← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 55

Sashe 50

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mom ta bashi amsa da fadin kwarai kuwa akan bai ishe ni bah, Nadira tace Mom meyasa kike aka, ga y'ay'an kinan suma kin hada dasu, duk mene aka, menene silan aka, Grandma tace kwarai kuwa, ki fada mana wane abu aka yi miki da kike son daukar fansa?

Mom tace Yunusa yusuf wato mijin ki, shine silan komai da ke faruwa daku,

Grandma tace yanzu mijin nawa mah saboda Allah da annabi baza a bar ruhin sa yasamu salama bah, sai anyi masa sharri,
Tabbas nasan karya kike bawani mijina da ya miki wani abu. Dakatar da Grandma Kabir yayi da fadin ki bari muji menene yafaru, maida Kallon ta kan Mom yayi, yana mai fadin, ki fada mana abunda ya faru.

Dad yace dakata tukunan, dole Sai Maryam da Habib suna nan domin banason ayi komai a bayan idonsu, yanzu ku kiramin Habib da Kuma Maryam yanzu, suzo, daukan wayar sa, Sadiq yayi tareda Kiran Abban sa wato Habib, sannan shima Khalid ya dau waya Tareda kira Mahaifyar su Mami.

Bayan wasu hawanni kowannen su ya hallara .
Dad yace toh Alhmadulillah kowa yana nan, yanzu zaki iya magana

Kallon su Mom tayi tace.
SHEKARU BAYA DA SUKA GABA TAH.

Mahaifina da Kuma mahafin ku, wajen bussiness dinsu daya, Kuma sudin sun kasance babban abokai nee. Komai tare suke yi, amma mahaifin ku yafi mahaifina kudi nesa bah kusa bah, duda aka kakan ku bai taba nuna wai shidin wani ne.

Hana aka sai suka samu sab'ani Shida babana, akan wani maganar kudin da suka samu wajan Millions of Naira, sai mahaifin ku ya yanke cewar za'a kai gidan marayu, Wanda babana tsam bai amince da akan bah domin shi a ganin shi da akai kudin gidan marayu gwanda su Kara wa kansu jari, shikuwa kakan ku yace, indai rabuwa ce saidai su rabu amma bazai taba bin maganar sa bah.
Aka kuwa akayi yayinda kowannen su yayi hanyar sa, babu wanda yakara kula wani acikin ku.

Hana aka karayar arziki ta samu babana, yayinda muka talauce, koh gishiri Bamua samu mu siya saboda tsanannin talauci, a lokacin mahaifina ya yanke cewar zai Shiga qungiyar asiri domin yayi kudi ya zama sananne wanda babu kamar sa.

A lokacin yaje yayi joining qungiyan asiri, amma a lokacin aka gargadi mahaifina da cewa
kada ta kuskure ya fadawa kowa, Kuma dole ya kawo babban abokin sa wanda yake matukar kauna, sannan yayi sadaukar wa da jinin sa.

Mahaifina baiyi jayayya da akan bah, ya yarda da umarnin da aka bashi. Bayan wasu kwanaki. Mahaifina yayi kudi, dukiya suka habbaka, yazama sananne wanda babu kamarshi, haryazo yafi mahafinku kudi.

Hana aka, babana ya nemi suyi sulhu da mahaifin ku, shikuwa mahaifin ku, ya hakura suka koma normal yadda suke a da.

Sosai suka kara kaunatar junan su, inda mahaifina ya yanke cewar zai fada wa mahafin ku komai da komai, abunda yasa arzikin shi yayi yawa...

Hana tsaka da aka, baba na, ya nemi su fita da Mahafin ku, babu jayayya Mahaifin ku ya amince da akan, inda baba na ya kaishi Chan cikin jeji, sannan ya Kalli abokin nasa ya ceda shi,

Tabbas Kai abokine na kwarai, Amman inason na fada maka wani sirri na, Kuma Dan Allah inason ka adanamin, karka Bari duniya ta sani, mahafinku ya ceda baba na,

Menene sirrin? Meyasa ka kawo ni daji? Me kake shirin aikata wa?

Hatake baba na ya kira sauran yan qungiyan, lokacin da mahafin ku ya gansu, yayi matukar tsorata sosai,

A lokacin babana ya sanar dashi komai da komai, inda mahaifin ku yak'i amince a sadaukar da jinin sa inda a karshe yace saiya tona masa asiri, duniya tasan cewar shidin maciyi amana ne,

Shi Kuma a lokacin mahaifina ya Shiga bashi hakuri, Kuma yayi masa alkawarin cewar zai bashi kudade Duk abunda ya keso, amma Dan Allah kada ya tona asirin shi a idanun duniya, Hatake mahaifin ku ya kira police officers, suka zo suka tafi da baba na,

Shi Kuma mahaifin ku ya kwashi kudaden baba na, ya kaiwa su police, inda police din suka raba kudin a tsanin su.

Yayin da Baba na ya tafi magarkama na wajan shekaru goma, bayan ya futo, yaga komai nasa ya yi kasa, kudaden da ya Tara da duniyan da yake dasu duk babu, akan ya sashi cikin damuwa har yasamu ciwon zuciya,

yana cikin kakarin mutuwa ya kirani, ya sanar dani duk abunda ya faru, hawaye ne suka Fara bin kan kuncin Mom, sannan ta cigaba da fadin,

Baba na yace na daukan masa alkawarin cewar zan daukar masa fansa, bazan taba rabuwa da ku bah, ni kuwa na daukan masa alkawarin cewar saina ga bayan ku baki daya, bazan bar koda kud'a wanda nasan ya futo daga gidan nan bah, saina raba ku da farin ciki, saina sanya ku cikin kunci da bakin ciki,

Ina kaiwanan, Baba na ya tashi da zummar yaje zai kaini na Shiga qungiyar asiri, rike hannu na yayi yayin da muka futa wajen layin,

Ban hankara bah, naji han fara je fawa baba na Duwatsuna, da Kuma rodi, kuka a lokacin nai tayi, yayin da na dunga rokan su, subar min mahaifina, sannan ta Kalli Amina da Kuma mahaifiya ta, wacce ke a tsaye basu tanka wa mutanen bah,

A lokacin raina yayi matukar baci, ganin mahaifiya ta da yar uwata, basu tanka wa mutanen bah, a lokacin naji tsanan kowannen su a raina,

Aka suka cigaba da jifan Baba na har saida numfashi ya futa daga jikin shi, sannan suka barshi a wajan, sukayi tafiyar su.

Babu wanda ya taimaka min, ni da kaina na dauki gawar mahaifina sannan ta kaishi makabartar yayin da yan qungiyan asiri suka taimaka min, muka bunne sa,

Tunda ga lokacin na Shiga cikin yan qungiyan asiri, yayin da jini na ke tafarfasa, fansa kawai take son dauka, hana aka na Fara bibiyar mahafin ku, ban daina bibiyar sa bah, har saida naga na kawar da rayuwar sa, bayan nan kuma, naje gidan mu sannan na lashe mahaifya ta,

Itama Amina zan kashe ta, amma abunda yasa ban kashe ta bah tana gidan mijin ta a lokacin, yasa na barta da ranta amma duda akan bai hanani bibiyar rayuwar ta bah.

daga nan kuma na shigo cikin ahalin nan a matsayin mata, na saka Y'aya na Suleiman ya bani kai a matsayin mata, Kuma na shigo gidan nan domin daukar fansa .

Kuma bazan dakata bah, har sai na cikawa mahaifina burin shi na karshe kafun na sarara Wannan shine .

Ajiyan zuciya gabadayan su sukayi, inda Mami ta fara magana kamar aka, toh mahaifin ki ya mutu, amma ai bah mahafin mu ne ya kashe shi bah,

Kwarai kuwa mahafin ku ne ya kashe baba na, da mahafin ku bai fada wa duniya wanene baba na bah, da haryanzu nasan yana raye, Kuma na ruga dana daukan wa Baba na alkawarin cewar, Har jikokin Yunusa yusuf, bazan bari bah, Domin har su zan hada na kashe. Kuma shine zai sa a kara mun matsayi acikin kungiya.

Doct khadija tace, amma meyasa ni kika kashe min dana, Kuma kika kashe yarinyar Amina. Kuma kinsan da cewar Amina batasan cewar ke yar uwarta bane Domin rabonda ku hadu yakai,

kusan shekaru talatin da yan Kai, amma ke kingane ita din yar uwarki ce, yayinda ita bata sani bah,

Mom ta bawa Doct khadija amsa da fadin, ni ban kashe danki bah domin kuwa danki yana raye bai mutu bah, zaro ido Doct khadija yayin da jikin ta yafara karkarwa tace yana ina Dan Allah ki kiramun dana, inason na ganshi.

Mom tace zan fada miki Amman kafun nan, ki kiramun yar uwata Amina da Kuma danta da mijin ta yanzun nan,

Cikin rawar jiki, Doct khadija ta dauki wayar ta, Tareda dialling number Ammi wato Amina, ringing biyu Ammi ta dauka Tareda karawa a kunnen ta tace, hello Salamu alaiki, Amsa sallamar Doct khadija tayi tace,

Yar uwa, Dan Allah keda mijin ki da Kuma danki Duk kuzo yanzun nan, Ammi tace, amma dai lafiya koh, Doct khadija tace lafiya ce ta kawo akan karki damu babu komai kuzo kawai,

Tom shikenen gamu nan zuwa gidan su Kabir din, katse wayan Ammi tayi, yayin da ta Sanar da Abban yusuf komai da komai, sannan ta samu yusuf wanda yasamu sauk'in jikin shi sosai, tace masa ya shirya zasu je gidan su Kabir, bah jayayya, yusuf yace Tom shikenen,

Cikin kankanin lokaci suka isa gidan su Kabir, yayin da Amar ya kaisu dak'in da gabadayansu suke, Shiga ciki sukayi sallama rike a bakin su.

Amsawa su Grandma sukayi, guri su Ammi suka samu sannan suka zauna, Abban yusuf yace lafiya dai koh naga kowa ya taru hanan, Aunty amarya tace lafiya lau wallahi, Dama wani Dan karamin issue ne ake tattauna wa akai.

Kallon Ammi Aunty Amarya tayi tace shin Maman Yusuf kinsan wannan matar ta fada Tareda nuna Mom, Kallon Mom Ammi tayi tace, Aa ban Santa bah, amma nasan cewar itace Maman Kabir, Kuma tana min Kama da yar uwata hassana.

Doct khadija tace idan na fada miki wani abu zaki yarda?, Ammi tace me zai Hana, zan yarda mana,

Doct khadija tace, toh dai wannan da kike gani itadin yar uwarki ce wato hassanan ki, wacce kanku ya rabu akan Abban yusuf,

Da sauri Ammi ta Mike, Tareda Kallon Mom tace, da gaske kece hassana ta? Mom ta bata amsa da fadin kwarai kuwa nice nan, nina hanaki sukuni a gidan auren ki, na saka kika rasa yarki wacce kike mugun qauna wato Sabreena,

Kallon ta Ammi tayi a hassale tace, dama kece, ina kika kaimin y'ata, bayan kinsan cewar ita kadai na haifa, wato dana kaita asibity lokacin da Asman ta ya tashi ke kika kashe ta koh, Meyasa zaki aikata min aka bayan kisan ita kadai gareni.

da kallon mamaki Yusuf ya Kalli Ammi, sannan yace, Ammi ni din fah, ni bah danki bane.

Kallon shi Ammi tayi tace kwarai kuwa kai bah dana bane, Kai adopted child ne, zama Ammi tayi hawaye na bin kan kuncin ta, tace kayi hakuri nayi boye maka gaskiya na tsawon shekaru, tabbas Kai bah dan mu bane, sabreen itace kadai yar dana haifa.
Chapter 50 · 0% Book details