← Book details Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 55

Sashe 28

Aljanar Ruwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meee Amriya tafada. Kalisat tace meyafaru da matsala ne. Amriya tace Aa ba matsala.

Tace Yauwa... salma..dakin.. Wana.. Shiga.. Dazu..

Dariya su nadirah suka fashe dashi fateema tace yanzu ace dukk zaman dakikayi a gidan nan bakisan wannabe dakin na waye bah toh na mom nee dakin. Tana kaiwanan nadirah tajasu suka fuce suka bar itah kadai a dakin

Rass gaban Amriya yafadi. Tareda fadin dakin mom meyake faruwa. Zaro ido tayi tace kenen hakan yana Nufi mom itace uwar shedanu dake son ganin bayan wannan ahalin.

Kenen Itace tazoda Zeharis gidanan. Tabbas kenen itace Uwar shedanu.

Daga sama taji ance kwarai kuwa nice

COMMENT & SHARE PLS 馃檹馃檹
ALKALAMIN 馃枈锔?
BABY ISHA 馃挒馃挒馃挒
2/28/24, 22:07 - AISHA M.B (Baby isha): https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCAIATION 馃枈锔?
(J.A.W)
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'i 鉁忥笍

ALJANAR RUWA CE 馃鈥嶁檧锔忦煂婐煂? PAGE 2锔忊儯6锔忊儯鈻讹笍2锔忊儯7锔忊儯

WRITTEN & DIRECTED 鉁嶏笍
BY BABY ISHA 馃挒馃挒
(AISHA M.B)

-----------------------

Da kaolin mamaki amriya kebinta dashi tareda fadin mom kece. Mom batajira cewarta bah tace kwarai da gsk kinyi mamakine.

Tabbas nice. Zeharis ce tashigo murmushi dauke a fuskanta tace hmm yar uwata Aljanar ruwa hatare itada Mom suka kwashe da dariya

Cikeda bakinciki Amriya tace Amma indai kece mahaifiyan Kalb baiyi dacen uwaba.

Mom tace laaa Ashe mah kin iya mgn daidai.
Toh barakiji ni na haifesa kuma saina gabadayansa.

Cikin kunan rai Amriya tace karya kike baki isah kigabayansa bah Baku isaba indai har ina gidanan kuma Koh bana nan Allah saiya tona asirinki.

Azafafe mom tace saidai Allah yatona Asirinki aljanar ruwa . Kin manta duk wanda yabi hanyar da uwar shedanu tabi sunansa gawa. Saina gabayan wannan ahalin sainasa anyi ruwan jini..

Dakata nan Amriya tafada kinsandai ni Aljanar ruwace kekuma BIL Adama babu inda Aljanar ruwa da bil adama zasu hadu Dan haka Kisani kinyi kuskure fadamin gsk kece uwar shedanu sbd bazan bar mutum daya daga cikin ku shedanuba. Hmmm yanzu wasan yasoma.

Matso daff da Amriya mom tayi tareda fadin muzuba mugani. ALJANAR RUWA KOH KUMA UWAR SHEDANU

Juyawa su biyun sukayi daniyan futa dakatar dasu Amriya tayi dafadin kada ku manta ku hada makamanku Dan nawa makaman ashiryesuke.

Murmushi mom Da zeharis sukayi tareda fucewa daga dakin.

Dafe kanta Amriya tayi wasu zafafan hawayee nabin kuncinta tace Meyasa sai ke Mom meyasa zaizamana kece Maison ganin bayan wannan ahalin tabbas bazan barki bah dole nadaka tardasu yazama dole nasanar da Aunty Amarya.

Direct part din Aunty Amarya tanufah. Ta tarar da triplet acikin dakin .

Adeef yace yauwa Aunty gatanan mah tashigo kimata mgn Dan Allah.

Kiran Amriya Aunty Amarya tayi kusada itah. Zuwa Amriya tayi kusada anty Amarya tace gani aunty.

Aunty Amarya tace kinaji yan uwanki guda biyu waike suke so . Rass gaban Amriya yabada. Tace Nikuma Aunty meyasa saini.

Adeef yace kada Kice haka inason zan aureki ne kawai indan bakyaso toh saina hakura.

Amar yace amma wannan bayi bane naga dai naruga ka. Shikenen Amriya tace tareda fadin Aunty duk Abunda kikace shine daidai.

Aunty Amarya tace Aa amriya bafa iyasu bane khaleed mah yazo yafadamin yanzunan yasanar dani.

Hatare su Mom, grandma, dad, khaleed da sadiq dasu nadirah sukashigo tareda fadin kwarai kiss yar mu.

Dad yace yakamata muma ace yaran mu su samu Mace tagari irinki Amriya. Dafata mom tayi saurin cire kafadarta Amriya tayi tareda watsamata banzan kallo cikin murmushin yake Mom tace yar mu yakamata kizabi daya daga cikinsu koh.

Tunda Sun sanar dake abunda ke cikin zuciyansu. Murmushi Amriya tayi tareda fadin ehh zanyi tunani akai. Cikin ranta kuwa tace waiyoo Allah meke damun ahalinan rayukansu nacikin hadari sukuma suna min mgn aure. Taya Aljanar ruwa zata auri BIL adama abunda bazai taba yiwuwa bah kenen

Dad yace toh yata Allah yasa muji Alkhairy

Nadirah tace Amma bakaramin dadi zamuji bah idan kika zamo matar daya daga cikin Dan uwanmu.

Fucewa gabadayasu sukayi . Ajiyan zuciya Amriya tasauke. Tareda rikee hannun aunty Amarya tace Inason zanfadamiki wani abu.

Aunty Amarya tace menene fadamin. Amriya tace bah lallai kiyarda Dani bah idan nafadamiki Amma kisani tanaso taga bayan Ahalinan. Aunty Amarya tace ban fahimta bah Amriya wacece zatagabayan ahalinan.

Uwar shedanu mana. Amriya tafada. Tareda fadin wai Mom itace uwar shedanu .Aunty Amarya tace Mom. Kwarai Amriya tafada.

Murmushi Aunty Amarya tayi tareda fadin Nasani. Amriya tace kinsani kuma baki taba fadamin bah.

Aunty Amarya tace nafison kigano da kanki kuma yanzu kingano.

Amriya tace indai kuwa hakane bazan bartabah har ita zeharis din. Meeee zeharis kuma meye hadin zeharis yar uwarki kuma.

Bakomai Amriya tabata amsa.

(AFTER ONE WEEK)
kowa nagani a parlour a zazzaune. Kowa da abunda yake sakawa a ransa.

Dad yace muna jiran cewarki Amriya. Wa nee kikaga yadace da rayuwanki sai mubaki shi kizaba nikuma namiki alkawarin zan Aura mikishi.

Kallon Aunty Amarya Amriya tayi. Fatan nasara Aunty Amarya tayi mata.

Kallon kowannensu Amriya tayi tace ina mai gdy agareku ... da kuka ...bani.... wannan.. babban... daman ....a ..gsk ...yau... zanfadi wanda ....ke ...raina ...zan ....aura. ...A gsk..

Grandma tace toh ennen kifada mana saikin jamana rai kuma. Daidai lckn dakuma kabir kesaukowa daga upstairs.

Amriya tace a gsk.... Ni... Kalb... Nakeson... Zan... Aura...

Kabir Jin maganan yayi uwa aradu da kallon mamaki kowannensu kebinta dashi .

Dad yace shikenen yata aure ki kaddara andaura angama wanna Kalman dama nake jira kenen saikuma Allah yayi Kinfada. Sosai kowannensu yayi Murna furucinta. Dad yace khaleed zanbaka Fateema, kaikuma sadiq nabaka yata nadirah triplet Abdul yace nidama inada kalisat dita. Amar yace inason ummi. Adeef mah yace abani Aisha Dad.

Toh Alhamdulillah Insha Allah next month za'ayi baikon maza uku khaleed, kabir dakuma sadiq daga baya kuma anyi naku. Dama munruga damun yanke wannan shawarar da mamin ku dakuma uncle dinku Dan haka idan akwai mai jaa a mgn tah yafuto yafada

Daga sama sukaji nadirah tace bazai yuwuba wlh bazan yarda bah tana kaiwanan ta nufi hanyar daki da gudu. Su salma suka rufa mata baya.

Kabir yace Dad Dan Allah Dad kada ka Auramin itah wlh banason tah bana kaunarta idan na aureta bazan tabayin farinciki bah.

Grandma tace kaiii menene haka Kanaso kana kaiwa kasuwa. Toh dole sai anyi auren koh kanaso koh bakaso.

Sosai su khaleed basuji dadi bah ha hankali kowanensu yabar palourn.
Dad yace Amriya insha Allah cikin kwanan nan keda mijin ki na gobe zakutafi Dubai siyayya kayan dakinki.

Kabir kamm jiyayi uwa ya kwallah ihuuu tsabar takaici da bakinciki.

Fucewa Amriya tayi daga palourn ta nufi parlour aunty Amarya.

Tarar da Aunty Amarya tayi kan kujera Da sauri Amriya tanufah inda take tace Aunty Amarya meyasa zakice nace Kalb nakeso. Bayan itama nadura nasonsa dawane ido kike tunani zasudunga kallona dashi nida nazo karban zobena nakoma idan fah nayi aurenan ban koma bah da zoben mutuwa zanyi. Indan lckn da haka irgamun yayi.

Cikin rashin fahimta Aunt Amarya tace bangane bah mekike nufi wane zobe kuma.
Dafa kanta Amriya tayi tadago da brown eyes dinta wanda suka kara rinewa sosai tace.

Aunty Amarya a gsk niba mutum bace kamar yadda kikayi tsammani ni ALJANAR RUWA CE. Mikewa Tsaye Aunty Amarya tayii tareda fadin ke Aljanar ruwa ce.

Kwarai da gsk Amriya tafada tareda fadin nazo duniyakune kawai Dan Nakarbi zobena Nakoma. Bawai nazone Dan na cutarda kuba.

Kuma yanzu kwanakin da haka gindayamin nada komawa teku Dada jaa yake Dan Allah kidakatar da auranan banzo gidanan dan nakarbi farinciki wasubah .

Aunty Amarya tace idan ke bah mutum bace taya toh yazamtoh kikeyin period.

Amriya tace nima bansani bah, aunty Amarya tace kenen hakan yana nufin kinada Halaka da jinsin mutane kenen.

Amriya tace jinsin mutane kuma taya ni ALJANAR RUWA CE kuma banda kowa Banida yan uwa sai Aljanun ruwan damuke rayuwa tare harzuwa girmana . Taya zakice inada halaka da jinsin mutane.

Kwarai kuwa Amriya mgn tah ba karyabane tabbas. Kedin ruwa biyu ce Ba iya Aljanar ruwabah tabbas kinada hadin Jinin da mutane.

Dan Allah aunty Amarya kidaina fada kibarni naji da abunda kedamuna. Gashi mom tanason Ganin bayan wannan ahalin gashi zan auri Dan tah dawane ido kenen su nadirah zasu dunga kallona dashi.

Aunty Amarya tace su kalle kidin mana sundade basuyibah kenen sokike rayuwansa ta salwanta a hannun wannan shedaniyan matan idan baki aureshibah taya zaki iya dakatar da mugun abu dazai tinkaroshi.

Bayan kuma indan yaje ya auri wata matan Matar bazata bari kidunga zuwa kusada shi bah.

Amriya tace Meye Anfani kyautata wah wanda baison kanamasa hallaci bah ya tsaneni koh da yaushe
bashida wata mgn daya wuce na tsaneki banason ganin ki.

Hantara, zagi, Shaka, Duka, wanne bansha bah awajansa tun kafun na aureshi kenen idan na aureshi mah abunda zaiyi saiyafi haka bazai yuwubah takasheshi din itah ta haifi abunta. Amma wannan ahalin bazan Bari ta cutardasu bah koda kuwa Hakan shi zaizamo sanadiyan daina numfashina.

Aunty Amarya tace Amriya kawo kunnenki kiji datsa kunnenta Amriya tayi a saitin bakin Aunty Amarya. Saida Aunty Amarya tadau kusan 2minutes tana fadamata mgn.

Amriya tace Amma kin tabbata hakan zai yuwu. Anty Amarya tace kwarai da gsk

Shikenen baranje. Futa amriya tayi daga dakin tanufi dakinsu saida tadan tsaya. Tukunan tashiga.

Suna ganinta suka mike tsaye. Nadirah fuskanta shabe shabe da hawaye tace mayaudariya macucuciya na tsaneki wlh. Banason ganin ki kifutamana daga gida.

Amriya tace. Dan.. Allah.. Ku.. Fahimceni. Tasss tass Nadirah ta tsinka mata maruka har guda biyu. Dafe kuncinta Amriya tayi hawaye sukafarabin kuncinta.

Daff da Amriya salma taje tareda tofa mata yawu a fuska tace Allah wadaranki maciya amana
Sosai Zuciyan Amriya ke bugawa tsabar damuwa.

Kalisat tace kin bamu mamaki Amriya a fuska uwata Allah Amma azuciya ke shedaniyace. Macuciya. Kawai. Bamuason kara ganin ki munafuka Kawai

Tsugunawa Amriya tayi kan gwiwowinta tareda hada hannuwanta tace Dan Allah.. Ku.. Fahimceni... Ku.. Saurareni.. Kunyimin.. Mumunan.... Nadirah bata bari takarasa bah ta dauki glass cup tareda rotsawa kan Amriya. Faduwa Amriya tayi jini yafarabin kanta.

Nadirah tace ke macuciya duk irin soyayya da na nunamiki duk irin soda kaunan danake miki bantaba banbantaki da sauran yan uwana bah kayanda nakesa shikikesawa Komai nawa nakine Amma yau kika butulce mana. Kinci Amana yan uwantaka damuka nunamiki.
Chapter 28 · 0% Book details