yagama yadubi Maher yace " kayi musu huduba " cikin jin kunya Maher yace " a a Abba nabaku dama " murmushi Abba yayi yace to Ina godiya da wannan kyauta to amma wane suna kaza'bar musu ? murmushi Maher yayi yace " mazande kasamusu Abba na da Abbee na amma matan nabaku dama dubada su 3 ne kakannin nasu ga Umma ta gakuma Ummi na sannan kuma Ammi na bansan waze ha'kura ba "

Dariya kowa yasaki cikin murmushi Ummi tace a a ni nahaqura zuwa gaba nasamu tawa takwarar " dariya suka sake saki duban Sarki Zaid Abba yayi yace " to nabarmaka matan kayi musu huduba kaine kasan sunayen nasu kaga kenan kai tsaf dakai kasamu wasu matan yara shakaf " dariya akasaki bayan angama huduba Zaid Ishaq Karimat Batol duban Iftahal Sarki Zaid yayi yace to " gimbiya nasan dele zakusaka musu wani sunan na alkunya wannan kuma kece yakamata kifitar " cikin jin kunya tace " nabama su Aunty dama "

Tana rufe baki " Aunty Bahijjat tace " toni zanfara fad'in nawa Irfan " murmushi kowa yayi yace Masha Allah cikin sanyin murya Aunty kurrat tace " kaga yarinya wato yau kece babba ko ? shikenan tonima naza'bi Ibban " masha Allah kowa yace se Aunty Faheemat tace " nikuma Islam " Nanma Masha Allah sukace se Aunty Sumeer tace " nikuma Iman " Masha Allah nanfa kowa yacika dafarinciki Zaid shine Irfan Ishaq Ibban Karimat Islam Batol Iman "fad'in irin shagalin da'akasha bazai yiyuba Amma kunsan ansha shi'ani

Akwana atashi asarar mai rai bayan wasu shekaru Maher yakammala Skul d'in shi hakama Iftahal amma sunqi komawa Egypt shikam Maher ayanzu yashihara inde sari'ace tofa baya ta'ba fad'uwa ayanzu qasashe ake zuwa d'aukar shi tsayawa sari'a yara sunyi girma sosai se yanzu Iftahal tasamu wani cikin tofa Alhaji Tukur yawarke kuma Yana nan akan bakarshi hakama Hjy Himla Aunty Bahijjat kuwa itama se yanzu tasamu ciki ayanzu cikin nata 2 months yana matuqar wahalar da ita sosai Aunty Shukura ayanzu yaranta 2 Ummi itace babba se Junior me sunan dadyn Zayyat shikuma Yaya Ibrahim yaranshi duka mazane Sadeeq da Haidar

Egy

Baby an girma misalin 8 safiyar litinin tuni Akeey Zaffar yafita hospital cikin shagwa'ba baby tace " Momy gaskiya yau kece zaki kaimin abinci Skul Ina shi'awar haka " murmushi Aunty Bahijjat tayi tace " angama baby na zan kawo miki haka kuwa akayi dakanta takai mata abincin misalin 5 pm Akeey Zaffar yadawo shida abokinshi kabir suna shigowa baby tadawo rungumai Aunty Bahijjat tayi sannan Akeey Zaffar se Kabir sannan tashiga cikin bedroom d'in ta abinci Aunty Bahijjat tashiga kitchen ta d'akko Mata takaimata sannan tafito abinci takawomasu Akeey Zaffar sannan takoma bedroom d'in ta kamar 20 minutes sukaji ihun baby cikin bedroom saurin tashi sukayi sukanufi bedroom d'in itama Aunty Bahijjat cikin sauri tafito suna Isa suka tadda baby kwance saman Carpet tariqe ciki wani irin farin kumfa yana fita daga bakinta cikin sauri sukayi kanta aguje Akeey Zaffar yafito kayan kwaji yad'auka cikin sauri da rud'ewa yake dubata amma Ina kafin wani lokaci baby tace ga duniyar ku nan cikin tashin hankali Akeey Zaffar yadubi Aunty Bahijjat yace " my dear guba acikin abincin Baby daga Ina " cikin gigita Aunty Bahijjat tace " guba Kuma jinjina Mata Kai yayi yace tabbas " kuba baby taci irin kumfan bakinta ya'isa tabbatar dahaka kuka Aunty Bahijjat tasaki tace " wallahi bansan daga Ina akasamu guba ba " sosai Kabir yadubeta yace " kamaryafa Bahijjat amma kuma idan bakisaniba tayaya abinci yazama kala 2 wanda Kika bamu daban na baby Kuma daban ? " Cikin tashin hankali matuqa tace " wancan Wanda nayi da ranane shine nakaimata Skul ganin taci irinshi darana yasa senayi Mata wani " sake dubanta Kabir yayi yace dama kin safa yimata haka ? " girgiza kai tayi cikin tashin hankali cije lips d'in shi yayi yace " kenan sabida yau kin shirya wani abu shine kikayi hakan ? Cikin furgici Aunty Bahijjat tace " bangane Mai kake nufiba Kabir ?" Cikin fusata Akeey Zaffar yadubi Kabir yace wannan tambayoyin naka mesuke nufi kana nufin kace Bahijjat itace tasaka guba cikin abincin baby ? Ina Bahijjat bazata ta'ba kashe baby ba itada 'yarta "

Jinjina Kai Kabir yayi sannan yace " to ayanzu Kam sekabari bincike ya tabbatar dahaka "

Comments please

_Marmyn Zarah Ce_
🗡 *!!!FURUCI!!!* 🗡
💔💔💔
💔
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* 💓❣💘

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

🅿 61 to 62

Abu kamar wasa d'aga waya Kabir yayi yakira ma'ay kata cikin hadda wani doctor dan tabbatar da gubar da babyn taci cikin tsananin 'bacin rai Akeey Zaffar yace " Wai kai Kabir kananufin dagaske kakeyi ne wajan tuhumar Momyn yarinyar nan ? kabarni naji da d'aya mana ganin gawar baby a kwance kad'ai ya'isheni tashin hankali wallahi nayi imanin Bahijjat bazatakashe min baby tun bayan wasu shekaru take riqe da ita dazata kashe ta datuni takasheta " dafashi Kabir yayi yace " ka kwantar da hankalin ka Zaffar nimafa banace Wai tabbas itace takashe baby ba a a zargine Kuma nasan zakaso sanin wanda yayi maka wannan d'anyen aykin dubada irin tsananin son dakakeyima baby Wanda babu alamar zakasamu wata Koda kasamu dole bazaka manta da baby ba kodan Mahaifiyar ta kasanfa ni hukuma ne Mai hakqin kwatar makowane d'an Adam haqqin shi idan bincike yanuna matarka batada lefi to babu abinda zamuyi mata amma yanzu dolene mutuhumaita gunda ayanzu bamuda wani abin zargi se ita kayi haquri zamutafi da gawar baby danyin wasu gwaje gwaje dukda kasancewar ka doctor bakaine yakamata kayi wannan binkiken ba sabida ba lalle ne kasanar damu gaskiya dubada yadda kake qoqarin hanamu aykin mu bazamu tafi da matarka ayanzuba amma idan akwai yiyiwar hakan tofa zamudawo sekaji daga gareni "

Sawa Kabir yayi aka d'auki gawar baby kafin yafita Akeey Zaffar yadakatar dashi sannan yace " inaso kasani tabbas Bahijjat bazata iya kashe kowaba balle baby sannan dakake maganar babu tabbas d'in samun wata babyn to kasani ayanzu Bahijjat tana d'auke da cikin 2 months kuma wallahi idan kukayi sanad'in wannan cikin yasamu matsala asanadin wannan mugun zargin naku to wallahi senayi shari'a dakai sannan nikoma waye yakashe Baby nabarshi da Allah tunda nayi imanin ba Bahijjat bace dan haka kubani gawar 'yata ayimata sutura Allah yawadaran aboki irinka "

Sosai Kabir yadubaishi yace " haba Zaffar wallahi da alkairi nake tare dakai wannan abin dakaga nayi yazama dolene ni hukumane kasan wannan yazama dole nakama duk wani mai lefi koda kuwa shid'in ubanane to wallahi senakamashi sabida nayi rantsuwa akan haka sannan bama matar kaba Koda kaine zargi yagifta takanka tofa wallahi sena bincike ka dukda kuwa kaine kahaifi baby sannan idan Kai kayafe tofa ita government bata yafeba dole tabinciko mai lefi aduk inda yake kuma tahukuntashi har gobai Kai abokina ne Bahijjat inatayaki murnar samun qanwar baby "

Daga haka suka fita shida sauran jami'an da gawar babyn dasauran abincin dabata qarasa cinyewaba se alokacin Aunty Bahijjat tasaki wani irirn kuka had'ida fad'in Innanillahi wa'inna ilehirraju'uuuunn Allahumma ajirni fimusibati wakalumfi kayrun minha waqifli kairun minha " bata tayi zata fad'i Akeey Zaffar yayi saurin riqota shiko yamakasayin kukan sede wani irin zafi da zuciyar shi keyi yamarasa Yaya zaiyi

Cikin tashin hankali yad'aga waya yakira Mahaifiyar shi yasanar da ita kafin yaji yanayin tashin hankalin dazata shiga yayi saurin kashe wayar cikin raunin murya yace " my dear banaso kitashi hankalin ki kinsan de halin dakike ciki kuma nayi imanin bazaki iya kashe Baby ba kisaka hakan cikin ranki nasan su momy sunanan tafe ni zan bi su Kabir " daga haka yami'ke cikin sanyin jiki Yana kaiwa bakin qofa yajuyo yasake duban Aunty Bahijjat yace " dan Allah kibar wannan kukan har abada kece Momyn baby tatafi da tsananin sonki cikin zuciyar ta tabbas wannan abun alfahari ne agareki ada Baby babu Wanda takeso sama dani amma ayanzu tafi sonki fiye dani gashi kin rasata alokacin datake cikin tsananin gata agun Momyn ta Allah sarki baby ashe bazataga qanin nataba narasa Mahaifiyar ta yauma gashi narasata my dear Koda kece Kika kashe min baby bazan hukuntakiba sabida kinyi Mata dukkan alkairi amma ina da tabbaci cikin zuciyata cewa bake bace naroqeki karkisa nasake rasa little baby dan Allah my dear dan Allah 😭😭😭 👏🏻👏🏻👏🏻 "

Daga haka yafita cikin sauri yanazubba zafafan hawaye tsayin lokaci yana tsaye a parlour yakasa fita wani irin kuka yakeyi marar sauti amma dukda haka Aunty Bahijjat tanajiyo sautin shasshekar kukan nashi wani irin juwa Aunty Bahijjat taji had'ida wani irin mugun ciwon kai wayar shi tad'auka wadda yabari anan kiran wayar Ammin tayi bugu 2 tad'aga kasanin magana Aunty Bahijjat tayi sabida kuka sautin kukanta kawai Ammin keji cikin tashin hankali Ammin ke tambayarta amma takasayin magana sosai hankalin Ammin yatashi da qyar Aunty Bahijjat tace
Chapter 34 · 0% Book details