← Book details Furuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 41

Sashe 15

Furuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" _barka da 'kokarin Iftahal gaskiya najinjina miki nine wanda nasanar da Shanwul duk abinda yake faruwa akan Maher yanzuma zansanar dake wasu abubuwan amma kafin Nan kice Saraki yayi bacci cikin zafin rai Saraki yace " babu baccin dazanyi wato nayi bacci kasamu damar cutar da ita ko to wallahi baka isaba idan kaga kacutar da ita to sede idan kasheni kayi " murmushi tsohon yayi yace to ay kokanaso ko bakaso sekayi wannan baccin daga haka yahura mishi iska kafin wani lokaci tuni Saraki yabaje sosai Iftahal taji zuciyar ta tadake duban wannan Tsohon tayi shima yadubeta yace

" _Yarinya inamai sake sanar dake daki jajurce sosai sabida akwai 'kalubale dayawa akan zamanki da Maher sannan dole zakisamu rud'ani akan Maher dole zakiga kamar kinarayuwa da mutun 2 ne bayan Kuma 1 ne sekinyi ha'kuri kimaida maher kamar su 2 ne kamar yadda Kike kiran wannan Saraki to kibarshi ahaka Kuma kiyi rayuwa dashi mai kyau sabida anan gaba idan 'kwa'kwalwar shi takoma tahad'e zai iya tuna yadda kikayi rayuwa dashi a wannan lokacin duk wani abu dakike shakkar shi ko kike ganin baki'iya sanar dashi to duk zesani idan 'kwa'kwalwar shi takoma tahad'e amma ayanzu dole ki daukesu tamkar daban daban kiyi rayuwa da shi akowane yanayi yake aduk lokacin dakike so yajuya kamar yadda kike so to zan baki wata addu'a dakinyita danufin Maher kike so yajuya ko Saraki shi kenan zai juya amma daga lokacin da yasamu lafiya shikenan ni nabarki lafiya idan natafi kita'bashi zai tashi amma Saraki ba Maher ba Maher Yana bu'katar hutu sosai sannan kiyi duk yadda zakiyi kihana doctor yimai wannan allurar dazeyi idan yadawo Kuma wannan karon bada Sarki Zaid zezoba sabida shi zashi Nigeria wajan iyayen ki_

Daga haka yabata addu'o'i sosai sannan yatafi sosai Iftahal take jinjina wannan lamarin tayaya zatadinga rayuwa da mutu 1 amatsayin 2 sosai lamarin yake bata mamaki had'ida matu'kar d'aure Kai sannan tayaya zata iya hana doctor yin wannan allurar ? tsayin lokaci tanayin wannan tunanin sannan tajuya tadubi Saraki dake kwance kamar maiyin bacci cikin jin d'adi cikin rawar hannu tata'bashi kamar wanda aka furgita yatashi afurgice saurin jawota jikinshi yayi yana dube dubai zuwa can yasauke ajiyar yace

" My Wife babu abinda yayi miki ko ? " Murmushin 'karfin hali tayi tace " babu abinda yayi min kwantar da hankalin ka " sake rungumai ta yayi cikin sanyin murya yace " mu kwanta ko My Wife am dama dama dama " kallon shi tayi cikin mamaki tace " dama Mai sanar dani mana " sake kallon ta yayi yace " dama inaso musakeyin wannan abun ne najiya " zaro ido Iftahal tayi sabida sosai tafurgita dan kam bata manta irin azabar datashaba 'kokarin kwace jikin ta daga nashi tashigayi amma Ina yamatseta sosai cikin raunin murya tace " haba Saraki dan Allah kabarni banfa warke daga jinyar daka sakaniba Kuma banaso Maher yagane abinda yafaru dani sabida banida amsar bashi kaga kenan zansamu matsala

Afusace yaturata tafad'a saman bed d'in yabita cikin hassala yace " banace karki sakeyimin maganar wani Maher ba nine mijinki nahar abada Allah idan Kika sake yimin maganar wancan sena tarwatsa tashi 'kwa'kwalwar nahuta daga haka yake bakinshi cikin nata yafara kissing d'inta kuka Iftahal tafarayi sabida yadda taji jikinshi yafarayin rawa hannun shi yad'aura saman breast d'in ta jin shasshekar kukanta yasa Saraki dakatawa cikin muryar lallashi yace

" Haba my wife meye Kuma nayin Kuma tonaji nabarki shikenan amma gobe zakibani ? Saurin d'aga mishi Kai tayi sake sumbatar lips d'inta yayi sannan yaja musu blanket sosai yarungumai ta cikin 'kirjinshi cikin sanyin murya yace

" My wife ina tsananin sonki amma zuciyata tanayin zafi idan naji kin ambaci wancan Maher d'in nine mijin ki bashiba dan haka daga yau babuke babu shi kinji my Wife cikin shagwa'ba tace " Ina ay dama ni Babu ruwana dashi Kai ne Mai sakarmin fuska Kuma Kai ne mai furtamin kalmar soyayya nima Ina matu'kar son ka Saraki na " sake matseta yayi cikin jikinshi sabida dad'i ahaka har bacci yayi gaba dasu sosai Iftahal tayi bacci Mai dad'i cikin wannan daran Kiran sallar asalatu yafarkar da Iftahal kallon fuskar Saraki tayi sefaman Shan bacci yakeyi sosai takejin dad'in kallon shi murmushi tasaki tace " Allah sarki Saraki na yanzu zakabar ni nida wannan uban miskilancin " daga haka tayi addu'o'i da wannan tsohon yace tayi

Babu jimawa Maher yabud'e idonshi ahankali suka sauka kan kyakkyawar fuskar Iftahal saurin janye jikinshi yayi daga nata tamke fuska yayi sosai yace " waye yasaki hawamin saman bed ? " Murmushi Iftahal tasaki tace katambayi kanka Mana Prince Kai da kanka kajawoni Kuma bakaga yadda karungumeni ba ? " tsaki yaja afusace yace " banason shashancin daga yau Kar in sake ganin hakan " cikin d'an damuwa Iftahal tace " to amma naga umarnin Ammin ne hakan tace karmu raba gurin kwanciya " banza Maher yayi da ita yasauka daga bed d'in seda yake bakin 'kofar toilet yace " hakane umarnin Ammin ne amma Kinga wannan cushion d'in to anan zakidinga kwanciya " har yad'aga qafarshi zai shiga sekuma yatsaya yace " waye ya kwashe aman dake gurin nan ? " saurin duban gurin tayi tabbas Babu komi agurin Kuma iya saninta bata kwashe shi ba sosai Iftahal tayi matu'kar razana amma cikin in ina tace nice " tsaki Maher yaja yace " Wai banace babu ruwanki cikin lalurataba Kinga Iftiih!!!!! banaso kina saka kanki cikin wannan lamarin ki kiyaye tashi kibar bedroom d'in nan "

Saurin sauka Iftahal tayi tafita sabida tsananin tsoro dan Kam tafurgita sosai tana sakkowa tanufi bedroom d'in ta abinda tagani yasata saurin jabawa gaba d'aya ancanza tsarin kayan bedroom d'in aguje tafito tana kwalama Maher Kira cikin sauri yafito kogama alwala baiyiba kasa magana tayi senuna mai hanyar bedroom datayi Kai tsaye yanufi bedroom yashiga dube dube yashigayi amma baiga komiba Kuma Shirin kayan yakoma yadda yake ahankali Iftahal tale'ka amma setaga yadda Shirin yake tunda haka yake wani irin kallo Maher yayi mata yaja tsaki yabar bedroom d'in

Comment please

_Marmny Zarah Ce_
🗡 *!!!FURUCI!!!* 🗡
💔💔💔
💔
*((((( Murd'add'iyar Soyayya)))))* 💓❣💘

Story and written
BY
NPEEDY A AJI 🌸marmny Zarah🌸

Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
And
Lovely
Daughter
*Zarah*

KAFAD'I ALKAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT 2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
5 HAYATUL MAHAYAT
6 MUGUN SARTSE

Loading....... 📖🖊

🗡💔 FURUCI!!!!!💔🗡

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Ina masoyana ha'ki'ka iname baku ha'kuri akan abinda zakuji yanzu ada banida niyyar yin hakan yanzuma wani daliline yasa hakan Allah yasa zakufahimceni wannan book d'in nakud'i ne 200 kacal nasan nafi karfinta agareku ko kyauta zakuiya bani

ZAKUTURO NAIRA 'DARI BIYU KACAL TA ACCOUNT NUMBER NAN FIDDAUSI ISHAQ
0005556335
JAIZ BANK

IDAN AN TURA A YIMIN SCREENSHOT DIN TRANSACTION DIN KO KUMA KATIN 'DARI BIYU NA MTN WHATSAPP NUMBER NA

08135419440 akwai saban group wanda zansaka duk wanda yabiya in sha Allah typing kullum amma banda ranar Friday

DUK WANDA YAFITAR MIN DA BOOK TOFA SHIDA ALLAH NASAKE FADA SHIDA ALLAH

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA ALLAH YABAR ZUMUNCI DA SOYAYYA NPEEDY A AJI TAKUCE HAR ABADA

🅿 21 to 22

Tsayawa tayi tana nazarin lamarin amma cikin matu'kar tsoro take tsayin lokaci tana tsaye tana karanto addu'a sannan tashiga ciki darajar addu'a yasa Iftahal taji zuciyar ta tadake sosai Kai tsaye tanufi toilet tayo alwala tafito salla tatada kafin Kiran sallar asuba sosai Iftahal takeyin addu'a akan wannan lamarin Allah yayi mata jagora

Egypt

Bayan dawowar Sarki Zaid da Sarauniya Batol mama takira Sarki Zaid Babu jira ya amsa kiran Mahaifiyar tashi yana shiga parlour ya taradda hjy Himla da d'anta Abdul bayan yazauna yagaida mama sukuma suka gaidashi ygara zama mama tayi tace " Zaid abinda yasa nakiraka bawani abu bane maganace akan Abdul yana son auran Bahijjat kuma ni nayarda da wannan auran sosai Sarki Zaid yaji babu dad'i sabida dan Kam yasan halin Abdul bayaji tako Ina gaskiya bayason wannan auran to amma yaya zaiyi bazai iya yima Mahaifiyar shi musuba babu yadda zaiyi dole yadubi mama yace " to Mama tunda kinason hakan Allah yasa hakan shine mafi alkairi " murmushi mama tayi tace Allah yayi maka albarka Amin yace yami'ke yafita murmushi hjy Himla tayi shiko Abdul mi'kewa yayi yafita fuskar shi d'auke da murmushi part d'in Ammin yanufa sabida yasan Bahijjat tanacan yana shiga yasameta zaune akan cushion tana latsa wayar ta Zama yayi kusada ita afurgice tadube shi cikin fad'a tace

" Maiye haka Yaya Abdul Babu ko sallama wallahi ni Kam kabani tsoro " tamke fuska yayi yace " to banyi niyyar yin sallamar ba jawota yayi tafad'o jikin shi babu zato rungumai ta yayi sosai yakawo bakinshi dede kunnanta yace " zuwa nayi nasanar dake cewa Maimartaba Zaid yabani auran ki kinga kenan daga yau zakifara yimin biyayya " cikin zafin rai tatura shi tadube shi tace Allah yatsari gatari dasaran shuka wallahi dana aure ka gara namutu babu aure kasani Ni Bahijjat ba irin matar kabace "
Chapter 15 · 0% Book details